Kyakkyawar fata mai laushi da sheki abar alfahari ce ga ko wacce mace. Dukkan matan da su ka amsa sunansu ba sa yin sakaci ko kadan wajen kula da gyaran fatarsu kai har da ilahirin jikinsu.
Hakan kuma na kara mu su matsayi a wajen mazajensu.
Wadansu matan kan yi amfani da mayukan shafe-shafe na zamani wadanda suke kunshe da sanadirai da ke da matukar lahani ga fata harma ga lafiyarsu.
Amma a wannan lokaci masana sun karkata hankalinsu wajen bincike akan tsirrai don samar da hanyoyi gyaran jiki na dabi'a marar illa ga lafiyarmu. Wannan dalili ya sa a yau mata da yawan gaske su ka juya wajen amfani da wadannan hanyoyi da ba su da illa ga lafiyarsu.
Kafin natsawa cikin wannnan batu, abin tambaya anan shine, me ke dusashe kyan fata ?. Abubuwan da ke haifar da dusashewar fata da bushewarta sun hada da aikace-aikacen yau da kullum, rashin isasshen barci, karancin abinci mai gina jiki, tsananin zafi (rana ko wuta ) shan taba da dai sauran su.
Idan aka cire shan taba kusan ace wadannan abubuwa ne da ba makawa a rayuwarmu ta yau da kullum.
To idan haka ne ina mafita. A dalilin haka ne mu ka wallafa wannan shafi don kawowa uwar-gida da amarya hanyoyin da za su bi su gyara fatarsu ba tare da zulumin samun wata matsala ba. Kuma hakan zai bayu wajen inganta rayuwar aure tsakanin ma'aurata.
1. Lemon Tsami.
Ana bukatar, ruwan lemon tsami babban cokali 2. Babban cokali daya na sikari.
A hada su waje guda a gauraya, a shafa, a jira tsawon mintuna 10 sannan a wanke da ruwan dumi. Za ai haka sau biyu duk sati.
Wata hanyar ta lemon tsami ita ce, a samu lemon tsami ya yanka don a samu ruwansa, sai a shafe jiki da ruwan a jira tsawon minti 10, a wanke da ruwan dumi, daga bisani a shafe jiki da kokumba. A yi haka kullum.
Ko kuma a samu ruwan lemon tsami a cakuda da babban cokali biyu na zuma a shafa a bar su tsawon mintuna 20 sannan a wanke. Za ai hakan sau 3 duk sati.
2. Kokumba.
Karamar kokumba guda daya. Baban cokali 2 na "yogurt".
A nike kokumbar a gauraya da yegot din a shafa a bar su minti 5 a wanke da ruwan sanyi. Ayi hakan sau uku 3 duk sati.
Ko kuma a yanyanka kokumba a shafe jiki da ita da dare, a wanke da safe da ruwan dumi. Ai haka kullum kafin a kwanta.
Ko a matse ruwanta a hada da na lemon tsami a shafa idan sun bushe a wanke daruwan dumi. Ai hakan a kullum.
3. Zuma.
A samu kyakkyawar zuma marar hadi, a shafa bayan an yi wanka, a shafa da kyau sai ta game ko'ina.A jira mintuna 5, sannan a wanke da ruwan dumi. Za ai hakan a kullum.
4. Man Zaitun.
Man zaitun cokali 1, ruwan dumi, hankici ko kyalle mai laushi.
Tun farko a shafa man zaitun a fuska da wuya, aci gaba da murzawa musamman wajen goshi,kunci da hanci, har tsawon mintuna 3. A tsoma hankicin a ruwan dumin sai a matse ruwan da ya debo sannan a dora shi a kan fuska tsawon sakan 40, a sake tsoma shi a ruwan sannan a goge man a hankali.
Za ai hakan da dare kafin a kwanta barci a kullum.
5. Man Kwakwa.
A samu man kwakwa a dumama shi kadan, a shafa ai ta cuda shi da yatsu tsawon mintuna 3, a kyale shi zuwa safiya, sannan a wanke da ruwan dumi. Ai hakan kullum kafin a kwanta barci.
6. Karot.
A tanadi karas kamar guda 5, sai danyar citta kamar sala guda, ruwa kofi daya.
Za;a yayyanka karas da citta ,sannan a nika su da bilanda ko a kirba gwargwadon abin da mace ta ke da shi, sai a zuba ruwa a tace a sha. Zai fi kyau ai hakan da safe sau uku a kowanne mako.
7. Ayaba.
A samu nunanniyar ayaba guda daya. Babban cokali 2 na madara, sai kankara.
A hada ayaba da madara a cakude, a shafa a fuska da wuya a bar su zuwa mintuna 15, sannan a wanke, sai a danko kankara a dinga gogawa tsawon minti daya. Ai haka sau biyu a mako.
8. Hoda (Baking soda).
Babban cokali daya na bakin soda. Babban cokali daya na man zaitun. Rabin cokali na zuma.
A cakuda su cikin mazubi, a shafa a fuska zuwa wuya, a bar su tsawon mintuna 10, a wanke da ruwan sanyi, a tsane danshin da kyalle mai laushi. Za ai haka sau daya a mako.
9. Abinci Mai Gina Jiki.
Wannan sanannan al.amari ne cewa cin abinci mai gina jiki yana da matukar amfani ba wai ga fata kadai ba harma ga dukkan gangar jiki. Don haka ne masana suka tabbatar da cewa, yawaita cin abinci mai gina jiki musammanma yayan itace da ganyayyaki na samar da kyakkyawar fata mai laushi da sheki.
Comments
Post a Comment