(1) Baki kai shekaru 50 a duniya ba amma zuciyarki tace miki kin tsufa kuma kika yarda kin tsufa din har ma kike aiki da hakan.
(2) Baki kai shekaru 50 ba kin watsar da gayu, gyaran jiki na musamman, da kuma dinkuna na yara domin mijinki.
(3) Baki kai shekaru 50 ba kina zama da daurin kirji alhalin ba wanka zaki shiga ba, duk wanda ya ganki ji yake kamar ya mare ki in baki sani ba.
(4) Baki kai shekaru 50 ba kina yawo ko ina babu rigar mama (brazier) da dan kamfai (pant), ba kama jiki yayin tafiya kin saki jiki wai ke kin tsufa, kin tasa ruwan sanyi a gaba, kina yawo tsakar gida ba takalmi.
(5.) Kin haihu baki damu ki gasa jikinki ba da zaman ruwan zafi ba da cin abinci ki koshi, da sanya hijab da safar kafa har kiyi shekaru 40.
(6.) Kin haihu baki son ki nutsu ki tanada kanki ba kina rayuwa kaman namiji bakya bin sassan jikinki da gyara, bakya damuwa da cin abinci, domin rashin abinci shi yafi komi lalata mace baki an kara ba har wata haihuwan ta sameki, kinga kin fara rushewa kenan.
(7.) Baki kai shekaru 50 ba amma kin bar fuskarki tayi kaushi ta koma ta tsohuwa ba ruwan ki da gyarata, jikinki duk ya bushe, ba kyan gani ballantana yayi kyau da laushi, ai ba wanda zaki burge.
(8)kin zauna baki kai shekaru 50 ba kince gyaran fata sai yara ko kuma baki da lokacin sa saboda yara amma kina da lokacin karanta littattafai, sauraron masu karanta shi da kallon fina-finai.
(9) Baki kai shekaru 50 ba kin raba kanki da shafa hoda, kin raba kanki da kamshi toh ya kike so mijin yayi
Comments
Post a Comment