Skip to main content

Ilolin Yaudara Tsakanin Yan Mata Da Samari

Lura da yadda yaudara ta zama ruwan dare a cikin al’umma, inda mata ke dora alhakin ga maza, su kuma maza su dora wa mata laifin, koma yaya ne; da ni da ku mun yi ammana cewa yaudarar nan tana taka muhimmiyar rawa wajen tabarbarewar alaka a tsakanin matasanmu maza da mata, kuma tana kawo babban tarnaki ga auratayya a cikin al’umma.


A duk lokacin da namiji ya yaudari mace ko wata ta yaudari namiji daga lokacin sukan tsani auren, mace kan tsani duk wani namiji, haka shi ma namiji kan tsani duk wata mace. Sukan ji duk wata sha’awar aure ta fita daga gare su.

Wannan ne ya sa na dauki bangaren maza don fitowa da ’yan mata irin hikimomi da dabarun da maza ke bi wajen yaudararsu ta hanyar kalamansu, domin duk yadda namiji ya kai wajen yaudara, to duk lokacin da ya kwankwasa ki ya ji babu wata kofa da zai yaudare ki to zai hakura. Ke dai ki nazarci wadannan muhimman bayanai kamar haka:
1. )Ko kin san jikinki tamkar sabon zinari ne a cikin leda sai namijin da ya biya sadakinki ne zai iya ganinsa? Ki yi kokarin kare mutuncinki.
2.) Ko kin san duk saurayin da yake gudun haduwa da iyayenki ko magabatanki, mayaudari ne ba mai son yin aure ba?
3.) Ko kin san duk saurayin da ya fiye magana a kan kirar jikinki da kyan fuskarki, mai sha’awa ce ba mai SO ba?
4.) Ko kin san duk saurayin da ya cika tattara hankalinsa a kan ado da kwalliyarsa, ba zai iya kula da gida ba?
5.) Ko kin san duk saurayin da yake damuwa da zancen dukiyar gidanku ba halayenki ba, ba son aure yake yi miki ba?
6.) Ko kin san duk saurayin da ya fi damuwa ya taba miki hannu ko jiki, ba son aure yake yi miki ba?
7. )Ko kin san duk saurayin da yake son ki rika zuwa wurinsa (dakinsa), ko ki rika raka shi wurare, ba son Allah da Annabi yake miki ba?
8.) Ko kin san duk saurayin da ya cika labarin matsayi da darajarsa, ba zai iya mutunta ki ba?
Wadannan da wasunsu na daga cikin dabi’un samarin da ya kamata ’yan mata da zawarawa su lura da su don gudun fadawa tarkon mayaudarabn samarin zamani.
Saura me? Lallai kwadayinki da son abin duniyarki na taka rawa wajen yi miki yaudara, matukar kina da kwadayi a nan matsalar take; masu iya magana na cewa; idan kunne ya ji to gangar jiki ta tsira

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

LAKANIN DA HADIN KARIN GIRMAN NONO DA KUMA DANKO DA MATSE GABA GA MATA

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa. Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..   Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:====== A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin kudin ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu. Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa: Kankana Ayaba Gwanda Goba Lemo Tumatir Rake Aya Kwakwa Dafaf...