Darasin yau yana daya daga cikin mahimman darussa na wannan shafin mai albarka, domin magana ce a kan matsalolin da suke faruwa a tsakanin ma’aurata, wato sabbin shiga, komai wayewar mace da namiji, ko ta yi ta sayar da kanta a matsayin ‘yar auren holewa in dai ba ta zauna da namiji a matsayin matarsa bisa shari’a ba to bakuwa ce, matar da ta yi rayuwa da namiji koda shekara daya tal ta yi da shi, tana da abubuwan da za ta fadi wadanda tsohuwar ‘yar daduro ba ta sani, haka namijin da bai taba aure ba koda kuwa ya yi ta tamfatsewarsa da mata in dai bai taba aure ba to akwai abubuwa da yawa wadanda sai an yi masa bayani..."
Babban dalilan da suke haifar da matsaloli a tsakanin wasu ma’auratan a shekarar farko suna da alaka ne da rashin sabawa da zamantakewar aure, dukkan su biyu sun yi ta bata wa juna ne lokaci a rayuwar da ba ta hakika ba, namiji ya rika jin cewa shi ne komai na ta, in ‘yar ajiyar zuciya ta yi sai ya fara kokarin sanin dalili, duk abin da take so nan da nan za a yi mata, in kudi ta nuna tana bukata ko dai a ba ta nan take, ko kuma a aiko mata, ita kuma za ta iya yarda cewa tabbas zai iya yin komai, don a fahimtarta kauna takan sa masoyi ya yi abin da bai taba tsammanin zai yi ba, kuma ita masoyiyarsa ce, yana kaunarta sama da kowa........"
Shi ma din samma-kal, domin takan nuna masa iya abin da za ta iya fitarwa na kauna, takan fito masa a matsayin wace take dai-dai da ta sayar da ranta a dalilinsa, shi ya sa ma takan ce masa “In ba kai ba rijiya” wato kauna ta kai mata inda take ganin rayuwa ba ta da amfani matukar ba da shi ne ba, bukatarta kawai ta gan ta tare da shi, suna musayar doke-doke da ‘yan dararraku, ba ta da wata magana sai ta sa, kamar yadda ba ta son ganin fuskar kowa sai ta sa, ko bakanta mata rai ya yi in ya yi murmushi shi kenan an gama, ta sauko kenan.
To yanzu rayuwa ce za a yi ta hakika, ba wata maganar sha’awar kaza, in fuska ake son gani yanzu ga ta ba hoda ba tozali, in kwalliya ce to sun ma ga junansu suna warin zufa ba kamshin turare ba, satar kallo ko wayon taban wani wuri bai ma taso ba tun da duk sun biya wa juna bukata ba daya ba ba biyu ba, yanzu abin da ya rage shi ne fuskantar zahiri a hakikaninsa. Ita mace tana bukatar wannan kulawar da ta jima tana gani, in kuma bai samu ba to hakika wani canji ne na daban wanda ba ta san sa ba ya kurdado.
Haka shi ma namiji yana son ya ci gaba da ganin wannan tarairayar da yauki gami da takwarkwasa kamar yadda ya saba tun tale-tale. Sai dai kash! ba abin da ya dace kenan ba, ya kamata in kida ya canja rawa ma ta canja, misali; mace a gidan uwayenta (wasu) da safe sai an gama komai za a tashe ta ta yi sallah, ta yi shirin makaranta, amma yanzu sai dai ta tashi ta shirya wa maigida abinci, ba ta da zama har sai ya fita, don ita ma tana da bukatar karyawar kamarsa, kenan aikin abinci da sanyin safiya ya kama ta, wanda a lokacin da take ganin tana soyayya ne ba shi a kanta.
Tana gama abincin safiya sai kuma zancen wanke-wanke, ga gyaran daki da tsaftace wuraren biyan bukata kamar kicin da ban daki. Sai kuma sharar gida da shirya gado da daki, bayan ‘yan uwanta da baki da za ta yi, wannan duk za ta yi ne bayan wanka da kwalliya, wadanda a da su kadai ta sani, tana kammalawa sai zancen abincin rana, idan ma har ta iya kammalawar kenan, tana sa rai ta yi aikin wahala ta gaji tibis, saboda hidimar gida yanzu tana jirar maigida ya zo, ya rarrashe ta cikin sanyin murya da magana mai dadi a yi wannan a yi wancan, wanda a fassararta su ne soyayyar in ba ta samu ba kuma canji ne yanzu sai hakuri.
Shi kuwa ya saba a dafa a ba shi, ba abin da ya sani sai kudinsa, yanzu komai shi ne duk wani abu na gida da bai saba sanin yadda ake yi ba yanzu shi ne ma zai dauki nauyin kammala shi, garin neman abin rufin asiri sai ka ga ya dawo gida a jigace yana sa rai da cewa yanzu matarsa za ta tarairaye shi kamar yadda ta saba, to a da lokacin tana gidansu ta rika yi masa a matsayinta na budurwarsa bare yanzu da komai na ta yake wuyarsa? Shi bai san wace wahala ta sha a gida ba, in bai sami yadda yake so ba sai ya yi tunanin an sami canji ne ba tare da kallon cewa ita ma tana bukatar abin da shi ma yake bukata a wurinta ba.
Shi kuwa ya saba a dafa a ba shi, ba abin da ya sani sai kudinsa, yanzu komai shi ne duk wani abu na gida da bai saba sanin yadda ake yi ba yanzu shi ne ma zai dauki nauyin kammala shi, garin neman abin rufin asiri sai ka ga ya dawo gida a jigace yana sa rai da cewa yanzu matarsa za ta tarairaye shi kamar yadda ta saba, to a da lokacin tana gidansu ta rika yi masa a matsayinta na budurwarsa bare yanzu da komai na ta yake wuyarsa? Shi bai san wace wahala ta sha a gida ba, in bai sami yadda yake so ba sai ya yi tunanin an sami canji ne ba tare da kallon cewa ita ma tana bukatar abin da shi ma yake bukata a wurinta ba.
Wani abin yakan faru amma ba bisa ganganci aka yi ba. Ya kamata sababbin ma’aurata su san irin wadannan canji na farkon zaman rayuwar aure, domin gudun kar daga yin aure a fara samun matsaloli. A wasu lokutan, wannan dan caji wanda ma’aurata suke samu farkon zaman aure shi haifar da rashin cin dadin zaman aure, wasu lokutan ma har a rabu, idan kuma ba a rabu ba sai a kasa yin zamantakewan da ta dace ko kuma ma’auratan su kasa bawa juna hakkin da ya dace. Allah ya ba mu ikon sanin yadda za mu fuskanci canji a tsakanin soyayya da kuma zaman aure.
Comments
Post a Comment