Daga Datti Assalafiy
Yau Datti Assalafiy ya cika alkawarin da ya dauka na fitar muku da wasu sirruka da ya shafi kungiyar Zakzaky
Mutane suna mamaki kuma suna tambaya akan hanyoyin da Zakzaky ya bi ya tara dunbin matasa a cikin kungiyarsa, da kuma hanyar da yake samun kudaden da yake amfani da su wajen gudanar da harkokin kungiyarsa alhali baya kasuwanci, kuma baya aikin gwamnati, da kuma abinda yake rinjayar matasa shiga cikin kungiyar
Nigeria kasa ce da Allah Ya albarkaceta da yawan musulmi, kuma ana son musuluncin da gaske, Zakzaky yayi amfani da damar soyayyar da ake yiwa Musulunci ya fara kira akan a bishi zai jagoranci kafa gwamnatin shi'ah a Nigeria da yake cewa wai gwamnatin musulunci
Sannan Zakzaky yayi amfani da halin kunci na sha'awa da son jima'i wanda yake addabar matasa, gashi ba su da halin yin aure, sai ya halasta musu zina ya fakaice da mut'ah, kwadayin son jima'i ya jefa dubbannin matasa maza da mata cikin kungiyar Zakzaky
Jama'a bakwa mamaki abinda yake faruwa a Abuja? 'yan mata ne musulmai manyan 'ya'yan attajirai suna killace a gida, sunyi karatu sun gama jami'ah suna son aure amma babu mazajen da zasu aure su, da yawansu sun fada kungiyar shi'ah domin su dinga rage sha'awar da take addabar su, 'yan mata da yawa suna cikin kungiyar ba tare da sanin iyayensu ba ana lalata da su
Amma duk da wannan jama'a da ya tara, Zakzaky ya san cewa ba zai samu nasaran kafa gwamnatin shi'ah ba face sai ya samu goyon baya daga gurin manyan 'yan siyasa da manyan jami'an tsaro wanda zasu taimaka masa wajen hambarar da gwamnati da karfin tsiya, kamar yadda magabacinsa yayi a Kasar Iran, shiyasa sai ya jira har zuwa ranar da 'yan kungiyarsa suka haye madafun iko kafin sai ya wanzar da kudurin nasa
Zakzaky yana da hanyoyin samun kudi guda biyu, na farko tallafin kudi da Kasar Iran take bashi, na biyu kudin zinar mut'ah da mutanensa talakawa, manyan 'yan boko da attajirai suke biya, bincikenmu ya tabbatar mana da cewa duk wanda zai biya kudin mut'ah ba za'a bawa budurwa ko matar da za'ayi mut'ah da ita kudin ba, kudin na Malam ne, ko da za'a bata amma dai Malam shi ke da kaso mai yawa, shi ake tarawa kudin, akwai masu yin zinar mut'ah na kwana biyu, sati daya, wata daya da sauransu, ko kwana nawane mai son auren mut'ah ya zaba da farashinsa, har ana iya samun juna biyu
Shekarun baya, na taba fada muku wani labari da ya faru, wata 'yar shi'ah ce ta rinjaye kawarta ta shigar da ita harkan mut'ah aka dirka mata cikin shege, rana tsaka uban yarinyar suka ga 'yarsu da cikin shege, a lokacin an dauki lokaci mai tsawo ana buga Shari'a a gaban alkali, nayi kira ga jama'a nace kowa ya saka ido akan 'ya'yansa mata, a yanke dukkan wata alaka dake tsakaninsu da 'yan shi'ah
Bayan wannan, lokacin da Zakzaky ya kwace ikon unguwar Gyallesu daga hannun gwamnatin Nigeria, ya sa ana yin garkuwa da 'ya'yan mutane ana kaisu can ana horar da su ayyukan ta'addanci da aikin soji da na 'yan sanda, yana da jami'an tsaronsa, ya nada kansa shugaban kasa, yana da gwamoninsa da chiyamomi da kansiloli, yana da jami'an tsaronsa na sirri da na fili da 'yan leken asiri, yana da likitoci da 'yan jaridu, har da sarakunansa na gargajiya, wasu ana horar da su anan gyalle su wasu ana kaisu Kasar Iran su samu horo na musamman.
