Skip to main content

Amfanin Lallai A jikin Ya Mace

Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar da mata su yi lalle akwai sirrika acikin sa.
.
.
Nafarko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama, yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafan sannan yana kula da dumin mace, bi ma ana yana kiyaye. ni imar mace ba tare da ya gushe ba, innace lalle wasu zasu dauka zanen henna nake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi nake magana akai:
Ga kuma sadaqa ga duk mai infection ta tafasa lalle inyadan huce sai ki dinga zama a ciki na sati biyu, in Allah yayarda za ki warke.
Saboda maganin da lalle keyi ma akan iya shan ruwan lalle cokali daya don wankin dattin ciki amma banda masu ciki, to yanzu dai zamu dauki bangare daya daga cikin amfanin lalle muyi magana akai, wato shine amfanin lalle da kuma yanda ake amfani da shi don gyaran Fata.Lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne ba bleaching yake ba amma yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata, in kina son gyara fuska tai kyalli, laushi da haske to ki kwaba lalle da ruwan Kwai amma banda kwaiduwar kwan ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum minti talatin kafin wanka, za ki sha mamaki in sha Allah:
Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun zakiga canji.
sannan gamai son kamshin fata
: Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket ki sa garin lalle ya jika yay já zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulun ki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu.
: Sannan ga gyaran duka jiki kuma zaki hada lalle da sabulun salo da Zuma kina wanka dasu duk zakiga canjin fata in sha Allah
Sannan ga Amare kuma
Kafin kiyi dilke na aurenki
 fata zatayi laushi, haske da kuma santsi.
Ki samu lalle mai kyau ki kwaba da turaren ki mai maiko, turaren gargajiya mai mai dinnan to ki jika kamar botiki ba ruwa ruwa sosai ba Kamar dai kunu, kullum sai ki shafe jikinki da hadin lallen nan duka jikin ki, sãi kizo ki saka turaren wuta a kasko ko burner ki rufu akai ki turara jikinki hayakin turaren nan ya shiga sosai sai ki fita kije kiyi wankan ki zakiga canjiDaga karshe kuma ga masu fama da pimples, sai ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskaar ki, kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Sirrin Samun Saurayi Nagari

Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ta na mace ta taba kokarin samun namijin kirki amma bata samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma yadamu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki. A watan azumi da ake ciki, ki kokarta wajen kyautata dangantakarki da Allah, ki bada kyauta ga mabukata. Haka ki yawaita fara'a da nafilfilin dare, da rokon Allah ya kawo miki miji nagari da kuma dacewa da sa'a a wannan rayuwar. Ki rage yawan fada, da yawan surutu tsakanin ki da sauran 'yan uwa mata ko maza. Kada kuma azumi ya hanaki kwalliya da gyaran jiki, yadda ya kamata ace ko wace mace na yi. Kokarta wajen kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi. To fara duba kanki, ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadd...