Menene Amfanin Lallai?
In nace lalle wasu zasu dauka zanen henna ake nufi ko, to lalle dai na gargajiya wanda muka rabu da yinsa yanzu shi ake magana akai.
1)-Na farko dai lalle Kariya ce daga sihiri, Kariya ce daga aljanu sannan kuma Kariya ce daga cututtuka da dama.
2)-Yin lalle a kafa na zuqe cutar dake kafa sannan yana maintaining dumin mace, bi ma ana yana inganta ni’imar mace ba tare da ya gushe ba.
3)- Ga duk mace mai infection, ta tafasa lalle in ya dan huce sai ta yi sit bath dashi na sati biyu in Allah ya yarda zata warke
4)- Ana iya sha ruwan lalle cokali 1 don wankin dattin ciki amma banda masu ciki.
5)- Don gyaran Fata; lalle dai ba karamin tasiri yake dashi wajen gyara fata ba, domin shi natural toner ne wanda ba bilicin yake yi ba amma
yanasa haske mai kyau kuma yana goge dattin fata,
6)- A bangaren gyaran fuska, yana sa fuska tai kyalli, laushi, da haske in an kwaba da ruwan Kwai amma
banda kwaiduwar kwan.ki kwaba ruwa ruwa amma ba sosai ba ki lizimci shafa shi kullum 30 mins kafin
wanka sai Kinga bambanci a cikin sati biyu Insha Allahu.
7)- Ga masu son hasken fata, ki kwaba lalle da ruwa, ki shafe a jikinki inya bushe ki dirje da man zaitun za kiga canji.
8)- Ga masu fama da pimples, yar’ uwa
ki hada lemon tsami da lalle kwabi mai dan tauri amma ba sosai ba kina shafa wa a fuskar ki bayan watanni kuraje zasu mutu sannan tabo bazai zauna ba ga hasken fuska da laushi.
9)-sannan gamai son kamshin fata,
Ki kwaba lalle da turaren ki mai kyau na ruwa wanda ake durawa ki zuba isasshen ruwa a bucket
ki sa garin lalle ta jika tai já zir sai ki tsiyaye
ruwan ki diga turaren ki mai kamshi ciki Bayan kinyi wankan sabulunki sai ki dauraye jikinki dashi inkin lizimci haka to bake ba rabo da kamshin jiki in sha Allahu
10) Sannan ga Amare Kafin kiyi dilke na aurenki ki kwaba lalle mai kyau tare da turare mai maiko, turaren gargajiya mai mai, ki jika kamar bucket daya
kada yayi ruwa ruwa sosai kamar dai kunu, kullum sai ki shafa a dukkan jikinki sai ki zo ki saka turaren
wuta akasko ku burner ki rufu akai ki turara jikinki har sai hayakin turaren nan ya shiga jikinki sosai sai ki fita
kije kiyi wankan ki,za kiga canji a fatar ki rapid canji kuwa.
Fata za tayi laushi, haske da kuma santsi. Two months before
bikin ki zaki iya wannan kedakanki kuma zakiji dadin hakan.
11) Lalle nasa cikan gashi,
ba yasa gashin kan mace ya zube, yana da matukan amfani wajen gyara gashin mace, inda wasu ke tura (steaming) gashin su dashi ma’ana.
12) A karshe mata na yin ado da lalle wajen kara kyaun kwalliyar su.
wanda su ke zanawa a jikin su
Amfanin Bagaruwa A Jikin Mace
Amfanin bagaruwa (Large Acacia tree)
Bagaruwa, itacenta, ganyenta da 'ya 'yanta duka Maganine kuma ana samunta a kasashe da dama kamar su INDIA, AUSTARALIA, Da kuma Qasashen Larabawa sannan anhi samunta a busashshen wuri.
BAGARUWA tana saurin saukarda Masassara, da kuma tsayarda zubar jini ko wane iri, kuma ana amfani da ita wajen yiwa Dabbobi Magani.
Ana Amfani da BAGARUWA wajen Magance Matsalolin fata, tsutsar ciki, tana karawa Hakora qarfi da haske kuma tana maganin ciwon hakora, sannan ana amfani da ita wajen magance matsalar ciwon suger, haka tana saurin saukar gudawa.
Konewa, Toyewa, ko Gogewa
Ana daka 'ya'yan Bagaruwa a riga zubawa ko kuma a samu 'ya 'yan ta wayanda basu bushe ba a riqa matsa ruwanta a cikin wurin.
Ciwon Hakori, Hasken su, ko warin baki
Ana samun iccen bagaruwa ayi asawaki da shi kullum in za'a kwanta bacci haka idan aka tashi daga bacci.
Ko kuma a samu itacenta a hada ta da jar kanwa a rinqa kuskure baki da shi duk za'a kwanta da kuma idan an tashi bacci.
Lafiyar Mata
A hada 'ya 'yan Bagaruwa da itacenta da Rihatul-hulbi a sa a wuta idan Suka tafasa sai a sauke a tace a samu buta a zuba a riqa tsalki da shi bayan 10 mint a sake sarki Wannan yana Matse macce kuma yana maganin toilet Infection sannan yana saka ta kamshi sosai.
Matsalar idanu
A samu ganyen Bagaruwa a tafasa idan ya tafasu a juye a buta a riga wanke idanu da shi duk safiya wannan yana kawar da jan ido da kuma yanar ido In shaa Allahu.
Amfanin ta ga Maza
Duk wanda ke saurin Biyan buqata kafin Matarsa Zai iya amfani da 'ya'yan bagaruwa ya daka ta sai ya zuba ruwa ya rinka sha In shaa Allahu zai ga cenji.
Comments
Post a Comment