Skip to main content

Posts

Showing posts from August, 2019

Cin Kashi Da Aka Yi Wa Yan Arewa A Lagos A Yau

A yau na dada tabbatar da cewa hakika shugaba Buhari ya fi son rayuka da dukiyoyin Yarabawa fiye da rayuka da dukiyoyin hausawa yan' Arewa. ”A rikicin da aka yi yau a kasuwar dake titin Lagos/Abeokuta, an kona rumfunan hausawa yan' Arewa an kashe mutum hudu yan' Arewa, amma kawo yanzu babu wani umarnin da ya fito daga bakin sa na a gaggauta kamo Yarabawan da suka yi musabbabin rikicin.” “Amma da ace rayuka da dukiyoyin Yarabawa ne aka kona kuma aka kashe da tuni kaji umarnin gaggawar cewa a kamo wadanda suka aikata abin.” WAI RAYUKA DA DUKIYOYIN YARABAWA SUNFI NA HAUSAWA YAN' AREWA NE AWAJEN BABA??? Inji - Kabiru Ado Muhd.

Rigimar Datti Assalafiy da Adam a Zango

YA DAURA DAMARAR LALATA TARBIYYAN 'YAN MATA MUSULMAI Daga Datti Assalafiy Jama'a kwanaki Adam A Zango ya fitar muku da sanarwa yace ya fice daga kungiyar Kannywood saboda wai an kama abokinsa daraktan shirya fina finai OSCAR, yanzu yana so zaici gashin kanshi, tun daga ranar da ya bayyana ficewar mun san dalilin da yasa yayi hakan Babban dalilin da yasa Adam A Zango ya fice daga Kannywood ba don an kama OSCAR bane, dalilin shine ya tanadi wasu shirye shirye na iskanci da badala a cikin film da waka da rawa na fitsara da rashin albarka, yana so ya fitar da su kasuwa, amma tsoron kamun hukumar tace finafinai na jihar Kano ya hanashi fitarwa To shine bayan an kama OSCAR sai yayi amfani da wannan damar yace ya fita daga cikin kungiyar Kannywood don ya samu ikon yada fasadi da barna a tsakanin Musulmi, Billahi munyi wannan binciken har daga abokan harkansa na kusa da suka san sirrinsa ciki da bai Muna kan nazari a haka, kwatsam sai dazu mukaci karo da sanarwan da Adam A Zango ya fit...

Zakzaky Ya So Ya Kunyata Nigeria Da Indiya A idon Duniya

Gwamnatin Najeriya ta ce wasu dabi'u da shugaban kungiyar harka Isalamiyya na Najeriya ya nuna a kasar Indiya da ka iya kunyata gwamnatocin Najeriya da India na daga cikin dalilan da suka sanya aka mayar da shi gida. A ranar Juma'a 16 ga watan Agusta ne dai Sheikh Ibrahim El-Zakzaky ya isa Najeriya bayan yunkurin kula da lafiyarsa da mai dakinsa Zeenat ya ci tura a kasar Indiya. Malamin dai a cikin wani sako da ya fitar ta faifan bidiyo gabanin komawarsa Najeriya, ya ce yana ganin ba zai samu kulawar da ta dace ba, kasancewar ba a bar shi ya gana da likitocin da suka cancanta ba. Sannan gabanin hakan ya yi zargin cewa an tsananta tsaro a asibitin da yake zaune, inda ya ce akwai matukar takura ga rayuwarsa. Me zai faru da Zakzaky bayan da ya koma Najeriya? Ibrahim Zakzaky ya so bijirewa a Indiya - Gwamnatin Najeriya Me ya sa 'yan Indiya ke 'maraba' da Zakzaky? Sai dai bayan komawar malamin Najeriya, kamfanin dillancin labaru na Najeriya ya ruwaito cewa babbar sakatar...

