An ce, hanyar da mace za ta bi ta mallaki zuciyar namiji biyu ne: cikinsa da shimfidarsa. Ni na qara da daya, sun zama uku: kunnensa.
‘Yar uwata namiji wawa ne. Namiji soko ne. Namiji gaula ne. Amma fa a gaban matar da ta san kanta, ta yarda da kanta, kuma ta laqanci mijinta. Lura da kyau, ba cewa aka yi mace mai kyau, asali ko ilimi ba, a’a, macen da ta san ita mace ce, ta kuma yarda da hakan, sannan kuma ta karanci dabi’ar abokin zamanta. Irin wannan mata, ita ce ke zama ji da gani da kuma tunanin mijinta
Na san cewa kin san duk yadda za ki inganta biyan buqatar cikin mijinki da shimfidarsa, don haka ba sai na ce komai a kai ba, musamman saboda ma na san cewa, dubban masanan da suka fi ni cikin mata da maza sun gabatar da bayanai a kai da dama. Inda kawai zan dan qara, shi ma ba don ba a yi ba, sai don ba a cika yi din ba, shi ne bangaren gamsar da kunnuwan mijinki da hira.
Sama da kashi 50 na rayuwar namiji tana ga harkokinsa ne na waje, yayin da sama da kashi 50 na rayuwar mace tana ga harkokinta ne na cikin gida, ko da kuwa ma’aikaciya ce. A nan, ‘Yar uwata, kina buqatar dan zaburowa da cicciba matsayinki. Saboda ki san yadda mijinki yake rayuwa a harkokinsa na waje. Ba fa ina nufin ki yi binciken sirrorinsa ko neme-nemen matansa ba, No! Wato nufina ki san sana’arsa ko kasuwancinsa, ko aikinsa da wasu harkokinsa da ba zai damu ki sani ba. Ki yi qoqari ki san ababe da dama game wadannan. Idan kika sani, sai ki zama abokiyar hirarsa a kai. Ki sa shi jin cewa, kin yi wa harkarsa sanin da dolensa ya buqaci shawararki ko ya yi hira da ke a kai. Da zarar kin samu wannan matsayi, to, kin gama mallake mijinki, amma fa da sharadin kina inganta ciki da shimfidar can, yes!
‘Yar uwata, soyayyar nan da kike gani wacce ke ba kya gajiya da ita a zubin halittar dabi’arki, wallahi gundurar namiji take yi. Maza da yawa sun sha yi wa matansu tsaki, ko gwasale, wasu ma har banka wa matan ashar yayin da suka kira su da tsakar rana don su nuna ko su furta mu su kalaman qauna. Saboda a lokacin, ba abin da ke gaban mazan ke nan ba. Haka abin yake a wani zubin idan miji ya dawo gida. Wai ba ki lura cewa in mijinki ya ga abokansa ya fi sakin jiki da su a hira a kanki ba? Ai ba wai don yana fifita su a kanki ba ne, a’a sam, sai domin kawai hirar da abokan za su yi masa ke ba za ki yi kwatankwacinta ba. To don me ke ma ba za ki koyi hirar ba ‘yar uwata?
Sayyada Rahma Abdulmajid ta samu ikon mallake zuciyar mijinta ne saboda ba ta tsaya ga iya girki da hidimar gida ba, ta yi qoqari ta laqanci yadda aikin soja yake da kyau. Don haka sai ta zama abokiyar hirar sojan mijinta a lokacin da yake raye. Idan ba a manta ba, a duniyar nan ta Facebook, da kanta ta taba fadin cewa, “salaryn” mijinta kai tsaye yake zuwa wurinta, ita ce take tsara yadda za a yi. A lokacin da ta yi maganar, na lura sai mata suka yi ta yaba wa mijin, saboda ba su san cewa ita ce ta haifar da hakan ta hanyar maida kanta amintacciya shi kuma ta maida shi abokin hira a kan kowane topic ba. Har zuwa yau din nan, wannan ilimi da ta samu kan sha’anin gidan soja, ya taimaka wurin maida ita “expert” a cikin mata idan ana batu na tsaro. Ke nan baya ga damar mallakar miji, koyon harkokinsan ma zai iya amfanar ki a kebantacciyar rayuwa ‘Yar uwata. Na sha ganin matan qabilu a nan Abuja da Kaduna suna cigaba da gudanar da jagorancin kamfanoni ko kasuwancin mazajensu yayin da suka mutu. In ba su da ilimin hakan tun suna raye, ba za su iya ba.
Wasu mata sukan ji cewa, ba su da wata hira da za su yi da mazajensu wacce ta wuce qorafin abin da babu a gida da qorafin rashin lafiyar wani ahalin gida da hirar iyayenta da ‘yan uwanta da qawayenta. Ba ruwanta da halin da mijinta yake ciki bare ta yi hira da shi a kai. Irin wannan hali ke sa maza fita waje hira da wasu abokai, wasu ma har su dade a can, daga nan har su hadu da wasu matan da za su qwace miki miji kina ji kina gani. Irin wannan hali ke sa maza fita harkar mata a cikin gida, ko tasa talbijin da kallo ko waya da chatting.
‘Yar uwata, rashin koyon ilimin rayuwar harkokin mijinki na waje, da rashin nuna kwadaituwa a kai, gazawa ce babba daga bangarenki. Don Allah ki gyra.
Comments
Post a Comment