Skip to main content

Posts

Showing posts from January, 2019

Dalilai Goma Da Ke Sa Mata Sufa Da Wari

(1) Baki kai shekaru 50 a duniya ba amma zuciyarki tace miki kin tsufa kuma kika yarda kin tsufa din har ma kike aiki da hakan. (2) Baki kai shekaru 50 ba kin watsar da gayu, gyaran jiki na musamman, da kuma dinkuna na yara domin mijinki. (3) Baki kai shekaru 50 ba kina zama da daurin kirji alhalin ba wanka zaki shiga ba, duk wanda ya ganki ji yake kamar ya mare ki in baki sani ba. (4) Baki kai shekaru 50 ba kina yawo ko ina babu rigar mama (brazier) da dan kamfai (pant), ba kama jiki yayin tafiya kin saki jiki wai ke kin tsufa, kin tasa ruwan sanyi a gaba, kina yawo tsakar gida ba takalmi. (5.) Kin haihu baki damu ki gasa jikinki ba da zaman ruwan zafi ba da cin abinci ki koshi, da sanya hijab da safar kafa har kiyi shekaru 40. (6.) Kin haihu baki son ki nutsu ki tanada kanki ba kina rayuwa kaman namiji bakya bin sassan jikinki da gyara, bakya damuwa da cin abinci, domin rashin abinci shi yafi komi lalata mace baki an kara ba har wata haihuwan ta sameki, kinga kin fara rushewa kenan. ...

Amfanin Lallai A jikin Ya Mace

Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata su yi lalle akwai sirrika acikin sa. . . Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai: Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na sati biyu, in Allah yayarda za ki warke. Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural tone...

Hanyar Da Zai Kai UwarGida Aljannah

Assalamu alaikum ’yan uwa maza da mata musamman magidanta da ke bibiyarmu a wannan fili da muke tattauna lamurran da suka shafi zamantakewarmu da iyali da tarbiyya a bisa mahanga ta shari’a da kuma al’adunmu. A yau zan yi magana ne a kan garabasar da Allah Madaukaki Ya tanadar wa uwargida in har ta tsare abububuwa uku a nan gidan duniya za ta samu rabo mai tsoka a Lahira. In muka dubi mu’amalarmu ta yau da kullum Allah Ya halicci mata a bisa wata irin daraja da ta dara ta maza irin yadda aka kebance su daga wahalhalu na nema da ciyar da kai. Su kuma maza Allah Ya dora musu hakkoki na ciyarwa da kula na mata da ’ya’ya da iyaye da duk wani wanda ya jibince su. Ta bangaren ibadoji kuma mata an kebance su da tsare ibadojinsu a cikin gidajensu yayin da maza aka dora musu fita masallatai da fita jihadi da sauransu. Akwai ayoyi da hadisai da dama da suka yi magana a kan mace ta zauna cikin gidanta kuma ta tsare hakkokin da Allah Ya dora mata domin a gidanta za ta samu lahirarta. Akwai Hadisin...

Ilolin Yaudara Tsakanin Yan Mata Da Samari

Lura da yadda yaudara ta zama ruwan dare a cikin al’umma, inda mata ke dora alhakin ga maza, su kuma maza su dora wa mata laifin, koma yaya ne; da ni da ku mun yi ammana cewa yaudarar nan tana taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar alaka a tsakanin matasanmu maza da mata, kuma tana kawo babban tarnaki ga auratayya a cikin al’umma. A duk lokacin da namiji ya yaudari mace ko wata ta yaudari namiji daga lokacin sukan tsani auren, mace kan tsani duk wani namiji, haka shi ma namiji kan tsani duk wata mace. Sukan ji duk wata sha’awar aure ta fita daga gare su. Wannan ne ya sa na dauki bangaren maza don fitowa da ’yan mata irin hikimomi da dabarun da maza ke bi wajen yaudararsu ta hanyar kalamansu, domin duk yadda namiji ya kai wajen yaudara, to duk lokacin da ya kwankwasa ki ya ji babu wata kofa da zai yaudare ki to zai hakura. Ke dai ki nazarci wadannan muhimman bayanai kamar haka: 1. )Ko kin san jikinki tamkar sabon zinari ne a cikin leda sai namijin da ya biya sadakinki ne zai iya ganins...

