Ina Æ™ara yi wa masu karatun wannan shafi barka da rana, tare da yin kira ga uwargida da ta ci gaba da bayar da himma wajen ganin an ci gaba da jajircewa kan ayyukan gida da kula da yara. A wannan makon ma za mu É—ora kan maganar da muke yi a kullum na gyara da kula da jiki, tun daga kan kwalliya da surar jikin mace. Ina ganin babbar ribar da uwargida za ta samu shi ne kula da kai da na iyali baki É—aya da yara har da shi ma mai gidan. Amma idan kika saki jikinki, ki ka murÉ—e ko kika cure a waje É—aya babu wani muhimmin aikin da za ki iya yi wa kanki ma, balle ki sauke waÉ—ancan nauyayan haƙƙoÆ™in da ke kanki. Za mu yi magana a kan wasu abubuwa ne guda biyu waÉ—anda a kullum muna amfani da su, amma galibi ba mu cika sanin amfaninsu a jikinmu ba. Misali Æ™wai, da dama ana ganin cewa babu abin da Æ™wai ke Æ™ara wa mutum a jikinsa illa don jin daÉ—i ne kawai, alhali kuwa ba haka abin yake ba. Ƙwai na taka muhimmiyar rawa wajen rage gurÉ“ataccen jini, kitse da rage duk wani nau’i na abin da mace ba ta buÆ™ata a jikinta, sannan ya rage Æ™iba. Haka ma kuma RiÉ—i. Shi ma yana da na sa amfanin a jikin mace. ........,
Bari mu fara da na RiÉ—in. Yawanci ba kowa ba ne ya san alfanunsa ba. Yawanci Hausawa ba su cika damuwa da shi ba, sai wasu Æ™abilu dake maÆ™wabtaka da su. RiÉ—i daga darajarsa ya kamata mu fahimci lallai yana Æ™unshe da amfani mai yawa ko ga zakkarsa idan muka duba. RiÉ—i yana da amfani mai yawa a jikin mace da namiji. Ga Mace yana mata matuÆ™ar amfani ga mahaifarta, don yana wanke dattin mahaifa, da rikirkicewar al’ada.Yana kuma saka mace saurin É—aukar ciki, da samun lafiyar mahaifa da rigakafin kamuwa da ciwon dajin mahaifa da sauran wasu cututtukan da suka shafi mata. Yana saka jikin mace ya daina bushewa da taushin fata. Idan za kiyi amfani da riÉ—i wajen neman lafiya,to aÆ™alla ki yi kwana biyu kina aikinsa, kafin ki kai ga samun garinsa yadda ya kamata. Da farko za ki gyara RiÉ—inki ta hanyar wanke shi sai ki bar shi ya bushe, sannan a niÆ™a shi zuwa gari. Za kiga ya dunÆ™ule saboda yana da mai, sai ki baza shi ya Æ™ara bushewa, sai ki zuba a turmi, harki samu ya warware. Sai ki riÆ™a É—iba kina sha a nono, ko ki ci shi haka nan. Amma ana so ki É—an ba shi tsoro da wuta...,
Na biyu kuma kina iya samun ƙwai kamar guda uku, ki fasa su, ki samu tumaturi, manya guda uku, ki zuba dafaffen zogale a matsayin albasa, ammah ya fi albasar da kike sakawa yawa. Ki sa Maggi, Gishiri yaddah ki ke so, ki juya, sosai sannan ki soya. Suyar ba za ta kafe ba, za ta dagargaje, ta yi miki ruwa-ruwa, ki zauna ki cinye. Idan kina da madarar shanu, ki dora a kai. Idan babu ki sami kamar Yoghurt ko nonon shanu, ki ƙara masa ruwa, ya yi tsululu, ki sa Suga ko zuma kaɗan, ki juya sannan ki shanye....,
Irin waÉ—annan abinciccikan suna da kyau mata su riÆ™a amfani da su a kowane lokaci. Haka ma Ƙwai, kamar yadda kowa ya sani ne cewa dafaffan Æ™wai ya na É—aya daga cikin nau’o’in kayan abincin da ke gina jiki. Kazalika da yawa daga mutane ba su san cewa Æ™unduwar dake tsakiyar Æ™wai ta fi farin da ke kewaye da ita fa’ida a É“angaren gina jiki, Æ™ara lafiya, kuzari tare da sanya Æ™warin jiki ga É—an Adam. Da akwai labaran Æ™anzan kurege da aka jima ana yayatawa, cewa wai duk wanda ke cin Æ™unduwar Æ™wai akwai yiwuwar ya kamu da ciwon zuciya, wannan dalili ne ya kan sa wasu mutune ya cire Æ™unduwar Æ™wan sun yasar a sau da dama, sannan su cinye ragowar farin dake kewaye da ita. Dangane da wannan jita-jitar ne ya sanya ni sha’awar tantancewa tare da fitar da gaskiya dake tattare da lamarin ta hanyoyin binciken da masana lafiya a duniya suka fitar. Kamar yadda binciken ya nuna, cin dafaffen Æ™wai tare da Æ™unduwarsa baki É—aya, ya na matuÆ™ar rage Æ™iba tare da sanya Æ™oshin lafiya. Saboda haka, yasar da Æ™unduwar Æ™wai ba dabara ba ce, idan aka yi la’akari da irin rawar da take takawa wajen gina jiki da kuma Æ™ara ingantacciyar lafiya ga jikin bil-Adama. Haka zalika, kai tsaye za a iya cewa, cin dafaffen Æ™wai a matsayin karin kumallon safe ga É—an Adam, na yin tasiri ta yadda duk wani abu da aka ci wadda ke sanya Æ™iba, to ko kaÉ—an a wannan ranar ba zai yi tasiri ba. Har ila yau a wani binciken da aka gudanar a Æ™asar Amurika, ya nuna cewa, waÉ—anda ke amfani da dafaffen Æ™wai a matsayi karin kumallon safe ba za su taÉ“a zama É—aya da waÉ—anda ba sa yi da shi ba, ta fuskar rage Æ™iba, tare da sanya kuzari da kuma yalwata lafiyar jiki baki É—aya%%%%%%,
A wani É“angare kuma, idan mace na da buÆ™atar rage Æ™iba, to abu mafi sauÆ™i da ya kamata ta yi a taÆ™aice shi ne kamar haka: Abu na farko da za ta nema shi ne zogale, bayan an gyara an wanke shi, sai a markaÉ—a, sannan a tace ruwan, kana a riÆ™a sha safe da kuma dare, ma’ana kullum sau biyu a rana. Sai dai kar a manta binciken ya bayyana cewa, akwai yiwuwar sanya gudawa, saboda an hau turbar rage Æ™iba ne. Muddin aka yi amfani da wannan dabara kamar yadda aka bayyana, to mace za ta rage Æ™iba sosai da sosai. Sannan kuma ga wacce take da tumbi, sannan ta ke son rage shi, to sai ta sami sassaÆ™en Gamji ta haÉ—a da ‘yar jar kanwa, sannan a tafasa a riÆ™a sha, in Allah Ya yarda za a neme shi a Rasa
Comments
Post a Comment