A wannan makala Mujalla za ta kawo mu ku wani binciken zamani kan magungunan da Habbatus-sauda ke yi ga jikinmu. Mu na fata Allah Ya sa mu dace, amin. Ana kiran Habbatus-sauda da sunaye da yawa, misali ana kiranta da"Habbatul Baraka" wato kwaya mai albarka, da turanci 'the blessed seed', Black Cumin, Nigella Sativa, Black Caraway da sauransu. Binciken ya dangata habbatus-sauda da matukar amfani wajen magance cututtuka daban-daban, sannan ta na taka muhimmiyar rawa wajen kiwon lafiya, cikin yardar Mai Duka. Ana samun Habbatus-sauda daga 'ya'yan tsiron "Nigella sativa". Hakanan an gano cewa, Shekaru aru-aru da suka gabata dubun-dubatar al'ummar nahiyar Asia da Afirka ke amfani da ita a fannin kiwon lafiya da kuma magance wasu cututtuka dake addabar jikin dan-adam. Ba tare da bata lokaci ba, ga jerin magunguna 23 da ake samu daga wannnan tsiro mai albarka, da fatan a sha karatu lafiya, sannan da fatan za'a jarraba domin gane wa ido amfaninta. 1....