Yan uwana mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan fili namu mai matukar farin jini, wato Sirrin Iyayen Giji… Kamar yadda ku ka sani shi wannan shiri a na yin shi ne, don matan aure zalla, domin ba su shawarwari ta kowane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su Inganta Rayuwarsu, kamar gyara zaman takewarsu da mazajensu da mu’amalarsu ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki, irin abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci domin inganta lafiyar jikinmu da samun dauwamammiyar ni’ima da kuzari a jikkunanmu. To, uwar gida ba sai na yi miki dogon bayani ba, wannan makon ma shirin zai dora daga inda ya tsaya. Saboda yawan tambayar da na ke samu daga ’yan uwa mata yawancinsu su na ƙorafin ba su san meye sha’awa ba ko su ce ba su da sha”awa sam, siyasa na yi tunanin fadada bincike na a kan sha’awa. Don haka ku biyo ni:- Mece Ce Sha’awa? Sha’awa dai wata aba ce da Allah Ya halitta kuma ya sanya ta tsakanin halittun mutane da dabbobi bakidayansu. Allah ya na sanya sha’a...
Mace Kayan Dadi