Alomomin Balaga Ga Namiji Da Mace

"Da Farko Ina Rokon Ku Da Kuyi Rubutu a kasa Sannan Ku Latsa Kararrawa" "Sauye-sauyen da ke shafar samari da ‘yan mata a lokacin balaga" @ tsawo da nauyi na karuwa, kuma jijiyoyi (muscles) na bunkasa @ al’aura na kara girma @ za a iya haihuwa @ murya na kara zama babba  abubuwan da ke samar da sinadari a jiki (glands) zasu kara aiki, kuma zasu iya sa kuraje @ sinadarin da ke samar da zufa ko kuma gumi zai kara yawan zufar, da kuma warin ta @ gashi zai fara fitowa a karkashin hamata, da kuma gashin zaza @ mai yiwuwa rai ya rika baci nan da nan @mai yiwuwa a ji ana sha’awar daya jinsin, ko kuma jinsin ka @watakila kuma a kara farga da dangantaka tsakanin namiji da macce Sauye-sauyen da suka shafi ‘yan mata ► nonuna na kara girma, kuma mai yiwuwa su rika ciwo a lokacin @kan nono na kara fitowa @ kugu na kara girma @ al’aura na kara girma, kana kwayayen nan biyu (ovaries) zasu fara samar da kananan kwayaye @ idan balaga tayi nisa, a lokacin sai a fara al’ada Sauye sauye...

Hanyoyin Dacewa A Soyayya

Allah SWT ya halicci mutane daga asali ‘daya (Annabi Adam A.S), amma sai ya sanya kamanninsu ya banbanta, wani fari, wani baqi, wani kore (hahaha), wani gajere, wani dogo, wani mai qiba wani siriri (kamar ni ) da dai sauransu. Abin bai tsaya iya nan ba, haka ma abinda zuciya take so shima daban-daban ne, wani yana son ruwan sanyi, wani ko sai yace yana sa shi mura, wani yana son naman akuya wani ko sai yace duk danginsu basa cin naman akuya…. Wadannan banbance-banbancen sun samo asali ne daga cewa ta yadda kowa yake ganin abubuwa daban, hakan yasa idan aka zo zancen Masoyi/Masoyiya, to abin ba abu ne mai sauqi ba, shi yasa dole ne muyi hankali wajen zaben abokin/abokiyar zama. Mutane sun banbanta a abubuwa daban-daban, amma anan zamuyi magana ne kawai akan abubuwan da suka shafi soyayya, abubuwan kuwa sun hada da: • Jinsi (yare, gari, qabila,…) • Sifa (dogo, gajere, mai qiba, fari, baqi,…) • Ilmi (Addini, boko, wayewar zamani,…) • Hali (Sauqin kai, saurin fushi, kulawa, mantuwa,…) Jins...

Fitattun Shawara 15 Ga Matan Aure

Mutuwar aure a halin yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin Hausawa fiye da kowace kabila a duniya. babu  Shakka  a kowace ranar Allah sai daruruwan ma'aurata sun rabu da juna saboda rashin jituwa da kan shiga, tare da samu gindin zama a tsakaninsu. Me ya jawo hakan? Shin ba rashin bin ka'idojin zaman aurene ya haddasa hakan ba? Ko kuma haka siddan ruwa tayi tsami? A wannan karon zan yi tsokaci da shawarwari 15 ga ma'aurata musamman mata domin gano bakin zaren dake maida su zawarawa. Da fatan Allah (swt) yasa mu dace da abinda zamu karanta..... Asha karatu lafiya! 1.) KI RIKE MATSAYINKI: A koina kika samu kanki ki tabbatar kin rike matsayinki na matar aure. Wasu mata in sun fita zuwa gidajen biki ko suna da wuya suyi kama da matan aure. Wannan yana sa mazan banza suna binsu. In anyi rashin sa'a mai kwadayice, su rudeta har su kai ga aikata alfasha. 2.) KUYI HADIN GWUIWA: A matsayinki na matar aure akwai wasu ayyuka da suka kamata ki je kuyi tare da mijinki. Karki kuskura k...

