Skip to main content

TSARABA GA MARASA HAIHUWA

Assalamu alaikum jama'a barkanmu da yau,wannan rubutu da zaku karanta gabadayansa zaiyi magana ne akan rashin haihuwa,kama daga abubuwan dake haddasa matsalar zuwa hanyoyin da zaa magancesu,mu fara da abubuwan dake haddasa matsalar::


1. Wajibine asani ita haihuwa lamarine daga ubangiji shike bayarwa ga wanda yaso.
2. Fitar farin ruwa ga mace ko namiji ta sanadiyar ciwon sanyi, shima kan hana samuwar ciki. 3.Haka ma karin mahaifa wato fibroids shima na hana samuwar ciki.

4. Masana aharkar iyali na bayyana cewa sai maniyyin namiji yakai tsawon kwana 3 wato kimin 72 hours kana yazama zai iya samar da ciki. Shiyasa ko gwajin zaA yiwa mutum na test akan kwayoyin halittar sai maniyyin da yayi 3days kana su iya ganewa. Donhka sai akiyaye da kuma tabbatar da ansamu kwanakin nan kana asadu musamman agab da mace zatayi al'ada da sati ko kwanaki 4 zuwa 5.

5. Yana da kyau mace ta daina saurin tashi bayan gama jima'I domin maniyyin yasamu damar gangarawa cikin jikinta musamman cikin mahaifa. Haka kuma kafin mace ta fara al'ada da kwanaki alokacin take fitar da kwayayen halittarta inda zasu jira haduwar maniyyin namiji ta yadda zasu gangara mahaifarta.

6. Sannan akwai tsari na ubangiji inda zaAsamu wani bai da matsala itama matar lokaci da baiyiba.

7.ba wai ruwan da ake gani shine maniyi ba. shi semen ake kiranshi. kaurinshi ko rashin kaurinshi bai da nasaba da hana haihuwa. matukar akwai isasshen kwayoyin maniyin a cikinsa. shi kwayoyin maniyi sai da microcope ake ganinsu. kuma zaka gansu kamar yayan gwadari ne suna yawo a cikin semen din. kuma daga yan kwadu suke fitowa su biyo ta vas deferense. su hadu da semen din sannań su shiga cikin mahaifa in anyi jimai. lallai karancin maniyi yana hana haihuwa.

domin sai kirgan yayan maniyin yakai miliyan arbain kafin ya iya ma mace ciki. shi yasa ake sperm count.

8.RASHIN ISASHSHEN MANIYYI

yawanchin wannan matsalar tana faruwa saboda rashin kwanciyar hankali da kuma rashin kyakykyawan abinci,rashin kwanciyar hankalin ma yafi kawo matsalar daga macen ko na namijin,
9.idan al aurar namiji ta faye kankanta tana haddasa matsalar.

10.idan ya zamo maniyyinsa baya fitowa sai da kyar ba lallai bane ya iya yi mata ciki


11.SAMUWAR WANI CIWO A JIKIN MUTUM

12.YAWAN AMFANI DA KAYAN DAA

suna haddasa
.toshewar mahaifa
.hana haihuwa
.kaikayin gaba
.kurajen gaba
.ciwon ciki
musamman ma wanda zaa cewa mace ta chusa a gabanta ,shi yafi kawo wannan matsalar,sai kuma wanda baa san mahadinsa ba
13.SHAN MAGUNGUNAN HANA DAUKAR CIKI idan mace tana amfani da ire iren wadannan magungunan,koda ace ta dena to zasu iya haddasa mata wannan matsalar
14.SABAWAR MANIYYIN MASU JIMA'I (maniyyin daya ya riga dayan zuwa) sai wanda ya riga zuwan ya lalace kafin na dayan yazo
15.RUWAN SANYI
yana raunata mazakutar namiji,shima yana iya hana haihuwa
SHAWARWARI DA MAGANUNGUNA
vitamin E yana yin maganin cutar rashin haihuwa ta bangaren maza da mata dan yana magance tsinkewar maniyyi,harma da maganin saurin kawowa (inzali),ana samunsa a alkama da latas man alkama da korayen ganyayyaki,da hatsin da baa surfa ba,dan ana fitar dashi a wajen tankade ko surfe,


QARANCHIN MANIYYI
Mai zauren fiqhu ya taba fitar da wata fa'ida a wani posting dinsa akan matsalar karanchin maniyyi, yace ga namiji ana amfani da zaitul lawus cikin shayi domin samun karuwar maniyyi
TARIHI
wani mutum yazo wajen imam hasanul basari yace masa inaso ka roka min Allah ya bani haihuwa,sai yace masa kaje ka yawaita istigfari,mutumin yaje yayi tayi kuma ya samu haihuwar,
WATA ADDU'AR
ya yawaita karanta (RABBI HABLI MIN LA DUNKA ZURRIYATAN DAYYIBAN INNAKA SAMEE UD DU A ) cikin sujada da kuma bayan kiran sallah,

A yawaita cin kayan gina jiki masu kara ruwan maniyyi ga namiji dakuma hada zuma da habbatussauda dakuma garin kistul hindi ana shan cokali 3 sau 2 duk bayan yan satittika.
Motsa jiki na taimakawa sosai.
bayan haka kuma masu wannan matsalar yanada kyau su ziyarchi asibiti su nemi shawarwarin likitoci,

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

LAKANIN DA HADIN KARIN GIRMAN NONO DA KUMA DANKO DA MATSE GABA GA MATA

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa. Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..   Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:====== A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin kudin ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu. Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa: Kankana Ayaba Gwanda Goba Lemo Tumatir Rake Aya Kwakwa Dafaf...