wasu masoyane biyu suna
mutuqar son junansu fiye da misali sai wata rana budurwar tagayyaci saurayinnata zuwa
gidansu domin yasha ruwa agidan ma’ana yayi buda baki daganan sai yagaishe da iyayenta sannan sauran yan uwanta suganshi domin suna bukatar hakan kawai surayinnan ya amsa gayyata
sukasa lokachi
lokachi yayi sai yaje gidansu.
budurwartashi bayan yaje gidan sai ta fara gabatar dashi agaban mahaifinta sannan takaishi cikin gidansu gurin mahaifiyarta sannan duk yan uwanta sukazo gurinsa …one-by-one… duk suka gaisa iyayenta da yan uwanta duk sukaji sun amince dashi saboda
ganin cancanta da sukayi daga gareshi
kowa yafita waje akabarsu su biyu kacal a falo domin yasha ruwa acikin nutsuwa da kwanciyar hankali akakawo masa kayan marmari da kayan ciye-ciye da shaye-shaye yana zaune yana chi ita kuma tana tayashi hira can sai yazo shan lemo ya daga kofi ya fara shan lemo sai yaji wata kalma mai dadi tafito daga bakinta cewa gaskiya naga iyayena duk sun yarda dakai yanzu maganar aurenmu kawai za’ay jindadin wannan kalmar datafada kawai sai yayi wata muguwar kwarewa daganan.
yayi dogon suma ganin hakan daya faru dashi takalleshi kamar ya mutu
kawai tadauki huqa tadaba acikinta nantake tafadi amace can bayan minti 4 shi kuma saurayin sai ya farko yana duba gefan
damansa sai ya ganta cikin jini yadubeta.
yarasa wanne irin kuka zaiyi kuma ga iyayenta da yan uwanta sunajiran fitowarsa
Comments
Post a Comment