Skip to main content

Hanyar Da Zai Kai UwarGida Aljannah

Assalamu alaikum ’yan uwa maza da mata musamman magidanta da ke bibiyarmu a wannan fili da muke tattauna lamurran da suka shafi zamantakewarmu da iyali da tarbiyya a bisa mahanga ta shari’a da kuma al’adunmu.

A yau zan yi magana ne a kan garabasar da Allah Madaukaki Ya tanadar wa uwargida in har ta tsare abububuwa uku a nan gidan duniya za ta samu rabo mai tsoka a Lahira.
In muka dubi mu’amalarmu ta yau da kullum Allah Ya halicci mata a bisa wata irin daraja da ta dara ta maza irin yadda aka kebance su daga wahalhalu na nema da ciyar da kai.
Su kuma maza Allah Ya dora musu hakkoki na ciyarwa da kula na mata da ’ya’ya da iyaye da duk wani wanda ya jibince su.
Ta bangaren ibadoji kuma mata an kebance su da tsare ibadojinsu a cikin gidajensu yayin da maza aka dora musu fita masallatai da fita jihadi da sauransu.
Akwai ayoyi da hadisai da dama da suka yi magana a kan mace ta zauna cikin gidanta kuma ta tsare hakkokin da Allah Ya dora mata domin a gidanta za ta samu lahirarta.
Akwai Hadisin Annabi (SAW) da ya ce “Idan mace ta yi imani da Allah ta kiyaye salloli, ta yi biyayya ga mijinta za ta shiga Aljanna.”
Akwai wani Hadisin da yake cewa “Duk matar da ta mutu mijinta na yarda da ita za ta shiga Aljanna.”
Akwai kuma Hadisin da Annabi (SAW) ke cewa “Aljannar mace na karkashin tafin mijinta.” Ke nan idan har ba ta yi masa biyayya ta yadda zai yarda da ita ba, ba za ta shiga Aljanna ba.
Sau tari mata na yi mini tambayoyi cewa me ya sa muka fi magana a kan hakkokin maza, su mata ba su da hakkoki ne?
Sai in ce yadda maza suke da hakkoki haka mata suke da su, sai dai kamar yadda na yi bayani a sama kusan duk ribar ’ya mace ta rataya ne a dakin mijinta wanda saba wa hakan na iya jefa ta cikin hallaka.
Sannan na biyu, uwargida sai ki gode wa Allah da har ake yawan fadakar da ku a kan hakkokinku don kuwa Hausawa na cewa “Gyara kayanka ba ya zama sauke mu raba.
Akwai wani sanannen Hadisi da Annabi (SAW) ya yi Isra’i da Mi’iraji yayin da aka zagaya da shi cikin wuta ya ce “Ya ganta cike da mata da masu kudi,” sai aka tambaye shi me ya sa mata suka fi yawa a wuta? Sai ya ce “Saboda suna saba wa mazansu. Sannan ya yi umarnin su yawaita yin sadaka.
Uwargida ga garabasa sai dai sai an yi hakuri domin nasara tana tare da hakuri.
Na san irin barazanar da kuke fuskanta a gidajen mazanku, amma saboda ku a cikin gida kuke kuma sai abin da aka kawo muku, wanda kuma duk inda kuka ga biyayya tana tare da hakuri.
Da fatan Allah Ya sada mu da ladan masu hakuri,  Ya ba mu dacewa da Aljanna Madaukakiya.
Sanusi Hashim Abban Sultana
Mai sharhi ne a kan al’amurran da suka shafi yau da kullum.  Ya turo wannan sako ne daga Jihar Katsina.

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Yadda Zaki Sa Gabanki Yayi Danko Koda Kin Haifi Yara Goma Mijinki Ya Ji Dadi

         "Da Farko Ina Rokon Ku Da Kuyi Rubutu a kasa Sannan Ku Latsa Kararrawa" Step 1: yadda macen da ta haifu xata gyara kanta da kuma yan'mataa da suka bude kafin ashiga daga ciki da yan'matan da suka hadu da qaddara ta rpe*** 1)Garin Zogale 2)Qwaro 3)Man kadanya 4)Man shanu... 5)Man xogale..... Zakihadasu waje daya ki cakudasu ki barsu su hade jikinsu in mataar aure ne wacce ta haifu ko kuma bata taba haifuwa ba zaki dibi kadan da yamma kiyi matsi dashi zuwa magarib xaki hade tsam tamkaar sabuwar budurwa saiki wnke wlh saikun bani labari. ***Wanda akai rpe nata bisa kaddara yan'mataa kenan ko wadda ta bude kafin ta shiga daga ciki*** ke kuma kina saura 1week Aurenki zakiyi amfani dashi for 3dys.....zaki hade koda yatsa baxai iya shigewa wajen ba....amma yan' mata Virgine wlh kar wacce ta kwada wannan sbda zaki shiga Uku dan zai xama maki matsala....be careful ***Steps2 Iyaye tun yara suna qanana basu lura da tsarkin mu maike rage qima...

Yadda Zaka Fahimci Mace Na Sonka

Hikimomin Gane Idan Ana Sonka:======== Idan kana son ka gane da gaske ana sonka, wadannan sune alamomin. Wannan rubutu yana da dangantaka ne da duk wanda yake tantamar soyayyar da ake masa, ta haka ne zai gane, duk da cewa dai soyayya ta gaskiya ba a gane ta a lokaci kankani kasancewar tana shiga ne sannu a hankali. Ita soyayyar gaskiya tana toho ne da yaduwa a cikin zukatan mutane a yayin da ake zama ana fahimtar juna. Wani abin bakin cikin yanzu shine soyayyar gaskiya ba ta cika dorewa ba. Wani lokacin sai an yi nisa sai a ~ata ko ta lalace, Wannan bayani ya gudana ne ga duk wani masoyi da yake shakkun masoyiyarsa ko tana son sa ko ba ta son sa. • Idan tana yawaita fada maka tana sonka kuma ka tabbatar da hakan, tana jin son sosai a zuciyarta, sannan kuma tana jin son ba tare da tana rokonka wani abu ba, sakamakon hakan ba ta jin bacin rai kuma ba ta bata maka rai. • Idan tana magana ka rinka kula da idonta, wajen magana za ka iya gane mace in tana sonka idonta yana nuna alamun tausa...