Skip to main content

GANIN JINI FA BA SHINE BUDURCI BA..



Korafin samari yayi yawa cewa 'yan matan da suke aura ba sune suka fara

kwanciya dasu ba.
Hujjar su anan ita ce, sunyi
saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu
ga jini ya fito ba..
Gaskiya wannan ba hujja bace da za'a yi wa
mace kallon 'yar Iska.
BUDURCI:- Wata fata ce dake cikin farjin mace
matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan
tana yagewa ne da zarar ta samu takura.
Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan
hanyoyin..
1. Saduwa da namiji
2. Daukar kaya mai nauyi
3. Guje-guje
4. Hawan keke
5. Hawan doki ko jaki
6. Mummunar faduwa
7. Sanya danyatsa a farji
8. Haihuwa..

Wasu matan ko an sadu dasu
fatar budurcinsu bata yagewa
har sai sun zo wajen haihuwa ananne zata yage.
Dan haka nake kira ga samari
don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar
yace lallai sai ya ga wannan jinin*****
Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa
matarka kallon'yar iska ko mazinaciya domin
inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun
kafin kuyi Auren, azatona tunda sanda kayi
bincike kamin kayi Auren,domin ba'a zama da
zargi don da zarar Zargi Yafara shiga Aure
To aure zai lalace.
Allah ya kiyaye mu da kiyayewarsa Kuma Allah
yasa 'yan uwana maza su Fahimta, Allah ya bamu Yaya na gari tare da Zuriya daiyiba.
Aameen....

Comments

Popular posts from this blog

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

Yadda Zaka Gamsar Da Matan Ka

Dukkanmu mun taso mun samu ana cewa mata sun kasu gida uku game da lamarin kwanciya: akwai harija, mutawassida da dakhila. Ta tsakiyar ce ta fi yawa a rahotannin baka. Marubucin nan bai da tabbas game da wannan bayani a ilmance. Amma dai maganar ba ta yi nesa da abin da gogayyar yau da kullum take tabbatarwa ba. Gazawa ce a bangaren namiji, ko ma a wane rukuni matarsa ta fada a cikin biyun qarshen nan, a ce ba ya iya gamsar da ita a wurin kwanciya. Kazalika qalubale ne a gare shi, idan matar ta kasance cikin rukunin farko, dolensa ya zaqulo yadda zai gamsar da ita. To me da me ke sa mutum ya iya gamsarwar? Farko, akwai buqatar bahaushe ya gane cewa ba fa zallan dukhuli ne ke gamsar da mace ba, sai ya riqa hadawa da nau’in “romance” din da matar ke buqata. Mata da yawa na qorafin wannan jahilci nasa. Binciken masana harkar ya bayyana cewa, ko minti biyar kawai miji zai yi a duhuli, amma ya yi “romance” da matarsa na kimanin awa guda, za ta gamsu. Wane irin “romance” ne mata ke buqata? K...