Sirrin Da Ya Kamata A Sani Game Da Haramtacciyar kungiyar Shi'ah Magoya Bayan Zakzaky

Daga Datti Assalafiy Yau Datti Assalafiy ya cika alkawarin da ya dauka na fitar muku da wasu sirruka da ya shafi kungiyar Zakzaky Mutane suna mamaki kuma suna tambaya akan hanyoyin da Zakzaky ya bi ya tara dunbin matasa a cikin kungiyarsa, da kuma hanyar da yake samun kudaden da yake amfani da su wajen gudanar da harkokin kungiyarsa alhali baya kasuwanci, kuma baya aikin gwamnati, da kuma abinda yake rinjayar matasa shiga cikin kungiyar Nigeria kasa ce da Allah Ya albarkaceta da yawan musulmi, kuma ana son musuluncin da gaske, Zakzaky yayi amfani da damar soyayyar da ake yiwa Musulunci ya fara kira akan a bishi zai jagoranci kafa gwamnatin shi'ah a Nigeria da yake cewa wai gwamnatin musulunci Sannan Zakzaky yayi amfani da halin kunci na sha'awa da son jima'i wanda yake addabar matasa, gashi ba su da halin yin aure, sai ya halasta musu zina ya fakaice da mut'ah, kwadayin son jima'i ya jefa dubbannin matasa maza da mata cikin kungiyar Zakzaky Jama'a bakwa mamaki a...

YADDA MATSALAR AURE KE FARAWA...

A lokacin farko da miji ya gamu da matar shi, ita ce macen da tafi kowacce mace kyau a duniya. Yakan kirata da sunaye kamar: queen, darling sweetheart, end of discussion, sarauniyyar kyau da dai sauransu... Da zarar anyi aure, rayuwa tana tafiya dai-dai saboda ma'auratan suna son junansu... Ana cikin tafiya sai macen tayi ciki, kamanninta su canja daga sarauniyyar kyau zuwa wani abun daban. Fuskanta da qafafuwanta su kumburu, duk shape dinta sun bace bayan ta haihu, tafara shayar da yaronka nono, tumbinta ya yankwane, nononta su kwanta tazama kamar wata yar shekaru 50 zuwa 60.... Yanzu maimakon ka tallafa mata wajen dawo mata kyawunta da (shape dinta) da nonon data shayar da danka suka kwanta, da tumbinta daya yankwane, sai kawai cikin sauki kayi watsi da ita.... Ka tsani kamanninta, wani lokacin kana basarwa idan ka ganta. A hankali har tsanarta da kakeyi ya fito fili kana cewa da ita: "Bana bukatar ganin ki" 😢😢 Anan matsalar ke somawa....

Yadda Zaku Applying Din Garabasa Da Saudiyya Da Turai Ta Kawo Arewa

Da Farko Ku Kafta A Akwatin Nema Kamar Haka: Sannan Sai Ku Latsa SIGN UP   Bayan Haka Sai Ku Cike Kamar Haka:  Da gana zaku ga wani a kwati kamar haka  Bayan Haka Sai Ku Shiga Cikin Gmail Dinku Ku Latsa Kan Sakon: Sannan Sai Kuyi Activating Kamar Haka:  Kuna Latsa Kan Sakon Zaku Ga Kamar Haka, Sai Ku Danna LOGIN HERE Sannan Sai Ku Shigar Da Bayannnan Ku Kamar Haka:   Bayan Haka Sai Ku Selecting Enterpreneur Da Proceed   Shikenan Kun Gama Applying Latsa Kan Kararrawan Sanarwa Domin Sanar Daku Sababin Da Zasu Fita Nan Gaba Rubuta Duk Wani Abinda Baka Gane Ba A kasa

Wani dan Izala mai suna Ahmad Abdullahi Assaminaky, ya koma Shi’a a Najeriya.