Yadda Zaku Farfado Da Soyayya A Cikin Rayuwarku Na Aure

Ga bayani kan hanyoyin da ma’arata za su bi don farfado da so da kauna da inganta zamantakewa a tsakaninsu:= In muka lura da yanayin zamantakewar auratayya a wannan zamanin, za mu ga cewa yawanci zaman hakuri kawai ake yi ba zaman so da kauna da jiyar da juna dadi da taimakon juna ba. Da yawa mukan ji wadansu ma’aurata na cewa ai ba wata soyayya sai dai zaman hakuri ko a ce ana zaune ne domin yara kawai, alhalin in aka duba tarihi akwai lokacin da ma’aurata suke cikin tsananin soyayyar juna har suna jin ba abin da zai iya shafe soyayyarsu har abada. Amma a hankali sai su wayi gari su nemi wannan soyayya a tsakaninsu su rasa. Ga ma’auratan da ke juyayin ina soyayyarsu ta lokacin samartaka ko lokacin amarci take; su sani cewa wannan soyayyar tana nan, illa dai kurar canje-canje ta rayuwa da ta lullube ta kuma ta dusashe kaifinta. Wannan bayani in Allah Ya so zai karantar da ma’aurata yadda za su kakkabe duk wata kura da ta boye soyayyarsu da yadda za su wasa kaifinta da kara zafafa ta ha...

Wai Me Ke Cire Annashuwa Ne A auratayyanmu Na Yanzu

  A kasar Hausa, maganganu irin su “Aure yakin mata” dadaddu ne kuma sanannu. Abin da a mafiya yawan lokaci tun kafin matar ta shiga gidan auren yake alamta ma ta cewa, auren nan fa ba abin dadi ba ne. Hasali ma dai yaki ne, don haka ta shiga da shirinta. Haka nan shi kansa namijin yayin da a ka ce yau an daura wa wane aure, sai a ce ‘ya kwanto kura!’ Wasu ma har da kari, wai ba takunkumi. To ta yaya ne kuwa za mu iya danganta mutumin da ya kwanto kura da samun zaman lafiya....? Amma kuma abin mamaki a gefe guda idan za ka kalli babban ko kuma daya daga mafiya girman dalilan da Ubangiji subhanahu wa ta’ala ya shardanta gina aure a kansu, sai ka taras shi ne samar da nutsuwa ga ma’auratan. Bayan ma an sami nutsuwar har da soyayya da jin kai ko tausayawa juna. Haduwar soyayya da jinkai da nutsuwa kuwa shi ne wani yanayi wanda duk duniya babu wani yanayi da ya kai shi dadi! Kuma duk duniyar babu inda za ka same shi sai a garin aure! To amma idan haka ne, “Me Ya Hana Aure Dadi?” Akwai ...

Gaskiya Ne, "Duniya Budurwan Wawa,"

