Skip to main content

Posts

Wani dan Izala mai suna Ahmad Abdullahi Assaminaky, ya koma Shi’a a Najeriya.

Wani dan Izala mai suna Ahmad Abdullahi Assaminaky, ya koma Shi’a a Najeriya. Ahmad, wanda dan kungiyar Izala ne a baya ya wallafa wannan bayani ne yau a shafin sa na Facebook, inda yace;=== “DAGA YAU NA KOMA DAN SHI'A MABIYIN ZAZZAKY Wallahi na dade ina nazarin shin anya malaman mu na Izala a kan gaskiya suke kuwa? saboda a duk malaman kasar nan kai haddama duniya gaba daya a iskar nan ta yau dake juyawa babu wani malami da yake damabiya kuma mabiyan na shi har su rika mutuwa saboda kare rayuwar shi sai Zakzaki.” “Kai ko annabi ne daga cikin Annabawa aka kashe mutum sama da dubu saboda kare rayuwar shi kafin akai kan shi abin a jin-jina ne balle malami, wannan abubuwa sun sani tinanin anya wannan mutun ba mujaddadi ba ne kuwa ? domin ko asiri yakewa mabiyan nan na shi asirin yakai asiri, ni dai duk dadewar da nayi ina Ahlussunna ban tabajin za'azo kashe wani malamin Izala inji cewa zan iya bada rayuwa ta dan in kare shi ba, dubi girman malam Ja’afar wallahi masallacin nan duk ...

GANIN JINI FA BA SHINE BUDURCI BA..

Korafin samari yayi yawa cewa 'yan matan da suke aura ba sune suka fara kwanciya dasu ba. Hujjar su anan ita ce, sunyi saduwar Aure ta farko da matan nasu amma basu ga jini ya fito ba.. Gaskiya wannan ba hujja bace da za'a yi wa mace kallon 'yar Iska. BUDURCI:- Wata fata ce dake cikin farjin mace matashiya, kuma fatar ba mai kwari bace sannan tana yagewa ne da zarar ta samu takura. Mace tana rasa budurcinta ne ta wadannan hanyoyin.. 1. Saduwa da namiji 2. Daukar kaya mai nauyi 3. Guje-guje 4. Hawan keke 5. Hawan doki ko jaki 6. Mummunar faduwa 7. Sanya danyatsa a farji 8. Haihuwa.. Wasu matan ko an sadu dasu fatar budurcinsu bata yagewa har sai sun zo wajen haihuwa ananne zata yage. Dan haka nake kira ga samari don Allah duk wanda ya auri mace Budurwa kar yace lallai sai ya ga wannan jinin***** Idan har baka ga wannan jinin ba to kar ka yiwa matarka kallon'yar iska ko mazinaciya domin inda yar iska ce ko mazinaciya da kasani tun kafin kuyi Auren, azatona tunda sanda kay...

Yadda Za'a gujewa kamuwa da ciwon ido a lokacin damina

Lokacin damina lokaci ne da ake yawan kamuwa da cututtuka kamar su zazzaɓin typhoid, amai da zawo, Hepatitis, shawara, mura, ciwon hakarkari da sauransu:==== Mutane da dama kan yi fama da ciwon Ido, kunne da maƙogoro matuƙa. Cututtukan idon da ake yawan kamuwa da su a wannan lokaci sun hada da yawan zyin hawaye a ido, matsanancin ƙaiƙayi a ido,Ido zai yi jajawur, apolo da sauran su. Malaman asibitin sun bayyana wasu hanyoyin da za su taimaka wajen kaucewa da magance matsalar ido. Ga hanyoyin 1. A guji saka hannun da bashi da tsafta a cikin idanu. Hannayen da basu da tsafta na dauke da kwayoyin cuta da ake kira ‘Virus da Bacteria’. Tsaftace hannu da amfani da tsuman goge fuska mai tsafta na da mahimmanci wajen gujewa kamuwa da wadannan cututtuka. 2. Yin amfani da maganin ido na digawa Idan ido na yawan yin hawaye ko yana yawan yin ja ko kuma kaikayi kamata ya yi a garzaya asibiti domin samun maganin ido da za a riƙa digawa domin a warke. 3. Yin amfani da gilashin ido Gilashin ido na han...

