Kowa ya san cewa da an ambaci amare, ana nufin matan da ake musu shiri na musamman domin tarewa a gidan miji.
Ko wane yanayi yana da irin tanadin da ya kamata a yi ma sa domin idan amarya ta shiga dakin angonta, ta more amarcinta ba tare da fuskantar wata matsala ba.
Shi ma kuma ango ya san cewa lallai yayi dacen amaryar da yake burin samu kuma bai yi zaben tumun dare ba.
Dangane da yawan wayar da nake samu a kwanakin nan, na gabatowar azumi yawanci amare ne suke neman yadda za su yi da fatarsu don su yi kyau da sheki a lokacin bikin nasu.
To masu neman biyan wannan bukata kusha kuruminku don na yi muku tsaraba.
Bisa binciken da na yi ga abun da na fara samowa, Insha Allah wani satin zan kara turo yadda za a cire baki da ke makalewa a wurare, kamar su giwar hannu da yatsotsun kafa da hannu da guiwa da kuma matse matsin cinya, Insha Allah. Amma ga wannan yandu kuna iya farawa. Ana bukatar abubuwa kamar haka:-
DILKA
Ki samu dilka ki zuba mata ruwan zafi, idan ta yi laushi sosai sai ki ajiye ta a gefe.
KURKUM
Ki fasa kwai ki cire yalo din ki zuba kurkur a ciki da dan lemon ki buga sosai ki ajiye a gefe.
Dorot
Ki tanadi turaren dorot dinki.
Ki shafe jikinki da wannan kurkur din ko’ina, idan ya bushe sai ki dauko wannan dilka din ki goge kurkur din da shi ki yi ta murzawa sai komai ya fita ya yi fes, sai ki samu manja ki shafe jikinki da shi, sai ki zuba dorot ki rufe jikinki ruf amma banda kai, idan kika dan jima sai ki fito ki je ki yi wanka, washe gari ba sai kin shafa manja ba da kin shafa kurkur ki yi turaren idan kin fito ki goge da dilka. Haka za ki yi har tsawon kwana hudu, idan ba ki da ‘pimples’ ki yi har fuska. Idan kina da su, in kin gama ki shafa lemon tsami a fuskar. Kar a manta idan an gama wankan a zuba madarar turare a dan ruwa kadan a watsa a jiki.
Comments
Post a Comment