Haryanzu dai babu wani tabbaciko bayani ko dalili dake bayyana dalilin saurin kawowa ba, saidai wasu bayanai akan dalilan da ka iya bada haske gameda matsalar saurin kawowa ga maza Sune kamar haka:::::====
1. Matsalar rashin karfin mazakuta ,Idan namiji baya da karfin gaba to akwai yiwuwar asami saurin kawowa lokacin jima'i , haka kuma, idan akwai karfin zakari to akwai yiwuwar dadewar yin jima'i mai tsawo tsakaninin ma'aurata biyu. Saboda haka, saurin inzali na iya zama wani lokacin alama ce ta rashin karfin zakari.
2. Yanayin halittar wasu mazajen. Wani haka Allah Ya halicce sa ko minti 1 baya iya yi da mace. Amma wannan baya nufin baza'a iya samun saukin yanayin ba. Za'a iya neman magani ko Allah Yasa a dace.
3. Samuwar hadar iabun hawa wanda zai iya sanadiyar shafar al'aurar mutum, Hadari wanda ya shafi lafiyar al'aura na iya haddasa matsalar saurin kawowa.
4. Magungunan kayan mata/da'a da mata keyi.
Magunguna na matsi da mata ke sakawa cikin gaba domin matse/tsuke farji Idan mace tayi amfani da wani magani gabanta ya tsuke/matse fiye da yanda maigidanta ya saba jinta zai iya sa maigidan yayi saurin kawowa saboda karuwar dadi ko dandanon jima'i.
5. Cututtuka masu shafar lafiyar jima'i, kamar cututtukan sanyin mara na maza da mata.
6. Ciwon damuwa ko fargaba na iya haddasa saurin inzali. Misali, idan mutum yayi sabuwar amarya budurwa ko bazawara , idan yana fargabar ko zai iya gamsar da ita ko damuwa akan wani abu, wannan tunani zai iya sanya saurin inzali a cikin saduwar su.
7. Yin istimina'i da gaggawa da wasu matasa keyi kamin suyi aure, musamman yara don gudun kada a kamasu (wasa da al'aura ko zinar hannu). Yana shafar lafiyarsu, yana haddasa saurin kawowa lokacin jima'i.
8. Gado daga wajen mahaifan mutum Akwai yiwuwar mutum yayi gadon saurin kawowa daga mahaifinsa ko kakansa ko wani jininsa, wato tsatstsonsa. Wato haka duk "family" nasu suke amma bai sani ba.
9. Matsananciyar sha'awar yin jima'i. Idan mutum ya kosa yayi jima'i , fitinar sha'awarsa ko kamuwa da yawa zata iya sanya shi yayi saurin kawowa da zaran zakarinsa ya shiga jikin mace ba tare da bata wani lokaci ba.
10. Nau'in wasu magungunan. Akwai wasu magungunan da "side effects" nasu zai iya haddasa saurin kawowa ga mutum. Da sauransu, mu takaita haka.
Comments
Post a Comment