Skip to main content

ILLAR SAKA YAWU A FARJIN MACE YAYIN JIMA'I


Bayanin da zai biyo bayan taken wannan rubutun yana da nauyi, don haka ayi hakuri da kalmomin da za'a ji, muhimmancin dake tattara da bayyana bayanin a fili yafi boye bayanin saboda amfanar al'umma gaba daya

Sannan yana daga cikin manufar shafin Datti Assalafiy shine wayar da kan al'umma game da abinda zai amfane su a rayuwa da zamantakewa, da fallasa asirin abubuwan da zasu cutar da al'umma gwargwadon abinda zamu iya

Na karanta wata doguwar takadda wanda wani kwararren Likitan mata ya wallafa yake bada shawara domin ma'aurata su kiyaye akan abinda yake matukar cutar da lafiyar su a rayuwar aure ba tare da sun sani ba

Likitan ya bayyana cewa duk ma'auratan da suke yin amfani da yawun bakin su (saliva) a gurin jima'i to su yi gaggawar denawa, saboda yawu yana kunshe da wasu sinadarai masu karfi da suke taimakawa wajen narka abincin da ake ci, wanda idan suka shiga cikin farjin mace suna iya haddasa mata mummunan infection mai matukar wahalar magani, likitan yayi bayanin cewa, wasu infection na iya yin shekara 5 a farjin mace kafin ya bayyana illarsa

Wato yana daga cikin dabi'ar mafi yawa daga cikin ma'aurata, su kan yi amfani da yawu wajen karawa jima'i ko saduwa armashi, saboda akwai matan da haka Allah Ya halicce su suna da karancin ni'ima, ni'ima da ake bayani anan shine; wani ruwa ne fari mai santsi da yake fitowa daga gaban mace a lokacin da sha'awa ta motsa, ko kuma a lokacin da ake jima'i

To akwai matan da basu da irin wannan ni'ima, akwai matan da kuma ana cikin jima'i sai ni'imar ta dinga daukewa, daga nan sai su fara jin zafi, anan ne ma'auratan suke saka yawu domin al'aurar tasu tayi santsi a samu abinda ake so, to irin wannan yawu da ake sakawa illa ne sosai ga farjin 'ya mace

Mutanen da sukayi sabon aure sunfi fuskantar daukewar ni'ima a yayin jima'i, akwai mata sabbin amare da basu taba sanin 'da na miji ba, to saboda tsoron zafin buda hanya a kwanakin amarci ni'imar su tana saurin daukewa, sai suyi amfani da yawu, ko man shafawa ko dai wani abu mai kama da haka, saka yawu kuskure ne balle mayukan shafawa da sauransu da ake sarrafawa da chemicals

Shiyasa kashi 90 cikin 100 na mata ma'aurata da suke amfani da yawun bakinsu ko wasu mayuka a yayin jima'i suna dauke da infection kala-kala ba tare da sun sani ba yana cutar da lafiyan su tare da rage musu armashin jima'i, wanda kan iya haddasa cin amanar aure ko ma rabuwa.
Ga matan da suke fama da matsalar rashin ni'ima ko daukewar ni'ima yayin jima'i, to ya dace su nemi shawarar kwararrun masana a wannan fanni, amma tabbas suyi gaggawan dena amfani da yawu ko wasu mayukan shafawa a lokacin jima'i
Don haka ma'aurata da sauran samari da suke sha'awar yin aure a kiyaye, sannan ya dace a yada wannan shawara saboda amfanar al'umma gaba daya
Allah Ka tabbatar mana da alheri Ka magance mana matsololin gidan aure Amin

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

Sirrin Samun Saurayi Nagari

Duk wata mace da ta gagara samun miji, to lallai akwai abun dubawa a kanta. A matsayin ta na mace ta taba kokarin samun namijin kirki amma bata samu ba? Ga wasu shawar’wari daga bakin masana. Idan har duk yadda kikayi wajen neman miji wanda yake sonki kuma yadamu da ke amma hakar bata cimma ruwa ba, to gwada wadannan abubuwan ki sha mamaki. A watan azumi da ake ciki, ki kokarta wajen kyautata dangantakarki da Allah, ki bada kyauta ga mabukata. Haka ki yawaita fara'a da nafilfilin dare, da rokon Allah ya kawo miki miji nagari da kuma dacewa da sa'a a wannan rayuwar. Ki rage yawan fada, da yawan surutu tsakanin ki da sauran 'yan uwa mata ko maza. Kada kuma azumi ya hanaki kwalliya da gyaran jiki, yadda ya kamata ace ko wace mace na yi. Kokarta wajen kamun kai, magana da kowane irin mutun, shiga harkar da bata shafe kiba, gulmar kawa ko aboki, yawaita bakinciki don kawarki nada saurayi, ke baki da shi. To fara duba kanki, ki gani wai me kikeyi wanda ya sabama yadd...