Wani dan Izala mai suna Ahmad Abdullahi Assaminaky, ya koma Shi’a a Najeriya. Ahmad, wanda dan kungiyar Izala ne a baya ya wallafa wannan bayani ne yau a shafin sa na Facebook, inda yace;=== “DAGA YAU NA KOMA DAN SHI'A MABIYIN ZAZZAKY Wallahi na dade ina nazarin shin anya malaman mu na Izala a kan gaskiya suke kuwa? saboda a duk malaman kasar nan kai haddama duniya gaba daya a iskar nan ta yau dake juyawa babu wani malami da yake damabiya kuma mabiyan na shi har su rika mutuwa saboda kare rayuwar shi sai Zakzaki.” “Kai ko annabi ne daga cikin Annabawa aka kashe mutum sama da dubu saboda kare rayuwar shi kafin akai kan shi abin a jin-jina ne balle malami, wannan abubuwa sun sani tinanin anya wannan mutun ba mujaddadi ba ne kuwa ? domin ko asiri yakewa mabiyan nan na shi asirin yakai asiri, ni dai duk dadewar da nayi ina Ahlussunna ban tabajin za'azo kashe wani malamin Izala inji cewa zan iya bada rayuwa ta dan in kare shi ba, dubi girman malam Ja’afar wallahi masallacin nan duk ...

GANIN JINI FA BA SHINE BUDURCI BA..

Korafin samari yayi yawa cewa 'yan matan da suke aura ba sune suka fara kwanciya dasu ba. Hujjar su anan ita ce, sunyi saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu ga jini ya fito ba.. Gaskiya wannan ba hujja bace da za'a yi wa mace kallon 'yar Iska. BUDURCI:- Wata fata ce dake cikin farjin mace matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan tana yagewa ne da zarar ta samu takura. Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan hanyoyin.. 1. Saduwa da namiji 2. Daukar kaya mai nauyi 3. Guje-guje 4. Hawan keke 5. Hawan doki ko jaki 6. Mummunar faduwa 7. Sanya danyatsa a farji 8. Haihuwa.. Wasu matan ko an sadu dasu fatar budurcinsu bata yagewa har sai sun zo wajen haihuwa ananne zata yage. Dan haka nake kira ga samari don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar yace lallai sai ya ga wannan jinin***** Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa matarka kallon'yar iska ko mazinaciya domin inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun kafin kuyi Auren, azatona tunda sanda kay...

Yadda Za'a gujewa kamuwa da ciwon ido a lokacin damina

Lokacin damina lokaci ne da ake yawan kamuwa da cututtuka kamar su zazzaɓin typhoid, amai da zawo, Hepatitis, shawara, mura, ciwon hakarkari da sauransu:==== Mutane da dama kan yi fama da ciwon Ido, kunne da maƙogoro matuƙa. Cututtukan idon da ake yawan kamuwa da su a wannan lokaci sun hada da yawan zyin hawaye a ido, matsanancin ƙaiƙayi a ido,Ido zai yi jajawur, apolo da sauran su. Malaman asibitin sun bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wajen kaucewa da magance matsalar ido. Ga hanyoyin 1. A guji saka hannun da bashi da tsafta a cikin idanu. Hannayen da basu da tsafta na dauke da kwayoyin cuta da ake kira ‘Virus da Bacteria’. Tsaftace hannu da amfani da tsuman goge fuska mai tsafta na da mahimmanci wajen gujewa kamuwa da wadannan cututtuka. 2. Yin amfani da maganin ido na digawa Idan ido na yawan yin hawaye ko yana yawan yin ja ko kuma kaikayi kamata ya yi a garzaya asibiti domin samun maganin ido da za a riƙa digawa domin a warke. 3. Yin amfani da gilashin ido Gilashin ido na han...

Yadda Zaki Gyara Fuska Ba Tare Da Kinyi Bleaching Ba

Gyaran fuska tayi fari da sheki naturally batare da kinsa chemical a fuskarki ba. Sannan zanyi bayani akan matan da suke tsintar kansu da wani irin wari ko kuma wani baki-baki a cikin armpit dinsu(hammatarsu) ko bakin fuska daga gefe daya due to bleaching products or sunborn. Dafarko idan kika ga fuskarki na irin wannan duhun daga gefe ko kusa da idonki to cikin biyune kina shafa cream kina shiga rana ko kina shafawa lokacin gari da zafi. Na biyu ko kina shafa man dayafi karfin fatarki to dai koma menene ya janyo ga hanyar da xakibi ki goge wannan tabo zaki sami madara ta ruwa kisata a fridge tayi sanyi sosai sai ki goga a wannan tabon naki bayan minti ashirin saiki wanke sannan idan gari da zafi zaki sami ruwan sanyi kisa cottonballs ki tsoma ki dora akan tabon saiki bari yayi minti 5 saiki cire cotton din ki shafa mai a fuskar.I dan kika yi sau uku saiki dinga yiwa fuskar gaba daya.Am assuring you zaki mamaki sosai. WARIN HAMATA-waddata sami kanta da irin wannan warin ko bakin sait...

