Shin kana fama da matsalar jujuyar kai, wanda yake yawan mai mai tuwa, wanda yake haddasa ciwon kai mai radadi?...
Bayan haka kuma kana bincike wajen neman mafita, ko magani wanda zai saukaka maka daga tsananin radadin da yake damun ka?
To ga hanyar da zakabi yakai dan uwa /yar uwa, domin wadannan magungunan suna taimakawa matuka.
(1)Danyan citta cokali daya. Idan kuma busassace karamin cokali.
(2)Sai Kuma sarkin magungunan wato itaciyar Iklilil jabal, wato Wanda a harshen turance ake Kira da (Rosemary)
(3)Zaka samo Lavender, wanda a Kira da harshen larabci cewa (Kazama).
(4)Zaka samo Yansun.
Yadda zaka hada shine :
Zaka zuba karamin cokali na kowanne maganin amma banda danyar citta, zaka zuba cokali daya ne ita, amma kada amanta, abaya munce idan busassace karamin cokali, ko rabin cokali ya isa.
Zaka tafasa ruwa sai kazuba ruwan dumi akai, amma wanda aka dafa sosai, bayan anzuba sai karufe kabar shi, bayan mintina kadan sai katace karika shan kadan kadan,lokaci,lokaci,insha Allah akarshe zakaga sakamako mai kyau.
Amma idan wannan tayi wahala to kabi wannan bayanin zaka samo:
Kisdul hind.
Garin habbatisauda.
Garin hulba.
Garin halitit.
Da Kuma garin kanin fari.
Bayan haka wannan yana taimakawa wajen saukaka matsalolin zuwan jinin alada, ko sanyin mara, ga mata, da Kuma maza.
Bayan anhada sai arika tafasa wa anayin suracensa, ana Kuma zuba wani aruwa wanda aka tafasa kana sha, da zuma ko madara insha Allah wannan hanyama Zaa iya samun waraka biiznillah.
Comments
Post a Comment