Mutuwar aure a halin yanzu ya zama ruwan dare a tsakanin Hausawa fiye da kowace kabila a duniya. babu Shakka a kowace ranar Allah sai daruruwan ma'aurata sun rabu da juna saboda rashin jituwa da kan shiga, tare da samu gindin zama a tsakaninsu.
Me ya jawo hakan? Shin ba rashin bin ka'idojin zaman aurene ya haddasa hakan ba? Ko kuma haka siddan ruwa tayi tsami? A wannan karon zan yi tsokaci da shawarwari 15 ga ma'aurata musamman mata domin gano bakin zaren dake maida su zawarawa. Da fatan Allah (swt) yasa mu dace da abinda zamu karanta..... Asha karatu lafiya!
1.) KI RIKE MATSAYINKI: A koina kika samu kanki ki tabbatar kin rike matsayinki na matar aure. Wasu mata in sun fita zuwa gidajen biki ko suna da wuya suyi kama da matan aure. Wannan yana sa mazan banza suna binsu. In anyi rashin sa'a mai kwadayice, su rudeta har su kai ga aikata alfasha.
2.) KUYI HADIN GWUIWA: A matsayinki na matar aure akwai wasu ayyuka da suka kamata ki je kuyi tare da mijinki. Karki kuskura ki zauna kina kallo yana aikin ba tare da kin je kuyi tare ba.
Kullum ki zama mai taimako a gareshi.
3. )KIYI MASA KYAKKYAWAN ZATO: A duk duniya babu mijin da za ki sameshi dauke da duk halayen da kike so. Dole a samu wasu kina so, wasu kuma ba kya so. Saboda haka ki maida hankalinki kan abinda kike so a tare da mijinki, ki kuma rufe idanuwanki daga abinda ba kya so.
4.) KI SO MIJINKI YADDA YAKE: Wasu mata sai bayan aure sai su wayi gari suka ba irin mijinsu suke so ba. Wasu don a ganinsu yana da kudine, wasu kuma dogo suke so, wasu gajere suke so.
Ko kuma wasu halayensa ba sa so. Wannan matsalace mai saurin kawo mutuwar aure. Ya kamata ki so mutum don shi ba don abin hannunsa, ko kuma sai yadda kike so ba.
5.) KI AMSA KIRANSA: A koda yaushe ya kiraki zuwa shimfidarsa, ki nuna masa farin cikinki. Amma kafin ki kusanceshi ki tabatar kina cikin tsabta mai kamshi.
6. KI SAMU LOKACINSA: Komai aikinki, ki tabbatar kina da lokacinsa da za ku zauna a matsayin mata da miji. A irin wanna lokaci kuna iya yin wasanni tare wanda hakan ke kara so mai tsawon kwana.
7.) KI KASANCE MAI JITUWA: Rashin jituwa da mijinki na nufin igiyar aurenku na tangal-tangal yana shirin tsinkewa. Toh kiyi kokari ki zama mai fahimta da kuma jituwa da mijinki. Ki tsaya ki fahimci dalilansa kafin ki yanke hukunci.
8.) KI NEMI SHAWARA: Idan akwai abinda yake damunki, ki kasance kina neman shawarar mijinki kafin ki yanke hukunci. Ta haka zai sa mijinki yaso ki ganin kin nuna masa shi abin yarda ne.
9.) KADA KI HADA KANKI DA WATA: A matsayinki na matar aure, kada ki hada kanki da matan wani.
Kice "Ina ma nima kamar wance." domin in ba ki sani ba, watakila kin fi wanda kike neman hada kanki da ita kwanciyar hankali. Saboda haka kullum ki fuskanci gabanki kar ki tsaya kalle kalle.
10.)KI FADA MASA GASKIYA: A matsayinki na uwargida ki sanarda maigida halin da gida yake ciki ba tare da kin boye wani abu ba. Kada ki ce ai wannan ba komai bane domin akwana a tashi zai zama komai. Idan kuma haka ta faru, mijinki ba zai ji dadi ba. Zai ce ke kin nuna ba ki damu ba. A karshe in ba'a yi sa'a ba sai ya baki takardarki.
11.) KI KOYI SANA'A: Yawan tambayar mijinki kudi yana nufin kina takura masa. Domin ba kullum ake kwana a gado ba. Idan yau zai iya, mai yiwuwa gobw ba zai iya ba. Toh mafi kyawu gareki shine ki koyi sana'a domin biyan wasu kananan bukatunki. Watarana ma za ki taimakeshi. Shin ba za ki yi farin ciki ba ace mijinki ya nemi taimakonki kin amsa?
12.) KI ZAMA MAI GOYON BAYANSA:
A matsayinki na matar aure, kar ki yarda ki goyi bayan makiyansa. Kar ki yarda kina fadin sirrinsa a wajen wasu. Ki zama mai kare mijinki da kyawawan halayensa.
13.)KI RIKE BAKINKI: Idan kuna fada da mijinka kina iya fadin wasu maganganun da bai kamata ba saboda bacin rai. Toh ki guji yin fada ko kace-nace da mijinki. A duk lokacin da ya taso miki, ki yi shiru har sai ya huce, sannan ki sameshi ki bashi hakuri koda ke kike da gaskiya.
14.)KARKI MANTA KE WACECE:
Komai matsayinki, karki manta cewa ke macece, kuma za ki zauna a karkashin namiji.
15.)KI ZAMA MAI KYAUTATAWA IYAYE DA YAN UWANSA: Idan har kina da jituwa da 'yan uwansa tamkar kina da jituwa da shine. Ki zama mai farantawa, kyautatawa, da kuma taimakawa ga 'yan uwan mijinki. Ki daukesu tamkar naki 'yan uwan. Allah yasa mudace.
Comments
Post a Comment