Maganin 15 da Baure Keyi

Tsawon shekaru aru-aru, 'baure wani nau'i ne na dangin kayan marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani sabon bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka da dama kama daga ciwon suga zuwa cututtukan fata.  'Baure ya kunshi sunadarai da dama masu gina jiki da suka hadar da fiber, antioxidants, vitamin A, vitamin C, vitamin K, B vitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron.  Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2016 ya tabbatar da cewa, sunadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon suga. Ga wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam:====== 1. Magance kwarnafi da tashin zuciya. 2. Hawan jini. 3. Bunkasa lafiyar zuciya da jini. 4. Ciwon daji wato cutar Kansa. 5. Rage nauyin jiki. 6. Inganta lafiyar mazakuta da kuma ni'imar ma'aurata. 7. Magance ciwo...

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin Mutum

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayyaki irin...

Abinda yasa Mata Basa Ganin jini a Ranar Darensu Na Farko

 Ba za ka iya kirga adadin aurarrakin da suka mutu ba sakamakon rashin fitar jini daga gaban amaryar da angonta ya aureta a matsayin budurwar da shi zai bareta a leda A yadda muka dauka shi ne, sai ango ya ga amaryar kaca-kaca cikin jini a darensu na farko, shi ne zai tabbatar masa da cewa amaryar tasa bata taba sanin da namiji ba Ita kanta amaryar cike ta ke da fargaba na ko angon nata zai tono jini ko kuma a’a ko da kuwa ta san ba ta taba aikata lalata da wani da namiji ba kafin aure Ba sabon labari bane ba a wasu zamaninnika da suka gabata cewar har jefa amaryar a ke yi da zarar mijinta ya yi saduwar farko da ita kuma jini bai fita ta gabanta ba Har farin kyalle ake shimfidawa akan abin kwanciyar amarya da ango a darensu na farko don a tabbatar da zubar jini daga gaban amaryar, kuma cikin alfahari za a yi ta yawo da kyallen ana nunawa manya fa cewa “Wance bata zub da mutunci ba kafin ta yi aure” Wannan dabi’a ta fitar jini daga farjin mace a jima’inta na farko ba mu kadai ke da ...

Maganin Warin Baki

dan kina goge haqorinki sau biyu a rana zai yi haske kamar hakaA wannan makon na kawo miki bayanin yadda za ki lura da hakorinki, wato- cire dattin hakori da kuma kara wa hakorinki fari da kuma lafiya.    Ana so ki rika wanke bakinki da man goge baki ko aswaki akalla sau biyu duk rana, hakan zai sanya hakorinki ya yi haske. Idan kina da dattin hakori sai ki nemi man goge baki kamar daya daga cikin wadannan: Colgate da Rembrandt da 3D Crest da Listerine da Akuafresh da sauransu, sannan kina goge hakorinki da shi. Za ki iya amfani da bakar soda (Baking Soda) wajen goge hakorinki sau biyu a mako. Kadan ake so ki rika diba idan za ki yi amfani da sodar. Sannan bayan haka ana bukatar ki kuskure bakinki sosai bayan kin kammala amfani da sodar. Kada don kina amfani da wadannan sinadaran sai kuma ki daina goge bakinki kamar yadda ya kamata. Ki rika amfani da kororon da ake shan jus ko lemon kwalba wajen shan jus ko lemon kwalba, hakan zai kara wa hakorinki fari da haske. Ya kamat...

