Skip to main content

Yadda Zaku Farfado Da Soyayya A Cikin Rayuwarku Na Aure


Ga bayani kan hanyoyin da ma’arata za su bi don farfado da so da kauna da inganta zamantakewa a tsakaninsu:=
In muka lura da yanayin zamantakewar auratayya a wannan zamanin, za mu ga cewa yawanci zaman hakuri kawai ake yi ba zaman so da kauna da jiyar da juna dadi da taimakon juna ba. Da yawa mukan ji wadansu ma’aurata na cewa ai ba wata soyayya sai dai zaman hakuri ko a ce ana zaune ne domin yara kawai, alhalin in aka duba tarihi akwai lokacin da ma’aurata suke cikin tsananin soyayyar juna har suna jin ba abin da zai iya shafe soyayyarsu har abada. Amma a hankali sai su wayi gari su nemi wannan soyayya a tsakaninsu su rasa.
Ga ma’auratan da ke juyayin ina soyayyarsu ta lokacin samartaka ko lokacin amarci take; su sani cewa wannan soyayyar tana nan, illa dai kurar canje-canje ta rayuwa da ta lullube ta kuma ta dusashe kaifinta. Wannan bayani in Allah Ya so zai karantar da ma’aurata yadda za su kakkabe duk wata kura da ta boye soyayyarsu da yadda za su wasa kaifinta da kara zafafa ta har tafi ta da ma dumi. Ga wadanda soyayyarsu na nan da duminta, bayani zai zo kan yadda za su kara tabbatar da wannan dumi har karshen rayuwarsu cikin yardar Allah Azza Wa Jallah!
Sinadarai uku na aure:
Yana da kyau ma’aurata su san cewa Allah (SWT) Ya gina zamantakewa irin ta auratayya a kan sinadarai uku: natsuwa, soyayya da tausayi (jinkai) kamar yadda Ya sanar mana a cikin Alkur’ani Mai girma:
“Kuma daga cikin ayoyinSa shi ne Ya halitta muku mata daga kawunanku, domin ku samu natsuwa daga gare su, kuma ya sanya soyayya da rahama a tsakaninku; lallai a cikin wannan akwai ayoyi ga ma’abota tunani.”
Ga bayani kan sinadaran nan uku da tasirinsu a  rayuwar aure:
Natsuwa:
Aure yana samar da natsuwa a rayuwar ma’aurata da dama: na farko akwai samar da natsuwa ta sha’awar mutum, duk ma’aurata suna da natsuwar cewa duk lokacin da sha’awarsu ta motsa, to fa suna da wannan na musamman din da zai biya musu bukata cikin kwanciyar hankali kuma duk lokacin da suka so.
Akwai kuma samun natsuwar cewa mutum yana da wani na musamman da Allah Ya kaddara shi ne kamar wani murufi da ya rufe gibin rayuwarsa, wanda da shi zai cika masa addininsa, wanda zai boye masa sirrinsa, zai taimake shi ya rufa masa asiri a duk lokacin da wata masifar rayuwa ta taso, kamar yadda Allah (SWT) Ya fada mana cikin Suratul Bakara, aya ta 187:
“Su (matan aurenku) tufa ne a gare ku, kuma tufa ne a gare su”
Awai kuma samun natsuwar cewa mutum yana da wannan na musamman da yake jin dadin zama da shi, wanda zama da shi yake kayatar da shi fiye da zama da kowa a duniya, kamar yadda Allah (SWT) Ya nuna cikin Suratul A’araf, aya ta 189 cewa Ya halicci mace daga cikin namiji, domin ya ji dadin zama da ita.
“Shi ne wanda Ya halitta ku daga rai guda, kuma daga gare shi Ya halitta matarsa domin ya ji dadin zama da ita” Kur'ani :7: 189
Ga namiji akwai samun natsuwar cewa ko ina ya je ya dawo, yana da wannan ta musamman da za ta kula da shi, ta tarbe shi cikin murya mai taushi, ta rirriga shi ta hutar da shi. Ga mace kuma akwai samun natsuwar cewa tana da wani mai ciyarwa, shayarwa da tufatar da ita da kuma tsare mata mutuncinta da kare ta daga duk wani abu da zai cutar da ita. Da dai sauran natse-natse iri-iri  da sukan iya dangantaka da yanayin ma’aurata da yanayin aurensu.
Soyayya:
Natsuwa ita ke haifar da soyayya ta ainihi kuma tabbatacciya, ba irin soyayyar saurayi da budurwa ba, wacce yawanci soyayya ce da sinadaran jinsi na sha’awa da kuma sinadaran shauki ke haifarwa, amma soyayyar rayuwar aure daban take, domin ita Allah (SWT) ke kafa ta cikin zukatan ma’aurata kamar yadda ya zo a cikin ayar da ke sama.
Tausayi:
Soyayya kuma ita ke haifar da tausayi, har ya kasance mutum na hakuri da nakasun abokin zamansa da kau da kai ga abin da inda wani ne ya yi masa shi, to sai an kai ruwa rana. Mace sai ya kasance tana hakuri da rashin samun mijinta ko miji ya yi hakuri da wuyar halin matarsa da sauransu.
Sai mako na gaba insha Allah, da fatan Allah Ya sa mu kasance cikin kulawarSa a koyaushe, amin.

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

LAKANIN DA HADIN KARIN GIRMAN NONO DA KUMA DANKO DA MATSE GABA GA MATA

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa. Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..   Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:====== A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin kudin ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu. Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa: Kankana Ayaba Gwanda Goba Lemo Tumatir Rake Aya Kwakwa Dafaf...