Skip to main content

Muhimmacin Saduwar Aure Ga Ya Mace

Saduwar aure babban ginshiki ne ko kuma a ce jigo ne a cikin zamantakewar aure wanda idan ana samun tangarda a kai walau ta bangaren mata ko mijinta, yana da matukar wahala zaman aure ya yi dadi.
Wani abin haushi ne, sau tari za ka ga ana samun matsala ta wurin mata a kan saduwar aure.
Wata matsalarta ba ta cika so ba, wata matsalarta rashin sanin yadda za ta yi wa maigida domin jindadinsu baki daya, wata matsalarta ma sai miji ya yi da gaske kafin ya shawo kanta ta amince ya kwanta da ita, wata kuwa ma ta mayar da saduwar aure kamar wani abu da yake amfanar da miji shi kadai ban da ita.
To masu irin wannan dabi’ar, su sani cewa ba ga miji kadai saduwar aure ke amfani ba, har su kansu akwai amfanin da suke samu idan suka yi saduwa da mazajensu. Filin Taskira ya yi muku nazarin irin muhimmancin da saduwar aure ke da shi ga mata:

(1) Saduwan aure yana maganin tarin gajiya (stress), idan kina da wata tattaunawa (interbiew) kamar gobe ko za ki yi magana a wani taron mutane, bincike ya nuna wadanda ke saduwan aure akalla sau biyu a sati sun fi yin wani abin kirki.
(2) Saduwan aure yana sanyawa a samu barci maidadi mai kuma inganci kuma a samu lafiya,saboda zuciya ta samu natsuwa da sauran abubuwa .
(3) Saduwan aure yana maganin ciwon kai, in kina fama da ciwon kai to saduwa tana maganinsa.
(4) Saduwan aure yana maganin mura wadda sanyi ya kama ki, sannan yana ba da kariya ga jiki daga kamuwa da sanyi wanda ka iya haifar da mura.
(5) Saduwan aure yana hana tsufa da wuri, bincike na kiwon lafiya ya nuna duk matar da ke saduwa, a duk shekara 12 tana komawa ‘yar shekara 7.

(6) Saduwan aure yana sanyawa mace ta rika samun saukin yin period (jinin al’ada), da yawa ‘yan mata suna fama da ciwo yayin period amma da sun yi aure sai su nemi ciwon babu.

(7) Saduwan aure yana canza ma mace yanayin tsarin jikinta inda kasusuwanta zasu kara girma da wasu sassan jikinta.

(8) Saduwan aure yana kara ma zuciya lafiya, sanin ku ne ciwon zuciya shi ne ciwon da ya fi kashe mata a duniya, cin abinci mai inganta lafiya da rage kitse suna taimakawa sannan saduwan aure yana taimakawa wajen magance zuciya daga kamuwa da ciwo...,

(9) Kwanciyar aure yana kara ma mace lafiya a kwakwalwarta sannan ya cire mata bakin ciki da damuwa ya sanya ta nishadi.
(10) Saduwan aure yana taimakawa wajen inganta lafiyar ‘bladder’ ga mace.
(11) Saduwan aure yana sa mace ta ringa jan hankalin Mijinta saboda saduwa a kai a kai yana sa kyan fata da bakin gashin kai har da tsayi ma.
‘Yan’uwa mata sai himmatu wurin gyara abubuwan da za su kyautata wannan ibda ta aure. Allah ya taimake mu baki daya amin, mu a hadu a mako mai zuwa, insha Allah.

Comments

Post a Comment

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

LAKANIN DA HADIN KARIN GIRMAN NONO DA KUMA DANKO DA MATSE GABA GA MATA

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa. Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..   Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:====== A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin kudin ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu. Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa: Kankana Ayaba Gwanda Goba Lemo Tumatir Rake Aya Kwakwa Dafaf...