Maganin Faso Da Kaushi

kada ki kuskura kibar kafarki da kaushi.ko faso.zanin gadonki ya dinga kama kafarki.wasu zasu ce akwai faso na.ciwo wasu kuma suce fatarsu ce mai gautsi.to ai ana neman maganin kaushi da fatso.akwaina Hausa.akwai na asibiti.saiki zabi wanda zakiyi amfani dashi.don illar kaushi da faso bata saya anan kadai ba.don yana ragewa mace ni'ima sosai.to ko don wannan a nemi magani.ki kulada abubuwan da zasu kara miki ni'ima da nishadi. Ga kadan daga abubuwan daake gyara kafa tayi laushi.tayi kyau sosai.wasu matan rashin tsabta ce.yayinda wasu matan hallitace.haka koma dai menene ga mafita. A sami kofi yana na ruwan khal a hada da lemon tsami.sai a shafe kafar.kullum.sau biyu.a rana .bayan an wanke kafar da minti sha biyar .sai a shafe ta da zaitunza aga abin mamaki. Ruwa sanyi da gishiri a tsoma kafar a ciki zuwa minti sha biyar.sai a wanke .a shafa zaitun, amma sai kafafun sun bushe. Hanyoyin Gyaran Faso Da Kaushin Kafa Fason kafa ya kan zamewa mutane karfen kafa musamman ma a lokacin ...

Abubuwa Goma 10 da bai kamata miji ya fada wa matarsa ba

Masu iya magana dai na cewa ‘ Magana zarar bunu ce’, a don haka duk kalaman da mutum zai furta kan iya zama sanadiyar gyara ko wargaza zamantakewarsa da iyalinsa.  Ga jerin wasu abubuwa goma da ya kamata duk wani miji ya guji furtasu ga matarsa, saboda mata dan karamin abu kan iya sanya su cikin damuwa: ==== 1. Ya rage naki Mafi yawan mata basu son jin wannan Kalmar. A wasu lokutan zai kasance kana hasashen yin wani abu sai matarka ta baka shawara ko dai kaza zamu yi ne, fadin ya rage naki na matukar bata wa mata rai. 2. Ban iya tuna lokacin da na fadi hakan Haba yallabai, ya zaka fadi magana kuma kace ka mance lokacin da ka fade ta. Yana da kyau mu tuna mata na da kokarin rike abu a kwakwalwarsu, fadin wannan kalamin kan iya haddasa fitina tsakanin mata da miji.  3. Ban sani ba Wasu lokutan ma tambaya kadan mata za tayi wa mijinta, kawai amsar da zai furta mata ita ce ‘ban sani ba’.  A rika tauna magana kan a fade ta domin gyaran zaman takewa. 4. Ba komai Wasu mazan na d...

Sirrin Zaman Lafiya DA Yaran Miji

Yau maudu’in zai yi magana ne akan yadda zamantakewa yake tsakanin matar uba, da yaran mijinta. Mafi aksarin mata na samun matsala a wannan gab’ar, ta rashin sanin hanyoyin da zasu bi don ganin sun samu zama ta fahimtar juna tsakanin su da yaran miji da suka tarar, walau suna tare da iyayensu ko an fita an barsu da su. Bangaren Mata… Ina son jan hankalinmu mu mata, a duk inda aka kira mace to ana nufin uwa ce ko da kuwa kin haifa ko baki haifa ba, wannan dabi’a ta kasancewa uwa tana tare dake sai dai rashin sanin yadda zaki fitar ko tafiyar da kanki da zai sa ki amsa wannan suna ta uwa. A duk lokacin da kika shiga gida kika tarad da yara musamman wadanda suka fara girma da mallakar hankakin kansu ,to abu na farko shi ne karki bada wata kofa da zai sa su kalleki a matar uba kawai, ki bayar da kofofin da zasu kiraki da sunan uwa ta kowacce fuska. Ta ya ya hakan zai kasance? Hakan zai faru ne kawai ta hanyar kyautatawa a garesu. Da kyautata zamantakewa tsakaninki da mahaifiyarsu idan kuna...

