◉ LAYYA [YANKA] ◉ Bismillahir Rahmanir Rahim: . Lallai bayani dangane da Layya tana da fad'i sosai amma zamu taqaita a taqaice. . ◉ LAYYA: ita ce dabbar da ake yankewa domin neman yardar ALLAH daga cikin nau'o'in tumaki da Awaki da Shanu da Raquma wad'anda suka cika shekarun yin layya, kuma sun ku6uta daga kowane aibi. . →An shard'anta yanke dabbar layya a ranar 10 ga watan Zu-lhijjah da yini biyu masu bi mashi, bayan dawowa daga sallar idi, bayan kuma Liman ya yanke. [Fawakihud-dawaniy 1/440] . → Sheikh Abubakar Jaza'iriy ya fad'a acikin littafinsa mai suna [Minhajul Muslim] Yace: LAYYA wata dabba ce wadda ake yankewa ranar idi domin neman yardar ALLAH, ana yin ta ne don raya sunnar Annabi Ibrahim (AS) domin ALLAH Yayi wahayi zuwa gare shi da ya yanke d'anshi Isma'eel (AS), sannan kuma ya fanshe shi da Rago, ya Yanke shi a madadinsa. Kamar Yadda yazo acikin Alqur'ani ALLAH (SWT) Yace: . ﻭَﻓَﺪَﻳْﻨَﺎﻩُ ﺑِﺬِﺑْﺢٍ ﻋَﻈِﻴﻢٍ . Ma'ana: "Kuma m...
Mace Kayan Dadi