Gwanda tana da abubuwan da jikin dan’adam yake bukata da dama, ga dai amfaninta ga fata nan mun fada, masamman ta wajen kiwon lafiya, yadda fatar za ta yi karfi, lafiya da kyawun gani, gashin kai kuma ya yi santsi da karfi, ba zai rika kakkaba ba, namiji bai damu da sanko kamar yadda mace ta dauke shi ba, don in ma bai da shi yana iya yin tal-kwabo ya fita da kan a haka, ita kuwa abin kunya ne koda kuwa a wajen gyaran gashi ne, a irin wannan matsayin gwanda tana da rawar da take takawa ba ‘yar karama ba.
– Hawan jini daya ne daga cikin cututtukan da suke gallabar dan’adam, to gwanda tana da sinadarin Potassium mai yawa wanda shi kuma ya kan taimamaka wajen dai-daita jinin mai cutar tare da barin kwakwalwa a farke kowani lokaci.
– Gwanda kan kyautata ganin mutum, in mutum zai iya cin yanka biyu a kullum, ganinsa zai iya zama haka ba tare da ya ragu don girman shekaru ba, wannan saboda yawan sinadarin ne da ake zaton zai iya yin wannan aikin, bawai don ita gwanda ce an san dole ta yi haka ba.
– Gwanda kan taimaka wajen kyautata kwayoyin garkuwar jiki, don tana dauke da sinadarinnan na Beta Carotene wanda wannan yana daya daga cikin aikinsa.
-Kumburi wanda ya bayyana da boyayye duk cututtuka ne da suke cutar da jikin dan’adam, to gwanda takan taimakawa wajen hana kumburin kunne na din-din-din ko sanyi ko zazzabin influenza.
– Cutar zuciya ma kan yi illa, to gwanda tana da sinadaran da suke taimakawa, tana da Nutrients mai yawa wadanda suke maganin rubabben Cholesterol da haka sai ta yi maganin yuwuwar kamuwa da rashin bugawar zuciya, ko tsayuwar kwakwalwa.
– Sai kuma raunuka irin na jiki, gwanda kan taimaka ta yadda rauni zai yi saurin hadewa ya warke, in aka yanka gwandar sai a shafe raunin da shi, a nan muna ba da shawarar cewa duk raunin da mutum zai yi, ya yi kokarin samun likita don karbar allurar Tetanus, wannan kuma wata cuta ce mai kisa, wace take saurin shiga jikin dana’dam da zarar ya yanka, ko ya soke ko kuma ya yi wani rauni, in har ba a yi maganinta da gaggawa ba to akwai yuwuwar za ta yi kisa. Gwanda ba ta da amfani a nan.
– Wani lokaci a kan sami kurarraji ko maruru wadanda sukan yi ta damun mutum na tsawon lokaci, to a nan sai mutum ya sami gwandarsa ya nuke ta, ya hada ta da kindurmo ya shafa a wurin da marurun yake gallabarsa har sai ya bushe, in Allah ya so za a ga bambanci cikin gaggawa.
– Akwai kuma ciwon sukari, duk da cewa gwanda tana da zaki, amma kuma tana taimakawa wajen sassauta matsalar, alal akalla ba ta a cikin manyan ‘ya’yan bishiyar da ake hana mai cutar ya ci ko ya sha.
– Hanji masamman babban na karshe wanda daga shi ba-haya yake fita waje, wanda ake kira a Turance Colon ya kan kamu da cutar Cancer to Fibres din dake cikin gwanda suna da karfin da za su iya yin maganin wannan Cancer din kuma su ba hanjin kariya, ban da wannan ita ma ‘ya’yanta sukan taimakawa wajen magance wasu matsalolin saboda sinadaran da ke cikinta, sai dai ita ‘ya’yanta daci ne da su ba kamar sauran ‘ya’yan bishiyar ba, ‘ya’yan suna dauke da Bitamins da sauran sinadaran da za su taimaka mata wajen ida nufi.
Ga wadanda suka yi shaye-shaye har ya wuce kima hantarsu ta lalace ‘ya’yan gwanda kan taimaka, in mutum yana shaye-shaye hantarsa kan tattare ne ta cure wuri guda, sai ta gaza yin aikinta kamar yadda ya dace, to ‘ya’yan gwanda kan janye cutar matukar za a dena dibar barasar, sai mutum ya sami ‘ya’yan gwanda busassu ya nike su, ya rika sha a cikin lemon tsami, zai rika sha ne a kullum da tazarar lokaci kafin ya ci abinci, haka zai yi har zuwa wata guda cur, don gurbacewar ba ta fita lokaci daya kacal da haka in sha Allahu za a ci nasara, sai dai in mutum ya koma dibar barasar wata kila ba zai jima a duniya ba.
Kamar dai yadda muke fadi ne a kullum, matsalolimmu shi ne in aka sami dan bishiya guda to cin koshi za a yi masa, wanda hakan kuwa matsala ce ga jikin dan’adam, babu ko shakka rashin cin wadannan albarkatun gonar jikkunammu sukan shiga wani yanayi wanda cuta karama in ta cafki mutum sai ta kwantar da shi, to amma in aka ci sama da yadda jikin yake bukata nan ma wata matsalar ce ta masamman, sai mutum ya yi kokarin dai-daita abincinsa don kaucewa da na sani a cikin rayuwa. Allah ya ba kowa lafiya ameeeeeeeeeeeeen,
Comments
Post a Comment