Gwamnatin Najeriya ta ce wasu dabi'u da shugaban kungiyar harka Isalamiyya na Najeriya ya nuna a kasar Indiya da ka iya kunyata gwamnatocin Najeriya da India na daga cikin dalilan da suka sanya aka mayar da shi gida.
A ranar Juma'a 16 ga watan Agusta ne dai Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa Najeriya bayan yunkurin kula da lafiyarsa da mai dakinsa Zeenat ya ci tura a kasar Indiya.
Malamin dai a cikin wani sako da ya fitar ta faifan bidiyo gabanin komawarsa Najeriya, ya ce yana ganin ba zai samu kulawar da ta dace ba, kasancewar ba a bar shi ya gana da likitocin da suka cancanta ba.
Sannan gabanin hakan ya yi zargin cewa an tsananta tsaro a asibitin da yake zaune, inda ya ce akwai matukar takura ga rayuwarsa.
Me zai faru da Zakzaky bayan da ya koma Najeriya?
Ibrahim Zakzaky ya so bijirewa a Indiya - Gwamnatin Najeriya
Me ya sa 'yan Indiya ke 'maraba' da Zakzaky?
Sai dai bayan komawar malamin Najeriya, kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ruwaito cewa babbar sakatariyar ma'aikatar yada labarun kasar, Mrs. Grace Gekpe ta ce halayyar da Sheikh Zakzaky ya nuna a kasar ta India ne ta sanya dole a mayar da shi gida.
A cewar wata sanarwar da ta fitar "A wani yunkuri na wancakali da ka'idoji na kasa da kasa, jagoran na IMN ya fara tuntubar wasu lauyoyi a Indiya da nufin neman mafaka a kasar".
"Ya kuma tuntubi wasu kungiyoyi masu zaman kansu kamar hukumar kare hakkin dan'adam ta muslunci, da wasu kungiyoyi masu alaka da akidar Shi'a domin ganin ya samu nasarar neman mafakar.
Sanarwar ta yi bayanin cewa inda Sheikh Ibrahim Zakzaky ya samu nasarar samun umurnin kotu a kasar Indiya na neman mafaka, to da hakan ya saba wa ka'idojin da kotu ta gindaya a Najeriya game da shari'ar da ake masa.
Bugu da kari sanarwar ta zargi matar Sheikh Zakzaky, Zeenat, da laifin kokarin haifar da rashin jituwa tsakanin jami'an tsaron Najeriya da na Indiya, a lokacin da ta zargi jami'an tsaron Najeriya da laifin kisan 'yayanta.
Ita dai gwamnatin Najeriya ta yi kokarin bin umurnin wata babbar kotu ne ta jihar Kaduna, wadda ta amince wa Sheikh Ibrahim El-Zakzaky da matarsa Zeenat su tafi kasar Indiya domin neman lafiya.
Malamin yana fama ne da rashin lafiya tun bayan kama shi da aka yi da mata
Comments
Post a Comment