Taura A mafi yawan kabilun nahiyar Afrika, ana dora wa kan mahaifiya alhakin fadakar wa da yin nasiha ga budurwar da za a aurar. A mafi yawancin lokuta, kanwar mahaifiya ce ke shirya budurwa domin ta fuskanci kalubalen da ke cikin zaman aure. Amma lamarin ba haka ya ke ba a kabilar Banyankole da ke kudu maso yammacin kasar Uganda, inda aka dora wa kanwar mahaifiyar budurwar da za a aurar alhakin sanin namijin da za a bawa auren diyar 'yar uwar ta. Babban aikin kanwar uwar budurwar da za a aurar a kabilar Banyankole shine tabbatar da kuzarin ango ta fuskar saduwa kafin a kai ga aura masa diyar 'yar uwar ta. Domin tabbatar da kuzarin angon, a wasu lokutan, kanwar mahaifiyar kan yi saduwar jima'i da angon diyar 'yar uwarta domin tabbatar da kwazonsa a gado. Kazalika, kanwar mahaifiyar budurwar za ta bawa angon tabbacin cewa diyarsu cikakkiyar budurwa ce da ba ta taba sanin wani da namiji ba. Ita ce kuma ke da alhakin tabbatar da cewa diyarsu da zasu aurar ba ta taba sanin ...
Mace Kayan Dadi