YADDA ZAKI KULA DA FARCEN KI

Yau maudu’in zai yi magana ne akan yadda zamantakewa yake tsakanin matar uba, da yaran mijinta. Mafi aksarin mata na samun matsala a wannan gab’ar, ta rashin sanin hanyoyin da zasu bi don ganin sun samu zama ta fahimtar juna tsakanin su da yaran miji da suka tarar, walau suna tare da iyayensu ko an fita an barsu da su. Bangaren Mata… Ina son jan hankalinmu mu mata, a duk inda aka kira mace to ana nufin uwa ce ko da kuwa kin haifa ko baki haifa ba, wannan dabi’a ta kasancewa uwa tana tare dake sai dai rashin sanin yadda zaki fitar ko tafiyar da kanki da zai sa ki amsa wannan suna ta uwa. A duk lokacin da kika shiga gida kika tarad da yara musamman wadanda suka fara girma da mallakar hankakin kansu ,to abu na farko shi ne karki bada wata kofa da zai sa su kalleki a matar uba kawai, ki bayar da kofofin da zasu kiraki da sunan uwa ta kowacce fuska. Ta ya ya hakan zai kasance? Hakan zai faru ne kawai ta hanyar kyautatawa a garesu. Da kyautata zamantakewa tsakaninki da mahaifiyarsu idan kuna...

LAKANIN KARFIN AZZAKARI

Me Nene Rashin Karfin Azzakari Wannan na nufin kwantawarsa kafin agama saduwa Abinda suke jawoshi sune A) Halayyar mutun yadau kaso 95 bisa 100 sune kamar haka 1.Tsoron daukar cuta ko daukan cik 2. Rashin yadda da matar 3. Tsanar matar 4.Rashin son yanayin jikinta 5.wanda ke bin maza 6. Rashin ilimin saduwa da mace 7. Accident wanda ke taba kashin baya ko kwankwaso 8. Tiyatar bangaren mafitsara,ko wajen kashi B)Sauran abubuwa 1, Cutar jijiyoyi kamar su ciwon suga 2. Cutar kwakwalwa,zuciya,koda ko hanta 3. shan maganunnuwa MAGANI: 1.Canza salon rayuwa kamar su dena shaye shaye 2. Bawa mara lafiya shawarar dena sa azzakarinsa cikin farjin matarsa na tsayin sati 2,saidai wasa sosai banda sex 3. Yin shawara shakaninka da iyalinka akan wane abune yafi taimakamuku wajen shawar taku ta karu. 4. exercise ta hanyar matar tana shafa azzakarin mijin har sai yayi tauri sai ta daina tabarshi yayi laushi,sai ta kara ci gaba da shafawa har sai ya kara tauri. wannan na karawa ma aurata sanin cewa koda...

KU YI AUREN DOMIN NEMAN KUSANCI GA ALLAH

Muyi aure domin neman karin kusanci ga ALLAH, muyi aure domin ALLAH domin tabbatar da sunnahn manzon ALLAH (S.A.W). Kada kayi aure domin jima'i kawai, sani dai aure ba jima'i ne kawai ba, a'a zamantakewa ce da ake so ta kasance har abada, kuma ibada ce cikon rabin addinin ka, sunnah ce ta manzon ALLAH (S.A.W) nutsuwa ce kuma ni'ima ce, jima'i na ɗan wasu lokuta ne kawai shin idan sha'awar ka ta sauka shikenan, Baruwan ka da matar, Kada kayi aure domin baka son ka rasa wannan masoyiyar ta ka, saboda kyawun ta, mulkin gidan su, ko wata surar ta ko dukiyar ta ko na iyayen ta, wannan ba shine zai tabbatar da zaman ku cikin kwanciyar hankali ba, dukiya, kyawu, mulki, surar mutum, na iya gushewa a kowanne lokaci, kai de yi auren ka domin ALLAH, zaka iya auren ta saboda abunda muka lissafa a sama amma ya zamo akwai rikon ta da addini da tarbiyya, kuma ya zama auren domin ALLAH. Kada kayi aure kawai dan an takura ka a gida, a'a kayi aure domin neman yardar ALLAH ka ...