Lalle wanda muka sani a kasarmu ta Hausa wata bishiya ce da mata suka fi yawan amfani da ganyenta musamman dan yin kwalliya a lokutan bukukuwan aure.
A nan ba ina nufin lallen da ake yin zanen jiki na siffa ba, ina nufin lallen da muka sani na gargajiya da aka daina yin sa musamman a wannan lokacin.
Ita dai bishiyar lalle tana da ganye launin kore da hure da kuma sayyu,wadanda dukkanin su ana amfani da su a sarrafa a yi magani da shi. Ganin yanda wasu sun dauki lalle tamkar kayan ado na mata kawai wadanda ko su a yanzu sun daina yin lallen nan na gargajiya da na ke magana a kai, inda suka rungumi amfani da wannan da ake siyarwa a shaguna wanda wannan lallen hade-hade ne kawai na wasu sinadirran da har illatarwa suke yi. Kusan abin da suke kallon maccen da take yin lallen gargajiya tamkar bakauyiya.
A yau wannan shafin ya dukufa wajen farfado da asalin maganin da muke da shi tun a zamanin da wanda aka dauki lokaci mai tsawo ana cin moriyarsu, amma sai gashi a yanzu an fara mantawa da su, shi ya sa wasu cututtukan zamani suka gagari magani.
-Na farko dai darajar mace mai yin lalle ba ta daya da wacce ba ta yi ko farin jinin su da tagomashin su ba zai zamo daya ba.
-Lalle kariya ce daga aljannu dalili a nan shi ne, akwai miyagun aljanun da suka tsani ganyen lalle.
-Lalle na karya sihiri a jikin mace, dan haka sai a nemi ciyawar aniya makomiya a dake tare da ganyen lalle a tunga shafawa.
-Lalle kariya ce daga cututtuka masu dama musamman na fata.
-Yin lalle a kafa na zuke cutar da ke a kafa, sannan yana tabbatar wa mace da irin ni’imar da ke gare ta.
-Maccen da take fama da infection kamar na kaikayin gaba ko makamantansu, sai ta tafasa lalle ta tunga yin zama a ruwan na tsawon sati biyu. In sha Allahu za ta rubu da shi.
-Ana iya shan ruwan ganyen lalle cokali daya da safe domin wankin dattin ciki amma mace mai juna biyu kada ta sha.
-Don gyaran fata, lalle ne a kan gaba wajen gyaran fata da matukar tasiri domin yana dauke da ‘natural toner’ wanda ba bilicin yake yi ba, amma yana da sinadiran da ke canza launin fatar ta zamo abin sha’awa kuma yana goge dattin fata.
-A bangaren gyaran fuska, lalle ya zarce sauran kayan kolliya domin duk yanda kike amfani da foda a fuskarki, to ba za ta kai lalle tasiri ba domin shi lalle har sha’awa yake karawa mace, haka kuma yana janyo hankalin namiji yaji yana sha’awar matarsa muddin tana yawan yin lalle.
-Ga macce mai warin kashi sai ta nemi lalle ta kwaba da turaren da tafi bukata sai dai a kula wani tirare ya kan janyo iska a jiki musamman idan aka gauraya shi da lalle, kamar Zakyash da Zafran, dan haka a san irin tiraren da za a gauraya da lalle. To a zuba isasshen ruwa a bokiti sai ki saka garin lalle a ciki sai ya jika tai ja zir sai ki tsiyaye ruwan ki diga turaren ki mai kamshi a ciki bayan kin yi wanka da sabulunki sai ki dauraye jikinki da shi idan kin nace da haka to ba ke ba warin kashi. Haka mazan da ke fama da matsala irin wannan suma za su jarraba.
Ta bangaren magani kuma, lalle ya kasance mai maganin cututtuka kamar haka:====
Lalle yana maganin ciwon yatsa da muke kira dan kankare.
Lalle na maganin cututtukan da ke lailayi a baki kamar zubar jini a sanda ake kurkurar baki ko kuraje ga harshe ko a cikin baki na ba gaira ba dalili. Sai a tafasa ganyen lalle a dunga kurkure baki da ruwan a kalla sau uku a wuni.
Ganyen lalle na maganin ciwon huhu kamar tarin asma, tarin t.b da tarin nimoniya da wasu cututtukan huhu na daban. Sai a tafasa ganyen a tarfa zuma gangariya a sha.
Lalle na maganin cin ruwa na yatsu idan aka kwaba garin da ruwan kal a dinga shafawa.
Lalle na maganin hauhawar jini da bugun zuciya. Sai a tafasa a tarfa zam-zam da zuma a dunga sha.
Macen da take da ni’ima ma’ana wacce Allah ya san ya wa yawan sha’awa a jiki da kuma damshin jiki da gamsarwa, idan tana yin lalle to sha’awar da ni’imarta ba za su gushe ba har sai sanda tsufa ya kai wani mataki.
Comments
Post a Comment