Daga Sheikh Ibrahim Disina ﺃﻭﻝ ﻣﺎ ﻳﺴﻘﻂ ﻣﻨﻚ ﻋﻨﺪ ﻣﻮﺗﻚ ﻫﻮ ﺍﺳﻤﻚ .. Farkon abinda zai bace maka shine …sunanka ﻟﺬﻟﻚ ﻋﻨﺪﻣﺎ ﺗﻤﻮﺕ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻋﻨﻚ ﺃﻳﻦ ﺍﻟﺠﺜﺔ .. ؟ Saboda haka ne idan ka mutu zasu ce gameda kai: Ina gawar? ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺮﻳﺪﻭﻥ ﺍﻟﺼﻼﺓ ﻋﻠﻴﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﺍﺣﻀﺮﻭﺍ ﺍﻟﺠﻨﺎﺯﺓ .. ؟ A lokacinda za su yi ma sallah su ce, “A kawo mamacin” ﻭﻻ ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺈﺳﻤﻚ Ba za su kiraka da sunanka ba ﻭﻋﻨﺪﻣﺎ ﻳﺸﺮﻋﻮﻥ ﺑﺪﻓﻨﻚ ﻳﻘﻮﻟﻮﻥ ﻗﺮﺑﻮﺍ ﺍﻟﻤﻴﺖ ﻭﻻ ﻳﻨﺎﺩﻭﻧﻚ ﺑﺎﺳﻤﻚ !.. Idan za su turbudeka zasu ce “Ku miko da gawar”. Ba za su kiraka da sunankaba ﻓﻼ ﺗﻐﺮﻙ ﻗﺒﻴﻠﺘﻚ ﻭﻻ ﻳﻐﺮﻙ ﻣﻨﺼﺒﻚ ﻭﻻ ﻧﺴﺒﻚ .. Kada ka bari kabilarka ko matsayinka ko asalinka ya rudeka … ﻓﻤﺎ ﺃﺗﻔﻪ ﻫﺬﻩ ﺍﻟﺪﻧﻴﺎ ﻭﻣﺎ ﺃﻋﻈﻢ ﻣﺎ ﻧﺤﻦ ﻣﻘﺒﻠﻮﻥ ﻋﻠﻴﻪ .. Duniya itace mafi kankantar abu. Inda muka fuskanta ne mafi girman abu. ﺳﻄﻮﺭ ﻣﻦ ﺫﻫﺐ .. Ga Wasu Shedaru na Zinari.. ﺍﻟﺤﺰﻥ ﻋﻠﻴﻚ ﺳﻴﻜﻮﻥ ﺛﻼﺛﺔ ﺃﻧﻮﺍﻉ؟؟ Nau’i uku na bakin cikin ne za su kasannce a gareka?? 1- ﺍﻟﻨﺎﺱ ﺍﻟﺬﻳﻦ ﻳﻌﺮﻓﻮﻧﻚ ﺳﻄﺤﻴﺎً ﺳﻴﻘﻮﻟﻮﻥ ﻣﺴﻜﻴﻦ 1- Mutaneda suka sanka sama-sama za su ce: Miskini (Bawan Allah) -2 ﺃﺻﺪﻗﺎﺅﻙ ﺳﻴﺤﺰﻧﻮﻥ ﺳﺎﻋﺎﺕ ﺃﻭ ﺃﻳﺎﻣﺎً ﺛﻢ ﻌﻮﺩ...

Amfanin Da Ridi Da Kwai Ke Yi A jikin Ya Mace

Ina ƙara yi wa masu karatun wannan shafi barka da  rana, tare da yin kira ga uwargida da ta ci gaba da bayar da himma wajen ganin an ci gaba da jajircewa kan ayyukan gida da kula da yara. A wannan makon ma za mu ɗora kan maganar da muke yi a kullum na gyara da kula da jiki, tun daga kan kwalliya da surar jikin mace. Ina ganin babbar ribar da uwargida za ta samu shi ne kula da kai da na iyali baki ɗaya da yara har da shi ma mai gidan. Amma idan kika saki jikinki, ki ka murɗe ko kika cure a waje ɗaya babu wani muhimmin aikin da za ki iya yi wa kanki ma, balle ki sauke waɗancan nauyayan haƙƙoƙin da ke kanki. Za mu yi magana a kan wasu abubuwa ne guda biyu waɗanda a kullum muna amfani da su, amma galibi ba mu cika sanin amfaninsu a jikinmu ba. Misali ƙwai, da dama ana ganin cewa babu abin da ƙwai ke ƙara wa mutum a jikinsa illa don jin daɗi ne kawai, alhali kuwa ba haka abin yake ba. Ƙwai na taka muhimmiyar rawa wajen rage gurɓataccen jini, kitse da rage duk wani nau’i na abin da mace ...

Sirrin Samun Saurayi Nagari

Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ta na mace ta taba kokarin samun namijin kirki amma bata samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma yadamu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki. A watan azumi da ake ciki, ki kokarta wajen kyautata dangantakarki da Allah, ki bada kyauta ga mabukata. Haka ki yawaita fara'a da nafilfilin dare, da rokon Allah ya kawo miki miji nagari da kuma dacewa da sa'a a wannan rayuwar. Ki rage yawan fada, da yawan surutu tsakanin ki da sauran 'yan uwa mata ko maza. Kada kuma azumi ya hanaki kwalliya da gyaran jiki, yadda ya kamata ace ko wace mace na yi. Kokarta wajen kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi. To fara duba kanki, ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadd...

