Wani babban likita masanin abincin da ke gina jikin dan adam, Dakta Andrew Marbell, ya ce; wannan dan icen da aka fi sani da Agwaluma ya na taimakawa wajen rage suga a cikin jini, sannan ya na rage kitse a jikin mutum, sannan ya na matukar taimakawa wajen kiyaye kamowa da cutar ciwon zuciya.,,,, Likitan ya bayyana hakan ne ga manema labarai yau Alhamis a garin Abuja, a cewarshi Agwaluman ta na dauke da sinadarin “Vitamin C” kuma adadin sinadarin yafi na wanda yake cikin lemun zaki. Sinadarin ya na matukar taimakawa wajen kare jikin mutum daga cutukka irinsu kaikayin makoshi, coshewar ciki da ciwon hakuri, a wasu sassan Nijeriya ma ana amfani da ‘ya’yan agwalumar a matsayin maganin cutukkan fata, wasu sunce cin ‘ya’yan na taimakawa mutum wajen hana shi kamuwa da cutar kansa da ciwon suga. Dakta Marbell yana cewa; agwaluma na matukar taimakawa wajen rage kiba da nauyin jiki, ana amfani da sassan bishiyar agwaluman sosai, kamar misali jijjiyar bishiyar, bawon bishiyar ganyen wajen magance...
Mace Kayan Dadi