Gwamnatin Najeriya ta ce wasu dabi'u da shugaban kungiyar harka Isalamiyya na Najeriya ya nuna a kasar Indiya da ka iya kunyata gwamnatocin Najeriya da India na daga cikin dalilan da suka sanya aka mayar da shi gida. A ranar Juma'a 16 ga watan Agusta ne dai Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa Najeriya bayan yunkurin kula da lafiyarsa da mai dakinsa Zeenat ya ci tura a kasar Indiya. Malamin dai a cikin wani sako da ya fitar ta faifan bidiyo gabanin komawarsa Najeriya, ya ce yana ganin ba zai samu kulawar da ta dace ba, kasancewar ba a bar shi ya gana da likitocin da suka cancanta ba. Sannan gabanin hakan ya yi zargin cewa an tsananta tsaro a asibitin da yake zaune, inda ya ce akwai matukar takura ga rayuwarsa. Me zai faru da Zakzaky bayan da ya koma Najeriya? Ibrahim Zakzaky ya so bijirewa a Indiya - Gwamnatin Najeriya Me ya sa 'yan Indiya ke 'maraba' da Zakzaky? Sai dai bayan komawar malamin Najeriya, kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ruwaito cewa babbar sakatar...
Mace Kayan Dadi