Babban Malamin addinin Islama, Sheikh Ahmad Gumi ya soki Shugaba Muhamadu Buhari bisa nasarar da ya samu na lashe zaben shugabancin kasa na 2019 da aka gudanar a ranar 23 ga watan Satumba kuma aka sanar da sakamakon zaben a ranar 27 ga watan Fabrairu.
Sheikh Gumi ya koka kan yadda Buhari ya yi gadarar cewa shine zai lashe zaben tun kafin a fara kirga kuri'u da al'umma suka kada.
Kamar yadda muka samu rahoto daga Daily Nigerian, Sheikh Gumi ya ce, "Tun kafin a kirga kuri'u, Shugaba Muhammadu Buhari ya yi imani 100% cewa shine zai lashe zabe. Ta yaya ya san shine zai lashe zaben duba da cewa kan 'yan kasar a rabe ta ke kuma ana fama da talauci da fatara????
Yace "Ba dai zai ce ayyukansa da cancantarsa bane suka sanya shi ya lashe zabe. Tattalin arziki, tsaro da rashawa duk sunyi katutu a kasar. Kasar na fama da karancin ayyukan yi, ana samun karuwar kashe-kashe na kabilu, ana samun karuwar sace mutane, talauci da rashawa a ko wane lungu da sako.
"Abinda kawai zai sanya shi ya bugi kirji ya ce shine zai lashe zabe itace karfin mulki da ya ke dashi a matsayinsa na shugaba wanda shi ake nufi da halastaciyar rashawa.
"Duba TraderMoni da aka kaddamar watanni kadan kafin zabe sannan ana amfani da EFCC wurin musguwanawa abokan hammaya, amfani da kudin gwamnati wurin shirya kamfe, mamaye gidajen talabijin da rediyo na gwamnati da kuma amfani da masallatai domin yin kamfen da amfani da sojoji domin razana masu zabe da sauransu, halastaciyar rashawar na da yawa." inji shi
Sheikh Gumi ya koka kan yadda jam'iyyar APC ta rika rabawa mata a kauyuka N500 domin su zabi APC tare da amfani yara wanda shekarunsu bai kai na zabe ba wurin kada kuri'a da kuma yim amfani da mimbarin malamai domin kamfe.
Babban malamin ya yabawa dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar saboda jajircewarsa. Ya kuma shawarce shi ya yi watsi da sakamakon zaben ya garzaya kotu domin a bi masa hakkinsa kamar yadda Shugaba Buhari ya yi a baya.
A karshe Ya kuma yi kira ga al'umma su cigaba da zama lafiya tare da biyayya ga doka da oda.
Comments
Post a Comment