Yadda Zaki Sa Gabanki Yayi Danko Koda Kin Haifi Yara Goma Mijinki Ya Ji Dadi

         "Da Farko Ina Rokon Ku Da Kuyi Rubutu a kasa Sannan Ku Latsa Kararrawa" Step 1: yadda macen da ta haifu xata gyara kanta da kuma yan'mataa da suka bude kafin ashiga daga ciki da yan'matan da suka hadu da qaddara ta rpe*** 1)Garin Zogale 2)Qwaro 3)Man kadanya 4)Man shanu... 5)Man xogale..... Zakihadasu waje daya ki cakudasu ki barsu su hade jikinsu in mataar aure ne wacce ta haifu ko kuma bata taba haifuwa ba zaki dibi kadan da yamma kiyi matsi dashi zuwa magarib xaki hade tsam tamkaar sabuwar budurwa saiki wnke wlh saikun bani labari. ***Wanda akai rpe nata bisa kaddara yan'mataa kenan ko wadda ta bude kafin ta shiga daga ciki*** ke kuma kina saura 1week Aurenki zakiyi amfani dashi for 3dys.....zaki hade koda yatsa baxai iya shigewa wajen ba....amma yan' mata Virgine wlh kar wacce ta kwada wannan sbda zaki shiga Uku dan zai xama maki matsala....be careful ***Steps2 Iyaye tun yara suna qanana basu lura da tsarkin mu maike rage qima...

MAKUDAN LADAN DA AKE SAMU BAYAN AN GAMA JIMA'I DA IYALI

An ruwaito cikin littafin shifa’u sudur” cewa Annabi (SAW) yace idan mace ta shiga cikin shaanin hidimar mijinta ko tayi kwalliya domin neman yardar sa. ALLAH (SWT) zai rubuta mata lada guda goma kuma ya daukaka mata darajarta idan mijinta ya kirata tayimasa biyayya har ta dauki ciki zata kasance tanada ladan mai yin azumi da salloli dare kullum a wajen daukaka kalmar ALLAH wato jihadi”. A’isha(RA) tace hakika an baiwa mata alheri masu yawa to menene ku agareku maza? Sai annabi(SAW) yayi dariya yace “Babu wani mutum da ya riki hannun matarsa da nufin yin jima’i da ita sai ALLAH(SWT) yarubuta masa kyawawn ayyuka guda biyar idan yahada wuya da ita yanada lada guda goma idan ya sumbacceta (kiss) yanada lada guda ashirin idan ya sadu da ita ALLAH (SWT) zai bashi ladan da yafi duniya da abunda yake cikinta idan yatashi domin yin wankan (janaba) ruwan wankan bai gudanaba a wani bangaren jikinsa sai an shafe zunubansa a kuma daukaka masa darajarsa. Ana bashi ladan abinda yaf...

SIRRIN MIJINKI DOMIN SAMIN MATSAYI A GURINSHI FIYE DA KOWA

SIRRIN MIJINKI DOMIN SAMIN MATSAYI A GURINSHI FIYE DA KOWA* * Mata bari na baku wata sirri, ina matan gidan nan suke ??? Kufirfito kuji, wata sabuwa inji yan cac Duk lokacin da kike saduwa da mai house, ki tabbata lokacin da dick dinsa yake cikin farjinki, ki tsuke gabanki sosai, kada ki sake ta sam. Most especially idan ya gama releasing zai fitar da dick dinsa agabanki, ki tsuketa sosai. Wallahi, saiyaji kamar zai suma don dadi. Kuma ina tabbatar muku wannan sirri ne babba wadda ba kowacce macece take amfanida itaba. Kuma wallahi yana sa namiji yaji baya sha'awar saduwa da kowacce mace saike, kuma ko yayi sai yajiki daban da duk macenda zai taba arayuwarsa matuqar batasan wannan sirrinba. Sai angwada akansan na qwarai. MENENE SIRRIN KUKAN MACE GABAN MIJINTA A LOKACI DA TA BATA MASA RAI YAYI FUSHI DA ITA?? %%%Dukkan mace da takema mijinta kuka lokacin da yayi fushi yana qara masa sonki da qaunarki yana qara jin dadi aransa sbda kin nuna masa kin damu kuma kin qara nuna masa yanada...

