Skip to main content

Takaitaccen Tarihin ALi Nuhu


An haifi Ali Nuhu Muhammad a 15 ga watan march shekara ta 1974, shi jarumi ne na bangarori daban-daban hada daga Nollywood, Kannywood, da kuma ketare a takaice dai Ali Nuhu jarumi ne na Africa gaba daya. Bayan kasancewar sa jarumi sannan mashiryin film ne, marubuci, kuma mai daukar nauyi. Ana masa lakabi da Sarkin Kannywood saboda jajircewar sa da kuma kamun kai.
An haifi Ali a garin Borno, Maiduguri ta arewacin Nigeria. Sunan mahaifin sa Nuhu poloma dan garin Balanga Gombe mahaifiyar sa Fatima Karderam Digema yar Bama ce a garin Borno. Ya girma a Jos da Kano. Ya karanta Geography a jami'ar Jos sannan yayi bautar kasa a garin Ibadan, Oyo. Ba a nan Ali Nuhu ya tsaya ba ya cigaba da neman ilimi musamman ta fannin sana'ar sa wata film inda yaje jami'ar California domin daukar darasi akan hada fina-finai. Ali Nuhu ya fara shirin Hausa a shekara ta 1999 inda ya fara a matsayin jarumi, ya fito a fina-finai 260 na Hausa sannan 150 na turanchi. Ali Nuhu shine jarumin da yafi kowane jarumi karbar lambar girmamawa mai ma'ana a Kannywood inda ya fara da karbar gwarzon jarumi a shekara ta 2005, Gwarzon matashi a 3rd Africa movie academy award, Gwarzon shekara  a the future award, Gwarzon shekara a Zulu African film Academy award 2011 da sauran goma sha hudu da ya karba a wurare daban daban.
Yana da mata daya mai suna Maimuna Ali Nuhu da yara biyu. Ali Nuhu ya kasance fuska ta Kannywood.
Wannan shine takaitaccen tarihin Ali Nuhu Muhammad daga shafin DAULAR MASOYA

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Gammamen Bayani AKan Layyah

◉ LAYYA [YANKA] ◉ Bismillahir Rahmanir Rahim: . Lallai bayani dangane da Layya tana da fad'i sosai amma zamu taqaita a taqaice. . ◉ LAYYA: ita ce dabbar da ake yankewa domin neman yardar ALLAH daga cikin nau'o'in tumaki da Awaki da Shanu da Raquma wad'anda suka cika shekarun yin layya, kuma sun ku6uta daga kowane aibi. .  →An shard'anta yanke dabbar layya a ranar 10 ga watan Zu-lhijjah da yini biyu masu bi mashi, bayan dawowa daga sallar idi, bayan kuma Liman ya yanke. [Fawakihud-dawaniy 1/440] . → Sheikh Abubakar Jaza'iriy ya fad'a acikin littafinsa mai suna [Minhajul Muslim] Yace: LAYYA wata dabba ce wadda ake yankewa ranar idi domin neman yardar ALLAH, ana yin ta ne don raya sunnar Annabi Ibrahim (AS) domin ALLAH Yayi wahayi zuwa gare shi da ya yanke d'anshi Isma'eel (AS), sannan kuma ya fanshe shi da Rago, ya Yanke shi a madadinsa. Kamar Yadda yazo acikin Alqur'ani ALLAH (SWT) Yace: . ﻭَﻓَﺪَﻳْﻨَﺎﻩُ ﺑِﺬِﺑْﺢٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ .  Ma'ana: "Kuma m...