Yadda Zaki Gyara Fuska Ba Tare Da Kinyi Bleaching Ba

Gyaran fuska tayi fari da sheki naturally batare da kinsa chemical a fuskarki ba. Sannan zanyi bayani akan matan da suke tsintar kansu da wani irin wari ko kuma wani baki-baki a cikin armpit dinsu(hammatarsu) ko bakin fuska daga gefe daya due to bleaching products or sunborn. Dafarko idan kika ga fuskarki na irin wannan duhun daga gefe ko kusa da idonki to cikin biyune kina shafa cream kina shiga rana ko kina shafawa lokacin gari da zafi. Na biyu ko kina shafa man dayafi karfin fatarki to dai koma menene ya janyo ga hanyar da xakibi ki goge wannan tabo zaki sami madara ta ruwa kisata a fridge tayi sanyi sosai sai ki goga a wannan tabon naki bayan minti ashirin saiki wanke sannan idan gari da zafi zaki sami ruwan sanyi kisa cottonballs ki tsoma ki dora akan tabon saiki bari yayi minti 5 saiki cire cotton din ki shafa mai a fuskar.I dan kika yi sau uku saiki dinga yiwa fuskar gaba daya.Am assuring you zaki mamaki sosai. WARIN HAMATA-waddata sami kanta da irin wannan warin ko bakin sait...

Maganin 15 da Baure Keyi

Tsawon shekaru aru-aru, 'baure wani nau'i ne na dangin kayan marmari da ya shahara a duniya ta fuskar dandano da kuma amfani ga lafiya. Wani sabon bincike da jaridar Guardian ta wallafa ya bayyana muhimmancin baure wajen magance cututtuka da dama kama daga ciwon suga zuwa cututtukan fata.  'Baure ya kunshi sunadarai da dama masu gina jiki da suka hadar da fiber, antioxidants, vitamin A, vitamin C, vitamin K, B vitamin, potassium, magnesium, zinc, copper, manganese da kuma iron.  Wani bincike da aka gudanar a shekarar 2016 ya tabbatar da cewa, sunadarin ficusin da dan itaciyar baure ya kunsa na taka rawar gani wajen magance radadin ciwon suga. Ga wasu kadan daga cikin tasiran da baure ke yi wajen magance cututtuka da kuma bunkasa lafiyar jikin dan Adam:====== 1. Magance kwarnafi da tashin zuciya. 2. Hawan jini. 3. Bunkasa lafiyar zuciya da jini. 4. Ciwon daji wato cutar Kansa. 5. Rage nauyin jiki. 6. Inganta lafiyar mazakuta da kuma ni'imar ma'aurata. 7. Magance ciwo...

Kaifin basira da magunguna 4 da kwallon kankana ke yi a jikin Mutum

Kankana ta kasance daya daga cikin 'ya'yan itatuwa mafi shahara a doron kasa kuma mutane da dama su kan yi santi kwarai yayin kwankwadar ruwanta musamman wadanda kwayoyin halittun su masu bambance dandano ke aiki kwarai. A yayin da kankana ta kasance cikin dangin itatuwa da ake kiransu 'ya'yan duma, 'ƙwallayen cikin da sun ƙunshi sunadarai masu tarin alfanu da kuma tasiri wajen inganta lafiyar jikin dan Adam. Sai dai kash da yawan mutane su kan watsar da ƙwallon kankana a sakamakon rashin sanin muhimmancin su wajen inganta lafiyar su. Wadannan ƙwallaye da kankana ta kunsa suna da arzikin sunadarai da suka hadar da fatty acids, proteins, minerals (magnesium, poatssium, manganese, iron, zinc, phosphorus, copper), vitamin B (thiamine, niacin, folate) da kuma calories.  Bincike ya tabbatar da cewa, ana amfani da ƙwallayen kankana a matsayin abinci a yankunan nahiyyar Asia da kuma wasu yankunan daular Larabawa ta Tsakiya inda ake gasa su kuma kwadanta da ganyayyaki irin...

Abinda yasa Mata Basa Ganin jini a Ranar Darensu Na Farko

 Ba za ka iya kirga adadin aurarrakin da suka mutu ba sakamakon rashin fitar jini daga gaban amaryar da angonta ya aureta a matsayin budurwar da shi zai bareta a leda A yadda muka dauka shi ne, sai ango ya ga amaryar kaca-kaca cikin jini a darensu na farko, shi ne zai tabbatar masa da cewa amaryar tasa bata taba sanin da namiji ba Ita kanta amaryar cike ta ke da fargaba na ko angon nata zai tono jini ko kuma a’a ko da kuwa ta san ba ta taba aikata lalata da wani da namiji ba kafin aure Ba sabon labari bane ba a wasu zamaninnika da suka gabata cewar har jefa amaryar a ke yi da zarar mijinta ya yi saduwar farko da ita kuma jini bai fita ta gabanta ba Har farin kyalle ake shimfidawa akan abin kwanciyar amarya da ango a darensu na farko don a tabbatar da zubar jini daga gaban amaryar, kuma cikin alfahari za a yi ta yawo da kyallen ana nunawa manya fa cewa “Wance bata zub da mutunci ba kafin ta yi aure” Wannan dabi’a ta fitar jini daga farjin mace a jima’inta na farko ba mu kadai ke da ...