HADIN SABUWAR MACE AMARYA

kawata kina so ki koma sabuwa koda kinyi haihuwa goma idan kika bari gabanki ya zama kato kamar rami maciji mijinki bazai yarda ya zauna dake ba yaga kofar mutuncinki kamar rijiya saboda fadi idan ba kya so mutumci da darajarki ta zube a wajen maigida saiki nemi magani wanda zai saka gabanki ya tsuke maigida sai yayi da gaske zai shiga yaji kin matse shi gamgam dadi sai mace mai gyara jikinta. Mata da yawa musamman yan mata basu fahimci matsiba ballantana susan lokacin yinsa da kuma yanda akeyinsaba Sudai kawai daga lokacin bikin mace yazo sai kaga tanata saka abubuwa a farjinta da sunan matsi kuma wani lokacin wannan shine yake jawowa mata infection YAYA AKE MATSI? shidai matsi kala ukune kuma kowanne yanada muhimmanci a wajen mace matukar tanaso lokacin jima i tarinka rudarda mijinta yana sumbatu.. (1) akwai matsi Wanda akeyinsa don mace farjinta ya tsuke ya zama amatse shikuma wannan babu meyi sai Wacce farjinta ya bude ko dalilin haifuwa ko kuma anyi mata fyade ma ana wacce ta rasa...

Karanta Labarin Soyayya Mai Ban Tausayi

wasu masoyane biyu suna mutuqar son junansu fiye da misali sai wata rana budurwar tagayyaci saurayinnata zuwa gidansu domin yasha ruwa agidan ma’ana yayi buda baki daganan sai yagaishe da iyayenta sannan sauran yan uwanta suganshi domin suna bukatar hakan kawai surayinnan ya amsa gayyata sukasa lokachi lokachi yayi sai yaje gidansu. budurwartashi bayan yaje gidan sai ta fara gabatar dashi agaban mahaifinta sannan takaishi cikin gidansu gurin mahaifiyarta sannan duk yan uwanta sukazo gurinsa …one-by-one… duk suka gaisa iyayenta da yan uwanta duk sukaji sun amince dashi saboda ganin cancanta da sukayi daga gareshi kowa yafita waje akabarsu su biyu kacal a falo domin yasha ruwa acikin nutsuwa da kwanciyar hankali akakawo masa kayan marmari da kayan ciye-ciye da shaye-shaye yana zaune yana chi ita kuma tana tayashi hira can sai yazo shan lemo ya daga kofi ya fara shan lemo sai yaji wata kalma mai dadi tafito daga bakinta cewa gaskiya naga iyayena duk sun yarda dakai yanzu maganar aurenmu k...

Ko Kun San Banbanci Tsakanin Soyayya Da Sha'awa

Darasin yau yana daya daga cikin mahimman darussa na wannan shafin mai albarka, domin magana ce a kan matsalolin da suke faruwa a tsakanin ma’aurata, wato sabbin shiga, komai wayewar mace da namiji, ko ta yi ta sayar da kanta a matsayin ‘yar auren holewa in dai ba ta zauna da namiji a matsayin matarsa bisa shari’a ba to bakuwa ce, matar da ta yi rayuwa da namiji koda shekara daya tal ta yi da shi, tana da abubuwan da za ta fadi wadanda tsohuwar ‘yar daduro ba ta sani, haka namijin da bai taba aure ba koda kuwa ya yi ta tamfatsewarsa da mata in dai bai taba aure ba to akwai abubuwa da yawa wadanda sai an yi masa bayani..." Babban dalilan da suke haifar da matsaloli a tsakanin wasu ma’auratan a shekarar farko suna da alaka ne da rashin sabawa da zamantakewar aure, dukkan su biyu sun yi ta bata wa juna ne lokaci a rayuwar da ba ta hakika ba, namiji ya rika jin cewa shi ne komai na ta, in ‘yar ajiyar zuciya ta yi sai ya fara kokarin sanin dalili, duk abin da take so nan da nan za a yi...