Lokacin damina lokaci ne da ake yawan kamuwa da cututtuka kamar su zazzaɓin typhoid, amai da
zawo, Hepatitis, shawara, mura, ciwon hakarkari da sauransu:====
Mutane da dama kan yi fama da ciwon Ido, kunne da maƙogoro matuƙa.
Cututtukan idon da ake yawan kamuwa da su a wannan lokaci sun hada da yawan zyin hawaye a ido, matsanancin ƙaiƙayi a ido,Ido zai yi jajawur, apolo da sauran su.
Malaman asibitin sun bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wajen kaucewa da magance matsalar ido.
Ga hanyoyin
1. A guji saka hannun da bashi da tsafta a cikin idanu.
Hannayen da basu da tsafta na dauke da kwayoyin cuta da ake kira ‘Virus da Bacteria’.
Tsaftace hannu da amfani da tsuman goge fuska mai tsafta na da mahimmanci wajen gujewa kamuwa da wadannan cututtuka.
2. Yin amfani da maganin ido na digawa
Idan ido na yawan yin hawaye ko yana yawan yin ja ko kuma kaikayi kamata ya yi a garzaya asibiti domin samun maganin ido da za a riƙa digawa domin a warke.
3. Yin amfani da gilashin ido
Gilashin ido na hana kwayoyin cututtuka, haki ko kura shiga idon mutum musamman a lokacin damina.
Tsaftace gilashin ido a kowani lokaci na hana kamuwa da ciwon ido sannan yana hana kwayoyin cututtuka zama a kan gilashin.
4. A yawaita Wanke fuska da ruwa mai tsafta
Musamman idan mutum ya fito daga ruwan sama kamata ya yi ya wanke idon sa da ruwa domin wanke kwayoyin cututtukan dake cikin ruwan saman da ke iya shiga ido.
5. A guji saka ‘Contact lens’ lokacin damina
Saka ‘contact lens’ a lokacin damina na kawo jan ido da kaikayi inda hakan ya sa ake kira da ayi hakuri da shi.
6. A guji yin amfani da tsuman goge fuska da wani dabam ke amfani da shi
Wani hanyar kamuwa da cututtukan dake kama ido shine idan mutum na yawan amfani da tsuman share fuka ko kuma ido na mutane.
7. Yawan shiga ruwa na sa a kamu da cuta a ido
Shiga ruwa don wanka a rafi ko irin na gida shima kan sa a kamu da ciwon Ido.
8. Yin amfani da man (Castor Oil) da Zuma
Za a iya amfani da man ‘Castor Oil’ da zuma da za a haɗa shi kamar tozali a riƙa sakawa idan ido na yawan kaikayi ko kuma idan haki ko kura ya faɗa idon mutum.
Yin amfani da man (Castor Oil)da zuma na taimakawa saboda suna dauke da sinadarin dake inganta karfin ido.
Comments
Post a Comment