Yan wasan barkwanci na Arewa wato Arewa comedians sunyi Allah wadai da yadda sabuwar mawallafiya (Muneerat Abdulsalam) wato blogger a turanche ke yada batsa a kasar Hausa. Muneerat abdulsalam ta kasance tana daura vidiyoyi inda take maganganun batsa mutane na kallo abunda ya tunzura daya daga cikin Arewa comedians din mai suna Usman idris wanda aka fi sani da Ussy
Madobi ya fito yayi video akan masu tashoshin batsa na YouTube. Duk da cewa jarumin bai ambachi suna ba kuma bai kama sunan mutum daya ba amma Munnerat ta tsargu kuma ta fito ta maida martani cewa da ita ake, ta kuma hada su Arewa comedians gaba daya ta zage musamman Malam Hudu wato Mazaje Wanda take ikirarin ita mai goyon bayan shirye shiryen shi ce amma shi yake kokarin tona mata asiri saboda shine wanda yasa vidiyon da Ussy yayi a tashar sa. Wannan yasa Gulmar Arewa ta bi diddigi don zantawa da wasu daga cikin wadanda abun ya shafa inda muka samu mutum na farko wato MAZAJE.
A zantawar mu da Mazaje ya Nuna mana cewa shima abun ya Dade yana chi mai tuwo a kwarya kasancewar yadda yara da samari ke shiga YouTube suna kallon video Wanda ka iya lalata musu rayuwa, Mazaje ya kara da cewa shi ba yayi bane don ya kashe mata kasuwa amma yayi ne don ya taimaka sakon ya isa kunnen wainda aka yi don su, Cewar Mazaje, a yau idan Muneerat zata yi amfani da damar da Allah ya bata ta ringa fadakarwa ko wayarwa da jama'a kai ta YouTube ko wata kafar yada labarai zai zama mutum na farko da zai bata goyon baya, amma yada batsa irin wannan kamar fito na fito ne da Allah kuma bazan taba goyon bayan hakan ba, cewar Mazaje.
Haka shima Ayatullahi tage ya nuna Fushin shi kan vidiyon maida martani da Muneerat tayi inda yake cewa abunda ya bata mai rai shine har tana da bakin da zata iya maida martani ita da tayi abun kunya, sannan ya kara da cewa ki tuna ke musulma ce kuma zaki mutu ki koma ga Allah.
A karshe jami'in mu ya samu zantawa da Ussy Madobi inda ya bayyana mana cewa Ussy ya nuna rashin jin dadi matuka kan abunda masu tashoshin batsa ke yi a kasar Hausa, jami'in mu ya tambaye shi maganar fadan su da Muneerat Abdulsam, ga amsar da ya bashi "Ni Bana fada da ita ban ma San wacece ita ba sai dai kila in naga vidiyon ta zan gane cewa tana cikin masu tashoshin batsa kuma dama ni fada na da dukkan su nake, maganar martanin data maida ma ni sai daga baya naji kuma bazan biye mata ba saboda kamar yadda nace a baya jam'u nayi ita dai kawai taga ta fito a cikin su ne yasa ta harzuka, Alhamdulilah mutane sun fara sun fara ganewa cewa abunda suke bai dace da al'adun su ba, bai kama dace da addinin su ba. Ussy ya rufe da rokon mutanen Arewa da su daina bibiyan tashoshi Wanda ka iya zama musu Matsala tsakanin su da mahaliccin su.
Allah Ya Tsaremu Ya Tsari Iyalin Mu
Comments
Post a Comment