A cikin kowane jinsi akwai wadanda ke take dokokin Allah, akwai kuma wadanda ba su mayar da ibadar Allah bakin komai ba, haka batun yake ga mata wadanda suka hada daga kan iyayenmu mata masu sauran zarafi a jikinsu, har zuwa mata masu tasowa.
Idan aka samu mace ta koma ga Allah kacokam, to mafi yawanci sai dai idan ta tsufa.
Ban hana kowa ya yi musu ba, amma ina so ya yi la’akari da gidan biki, mata nawa suke Sallah bayan sun ji kiran Sallar? Mata nawa za a ga sun yi kokarin suturce jikinsu a lokacin bukukuwa da maslahar jin tsoron Allah? Akwai tsoro, ta yadda da kyar za ka samu mata suna horo da aikata alheri da kuma hani da aikata sharri a tsakaninsu.
Babu shakka a cikin ’ya’ya mata, akwai wadanda suke yin ibada da kuma kokarin neman ilimin addini, ka daina zancen ni da ba kowa ba a fagen ibada ko neman ilimi, hatta mazan da ake yi wa kallon jarumai a wannan fage, ’yan matan nan sun zarce su nesa ba kusa ba. Sai dai idan abu ya yi yawa. Amma ina sane da cewa ko cikin maza akwai ’yan ba ya irina! Allah Ya ba mu ikon gyarawa.
Watakila daga cikin dalilan da suka sa mata ke yi wa addini rikon sakainar kashi, akwai hangen da suke yi cewa harkar ibada da neman ilimin addini na maza ne, saboda su ne ke hulda da cudanya da jama’a fiye da su.
Na biyu kuma, al’amari na Allah, dama su mata an halicce su da rauni, amma dai wannan dalili na rauni, bai dace ya zama sharadin da zai sa mata su rika wasa da ibadar Allah ba. Su tuna da mata irin su Nana A’isha da su Sayyida Maryam mana.
Abin da ya kamata ’yan matan nan su rika sakawa a rai shi ne, bambancin jinsi da ke tsakaninsu da maza, ya tsaya ne kawai a wajen wasu hukunce-hukunce na shari’a da kuma yanayin cudedeniya ta yau da kullum.
Amma a bangaren kiyaye dokokin Allah, hukuncin duka daya ne. Yadda Allah Zai tambayi namiji a Ranar Lahira, haka Zai tambayi mace! Yadda Allah Zai sanya maza a cikin Aljanna ko wuta, haka Zai sanya mata. Kowa tasa ce za ta fitar da shi.
Wani lokaci sai ka ji kamar ka zubar da hawaye, idan ka ga yadda aka bar mata nesa ba kusa ba wajen neman ilimin addinin Musulunci da kuma dagewa ga bautar Allah. Musamman matan da suke karatun boko, za ka samu yarinya na kusa da kammala digirinta, amma ba ta sauke Alkur’ani Mai girma ba. Kuma ta dakatar da karatun na addini kwata-kwata.
Ka daina maganar hukuncin rafkanuwa a cikin Sallah idan ta kama, hatta karatun Fatiha da wasu gajerun surori na cikin Alkur’ani Mai girma, wallahi suna gagarar mata da yawa. Kuma abin tashin hankali, sai ka ga mahaifan ’yan matan ba su kula ba. Su dai muradinsu yarinyarsu ta kammala digiri, ko ta yiwo talla ta kawo musu kudi.
Su dai matan nan, ka bar su da shakatawa da sha’awar duniya da kyale-kyalenta. Amma bangaren addini, lallai an bar su baya. Wanda wannan ne ma yake kara yawaitar zinace-zinace da mafi yawancin barnar da ke faruwa. Macen da ba ta Sallah sai ta ga dama, Sallar ma kuma ba a san hukuncinta ba, ta yaya za ta iya kare imaninta? Kada mu manta da mutuwa da kuma hisabin da ke gabanmu.
Allah Ya tabbatar da cewa, Sallah tana hana alfasha da abin ki, ashe rashin yin ta kuma, yana haifar da aikata alfasha da abin ki. To mafi yawancin mata, musamman ’yan boko da ’yan yawon talla ba Sallar suke yi ba sai sun ga dama. Ban fadi haka ba sai da na tabbatar, kuma laifin iyaye ne.
Abin haushi; abin takaici, wai sai ka samu yarinya Musulma, amma tana da’awar cewa ba za ta cika Sallah ba tunda ba ta yi aure ba! Ko kuma ba za ta rika rufe jikinta ba sai ta yi aure. Allah ne ma Ya yi mana agaji da aka samu makarantun Islamiyya, ba domin haka ba, da al’amarin ya wuce haka lalacewa.
Ina kira ga iyayenmu, don Allah ku zage damtse wajen ceto ’ya’yanku mata daga wuta, amma wallahi akwai matsala. Ina fatar Allah Ya sa mu dace, Ya yi mana arzikin cikawa da imani.
Nasir Abbas Babi ya rubuto ne daga Jihar Sakkwato.
Comments
Post a Comment