Tattaki: jama'a kun san manufar da ta sa Zakzaky ya wajabta wa mutanenshi yin tattaki a duk inda suke a Nigeria su tafi Zaria da kafafunsu? wannan wani salo ne na horon aikin soji yake musu a fakaice, haka zasu fito mazansu da matansu suna tafiya a kafa suna yada zango a makarantun firamare da sakandare na gwamnati, ance mana duk kauyen da suka yada zango idan akwai kororon roba (Condom) sai ya kare a garin, tunda sun saba da tafiya a kasa, to akwai ranar da zai umarcesu su nufi Abuja da kafa suje su hambarar da gwamnatin Nigeria ya dare kujerar shugaban kasa.
Idan kuna son ku fahimci wannan bayanin, ku karanta abinda 'dan jaridar IMN Bilya Hamza Dass ya wallafa kamar haka:
"..wannan waki'a ta yaye mana wani labulen da ya boye mana Abuja a da. Yanzu mun fahimci tituna da lungunan Abuja tun kafin shiga Abuja na sosai ya zo. Yanzu Abuja ga 'yan'uwa kamar jariri ne da hantsar uwarsa. Kamar Maigida ne da gidansa.
Mun san Abuja kamar yadda muka san yawan kudaden da muka ajiye a aljifanmu. Mun fahimci lungu da sako-sakon garin. Babu inda kaza za ta bacewa muzuru in lokacin kalaci ya yi..." wato yana magana ne a fakaice cewa yanzu sun san sirrin Abuja, sun san hanyar fadar shugaban Kasa, rana tana tafe, ranar da Zakzaky zai umarcesu su tafi Abuja su kifar da gwamnatin Nigeria
Lokacin da suke zanga -zanga a Abuja da Kaduna, ku duba ku ga yadda suke kalubalantar jami'an tsaron gwamnati, 'dan shi'ah zai cire rigarshi ya zo gaban soja ko police wanda yake rike da bindiga yace harba, yawancin matasan shi'ah da suke yin haka ba a hayyacinsu suke ba, wato akwai wani ruwa da akayi packaging dinsa a cikin leda kamar ledar pure watar, ana fada musu cewa wai ruwan addu'ah ce da mujahidai suke sha, alhali karya ne, binciken mu ya gano mana cewa wannan ruwan addu'ah da ake bawa sojojin shi'ah magoya bayan Zakzaky hadadden miyagun kwayoyi ne masu gusar da hankali irin wanda 'yan ta'adda suke sha kafin su kaddamar da harin kunar bakin wake
Zaku ga a duk lokacin da matasan shi'ah suka fito zanga-zanga bayan an basu wannan ruwan sunsha suna jin wani irin karfi a jikinsu kamar kasa ba zata dauke su ba, ji suke a mutu ko ayi rai, lamari ne na miyagun kwayoyi da aka basu suka sha ya gusar musu da hankali
Duk abinda Zakzaky yake yi karshenta dai so yake yayi amfani da wadannan matasa ya kifar da gwamnatin Nigeria, amma kamar yadda na fada muku 'yan shi'ah basa kaunar a tona musu asiri akan miyagun akidunsu da kuma boyayyun ajandarsu, kamar yadda kungiyoyin asiri masu shan jini (secret cult) da manyan kungiyoyin bayar da agaji wanda ba na gwamnati ba (International NGOs) masu taimakon kungiyoyin ta'addanci a boye, suka ki jinin a fitar da sirrin ayyukansu, to haka 'yan shi'ah magoya bayan Zakzaky suke.
Duk wani mai kaunar zaman lafiyar Nigeria da ya san sirrin manufar kungiyar Zakzaky ba zai kaunaci mutuminnan ba balle ya tausaya masa, mutane suna fadin cewa me yasa gwamnatin Nigeria take takura masa? amsar shine yana cin amanarta, yana so ya kafa kasa a cikin kasa, Shehu Dahiru Usman Bauchi yafi Zakzaky yawan mabiya, me yasa gwamnati bata takura masa ba? amsar shine baici amanar gwamnatin Nigeria ba yana son zaman lafiya, Sheikh Dr Abdullahi Bala Lau yafi Zakzaky mabiya, amma me yasa gwamnati bata takura masa ba? amsa shine baici amanar gwamnatin Nigeria ba.
Yau inda ace Zakzaky zai nada kansa a matsayin Allah abin bauta, ya umarci mutanensa akan cewa su bauta masa, matukar bai taka dokar kasa ba ya zauna lafiya, babu ruwan gwamnatin Nigeria da abinda yakeyi, gwamnatin Nigeria zata bashi cikakken tsaro da kariya a matsayinsa na 'dan kansa
Allah Ka tsare mana Kasarmu Nigeria daga sharrin kungiyar Zakzaky
Comments
Post a Comment