Innalillahi Wa Inna Ilaihi Raji'un!!!
Matar Dan Jarida Ta Burma Wa Mijinta Wuka A Kaduna!
Daga Mukhar Othman
Sanannen dan jarida ma'aikacin gidan Rediyon Najeriya na Kaduna Malam Yahaya Maiyaki ya tsallake rijiya da baya, biyo bayan burma mishi wuka da matar shi ta yi a gidan sa da ke Kaduna.
Maiyaki wanda a halin yanzu yake kwance Asibiti likitoci na kokarin ceto rayuwar shi, an ce wata 'yar hatsaniya ce ta shiga tsakanin shi da matar tashi a daren jiya, inda ba tare da bata lokaci ba matar ta fusata ta fada cikin daki ta dauko wata zundumemiyar wuka ta burma mishi a ciki, nan take ya fadi a sume.
Ihun da ya yi shi ya ankarar da makwabta halin da ake ciki, nan take aka shigo domin ganin me ke faruwa, yayin da aka samu matar na yunkurin sake burma mishi wukar a karo na biyu, take anan jama'a suka kwace wukar a hannun ta sannan aka yi gaggawar kai shi asibiti.
Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar cafke matar kafin ta gudu, inda ake cigaba da binciken lamarin.
Comments
Post a Comment