Skip to main content

SAHIHIN MAGANIN KARFIN MAZA DOMIN GAMSAR DA MATA HUDU A LOKACI DAYA


Shi maganin Qarin kuzarin Namiji, ya bambanta ne daga wani mutumin zuwa wani. Misali maganin da wani yasha yaji dadinsa, ba lallai ne kai idan kasha yayi maka aiki ba. Amma dai ga wasu abubuwan da mun ta'ba yin bayaninsu anan Zauren Fiqhu kuma mutane da dama sunce sunyi amfani dasu kuma sunji dadinsu :
1. MAN HABBATUS SAUDA : Ka samu shayin Na'a-Na'a wanda aka sanya Na'a-Na'a din sosai. Ka zuba masa Man Habbatus Sauda cokali 1, sannan kasha. Safe da dare kafin kwanciya.
Ko kuma ka samu Qwan Tattabara ko Qwan Kazar gida guda biyu ko uku, Ka zuba garin habbatus Sauda cokali guda aciki. Agauraya a soyashi da Man Habbatus Sauda ko Zaitun, sannan kaci.
2. SAIWAR GINSENG : Wani itace ne ingantacce wanda ake kawoshi daga Qasar China. Idan Namiji ya yawaita amfani dashi zai samu Qarin Kuzari da girma.
3. KANKANA : Kankana tana kunshe da irin sinadarin dake cikin Kwayoyin Viagra. Don haka tana Qara Qarfin Namiji sosai, kuma 'Ya'yanta suna Qara ma Namiji girma ba tare da wata illa ga jikinsa ba.

Ka samu Qatuwar Kankana ka yanka bayan Magriba ko Isha'i ka shanyeta gaba daya. Kuma ka rika taunewa kwallon. In sha Allahu zaka ji bambanci mai yawa.
Kuma zaka iya samun ruwan kankana din, Ka matsa lemon tsami guda 1 ko 2 acikinsa sannan kasha. In sha Allahu zaka ji bambanci mai yawa.

4. RUWAN CITTA : Ka samu Madarar Peak ko Luna, ka tsiyaya ruwan chitta ko kuma garinta daidai misali. Sannan ka samu garin Kustul Hindi cokali guda ka zuba aciki, sannan ka sanya zuma daidai Misali sannan ka shanye, Minti 30 kafin kwanciya.

5. MAN JIRJEER : Yawancin Maza masu fama da raunin Mazakuta, Basur ne ke damunsu ko kuma Majinar Kwankwaso (Waist).

Shi Man Jirjeer yana Qone irin wannan Majinar ne, har majinar Qirji. Don haka yana Qara ma Namiji Qarfi.
Wadanda suke zaune a Qasashen Larabawa kamar Saudia ko Misra zasu iya samun ganyensa 'danye cikin sauki. Domin shi suke sanyawa a saman abincinsu kamar yadda muke amfani da Lettuce anan.
6. ZOGALE : Bawon jikin itacen Zogale idan aka shanyashi aka dakashi, ana hadawa da Madara ko Zuma ana sha. Shima yana Qara kuzarin Namiji sosai.
7. Kwallon Taura : Bayan an gwaguye abinda ke jikinsa, adauki kwallon adakashi gaba dayansa har 'dan cikinsa. Idan ya zama gari sai arika sanya cokali guda acikin shayi ma madara ana shansa minti 20 kafin kwanciya.
ABIN LURA==========
Yawancin wadannan Magungunan ba wai daga yin amfani dasu sau daya ko sau biyu zaka ga chanji gaba daya ba. Dole sai ka juri amfani dasu yau da kullum kana hadawa da Motsa jiki, kuma ka rage amfani da abincin zamani wadanda suke kunshe da sinadarai masu Qarfi. Irin su Lemon kwalba, Biscuits, Chocolate, Alawa, Succarine, Farin Magi, etc.
Ka koma amfani da kayan sha irin na gargajiya kamar irin su Kunun aya, Mazarkwaila, 'Ya'yan itace irin su gwanda, ayaba, Lemo, Karas, etc.
Allah yasa mu dace.
WALLAHU A'ALAM.
DAGA ZAUREN FIQHU 31-10-2016 (29-01-1438)
DON GIRMAN ALLAH KAR WANI YA CHANZA MANA ABINDA MUKA RUBUTA ZUWA GA SON RANSA. ('Barayin Fasaha aji tsoron Allah dai).

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Sirrin Samun Saurayi Nagari

Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ta na mace ta taba kokarin samun namijin kirki amma bata samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma yadamu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki. A watan azumi da ake ciki, ki kokarta wajen kyautata dangantakarki da Allah, ki bada kyauta ga mabukata. Haka ki yawaita fara'a da nafilfilin dare, da rokon Allah ya kawo miki miji nagari da kuma dacewa da sa'a a wannan rayuwar. Ki rage yawan fada, da yawan surutu tsakanin ki da sauran 'yan uwa mata ko maza. Kada kuma azumi ya hanaki kwalliya da gyaran jiki, yadda ya kamata ace ko wace mace na yi. Kokarta wajen kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi. To fara duba kanki, ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadd...