Wani ne mahaifinsa ya masa aure, sannan shi kuma ba ya son matar. Don tsabar ƙiyayya da yake nuna mata don su rabu, ba irin walakanci da ba ya mata. Amma ita ko ta kula da shi, abin da ta sa a gaba shi ne biyayyar da iyayenta suka ce mata ta yi wa miji tun daga gidansu shi ta ke yi. Ba ta taɓa kai ƙarar mijinta a gida cewa ga abin da yake mata ba. Duk da haka, ba ta taɓa gaya wa iyayen mijin abin da yake mata ba, duk da duka da zagin da yake mata da maganganu na cin fuska, ba ta kulawa..., Wata rana ya zo fita zai tafi wurin aiki, sai ta zo kamar kullum yadda ta saba, ta ce mishi maigida a dawo lafiya Allah ya ba da sa’a. Juyawarsa ke da wuya sai ya shimfiɗa mata mari a fiskarta. Nan take hawaye suka fara zubowa, hannunsa har ya kwanta a fiskar. To ashe akwai wani a waje yana sallama, suna amsawa ashe abokin mijin nata ne ya shigo har cikin PALOUR. Nan take matar ta share fiskarta ta nuna kamar ba wani abu da ya faru tsakaninsu. Shi kuma ashe abokin ya ga fiskarta kamar ba lafiya ba, don idanunta sun yi ja ba kamar yadda ya saba gani ba. Sai ya tambaye ta, Amarya lafiya na ga fiskar haka idon ki ya yi ja? Sai ta ce “ƙwaro ne ya shiga mani idanu na muttsuke shi yake damu na yanzu a ciki. Sai bai ce komi ba, da ya ga tana ƙoƙarin ɓoye wani abu, shi kenan sai suka sallameta suka fita, ta kuma cewa maigida Allah ba da sa’a sai kun dawo. Wannan abu da ta sake faɗa ya yi matuƙar ba wa mijin mamaki, nan take ya ce wa abokin nasa ya dawo ya ba wa matarsa nan haƙuri kan abin da ya mata. Suna shigowa sai ta ce lafiya na ga kun dawo? Sai mijin ya kwashe duk abin da yake mata tun farkon zamansu da ita har wannan abin da ya kasance a wannan lokacin ya gaya wa abokin nasa, ta ce a’a maigida wallahi ba ka min komi ba ni kam. Shi dai abokin yana ta ba ta haƙuri. Tun daaga wannan lokacin bai sake nuna mata walakanci ba, sai kuma ya fara nuna mata soyayya fiye da yadda take mashi. Da fatan za mu kasance daga cikin masu rike sirri dake tsakaninmu da abokan zaman mu daga mazanmu har matanmu, Amin.

Comments
Post a Comment