A yau zamu fara ne dayanda amarya zata gyara jikinta har zuwa ranar aurenta Wanda wannan ranace da akeso ta fito tsaf gwanin sha awa Wanda na fitar da wannan topic din ne saboda duba da yanda kowacce idan ta tashi nata gyaran jikin se ta bari se anzo daf da bikin wata sauran ma sati 2 Wanda awannan lokacin lokaci ya kure bazaki taba samun accurate result ba ,domin agaskiya asalin gyaran da akeson kiyi anason kifara ne daga sauran wata uku wasu ma sauran 6 month suke farawa amma de ke duk tsanani kar ya wuce sauran wata uku biki zaki fara naki gyaran saboda awannan lokacin kina da chance sosai koda ace kin Shafa wani abun ya bata miki skin dinki zaki iya replacing da wani daban hakanan koda wani hadin dakikayi be karfe ki ba nanma zaki samu kisake chanja wa kuma daman kyaunta duk wani chanji da kk son gani alokacin yakai wata uku ananne zaki fi samun kyakkyawan sakamakon gyaran da kikayi.
Gyaran amare suna nan dayawa Wanda zan lissafo miki su dukka in fadi miki yanda zakiyi Wanda inason kifara su daga yau da kanki har lokacin da za ashiga asalin satin bikin wannan ma idan kinga zaki iya sekiyi idan kinaso se kije gurin gyaran jiki su miki na sati guda.
Kedae ki tabbatar dazarar kin fara gyaran nan acikin wata guda kifara ganin changes idan har babu chanji gaskiya kimin magana insan INDA matsalar ke.
1. SHAN RUWA: A duk lokacin da za ayi magana akan gyaran jiki dazae Sa laushin jiki da kyaun fata to dole ne afara da maganar kara level din shan ruwa dakike yi akullum koda ace kinasha to yakamata awannan karon ya karu kamar da cup 4 kowacce rana kyaunta ace kina iya shan 8 to 10 cups na ruwa kowacce rana bawae dole se kinci abinci ba a a koda babu abinda kikaci ma zaki iya kiyi tasha Wanda kuma shi ruwan nan anason idan kina da hali kisamu asalin bottle water tsaftace kidinga shansa se ki ajiyeshi carton kina sha sosai saboda shi besa yawan fitsari hakanan besa ka cuttutuka kinga ga tsafta ga rashin fitsari zakiyi ta shansa sosai kowacce rsannidan kinga shan ruwa sosai ze dinga baki wahala se kidinga blending fruits zallansu da ruwa kar kisa sugar aciki se yazamto miki kamar ruwa shima kidinga shansa kamar cup 6 arana shima gaskiya ze gyara miki fata sosai idan har kika dimanci shansa dayawa kullum kullum amma kar kice wae zaki dinga shan juice na kwali ko kwalba domin shi gaskiya idan kika cika yawan shansa ze saka miki katon tumbi ko kuma basir ko angurya se kiga anzo gurin sex kina bada matsala saboda haka ki kiyaye duk wani watery Abu dazaki kai cikinki banda wadanda aka kara musu sinadarai akai yazamto kawae natural abubuwa zaki dinga sha sannan kiguji sugar gaskiya domin ze dinga cinki ta kasa yana kulle miki Mara lokacin sex saboda ke sabon shiga CE shiyasa zakiga amare dayawa suna complaints akan sex zaki ne yake musu yawa se ya kwanta amarar su se lokacin sex kiga tanajin gurin kamar ze balle don zafi kuma irin wannan yana hana maza suji asalin kololuwa na sex saboda zaki kulle ta karshe duk dama zanyi Karin bayani akan hakan atopic dinmu na tsuma jiki koda zumace zaki siya ki tabbatar bata da sugar aciki asalin original ce.
2. ABINCI: Dole ne sekin fara gyara daga cikin sannan kidawo waje saboda haka abinci kowacce yadanganta da abinda kike ci ne amma de lalle ne kidinga cin isasshen abinci kar yanayi na makaranta ko zuwa aiki ko wani guri yasa kidinga fashin cin abinci domin shi abinci dole se dashi ne duk wani sinadarai dazaki sha zasuyi miki aiki saboda haka kikiyaye sosai kuma kidinga cin lafiyayyun abinci dazasu kara fidda miki shape yazamto kowacce rana kina hada salad meyawa kicinyeshi ,kar kicika cin abinda ze birkita miki ciki don kuwa shifa ze dinga rage miki ruwan jikinki ne ,kidage da cin kayan dadi sosai awannan watannin.
3. SINADARAN GYARAN JIKI: to anan fa matsalar take don gaskiya awannan yanayin idan har kinason kiga best result dole se kinsha supplement na gyaran jiki masu ciko da mace saboda anfison aga amarya acike bazaki gane dagaske nake ba se kin zauna nan awaje namiji yagama tsaraki yana CE miki kin hadu kina jin kanki kawae se ranar first night zaki fara ganin chanji afuskarsa dazarar yasaka hannunsa akan breast dinki yaji ko hannunsa basu iya cikawa to nan kam fa se ahankali don a irin mazan yanzun nan wani alokacin ma zefara miki complaints din yanason nono ,saboda haka shawarata agareki karkiyi wasa da nono yar uwa domin kukam ma yan mata shine babban jarinku saboda akwanakin farko wlh maza basu jin dadin sex kasancewar ke sabon shiga CE kuma akulle gurin yake zakiga sex din bae wani armashi sosai idan saurayi kika aura kamma lokacin dukkanku kwamacala zakuyi tayi sedaga baya zaku fara gane asalin dadin shiyasa akeson ace kina da breast sosai dazae dinga Jan hankalin shi sosai tunda sex din alokacin bawani armashi har se ansaba to kinga atleast zae samu wani abun dazae dinga janye mishi hankalin shi don gaskiya maza suna matukar jarabar taba breast kuma duk azatonsu yanda suke ganin girman shi arigarki haka yake azahiri shiyasa nake baki shawara don Allah tunda akwae hanyoyi dayawa na Karin nono karkije mishi dasu fici fic. Yanzu nidae shawarar dazan baki tafarko akan gyaran nono shine kisamu centrum ki gwada shan na wata uku dinnan ahankali zasu cicciko koda kina dasu daman can zakiga jikinki yadan ciccika gwanin sha awa saboda akwae wata zatayi aure setake min tambaya akan breast nace tasha centrum ni fa har namanta da anyi hakan se jiya take kawae naga text dinta tana min godiya wae wlh jikinta cikin 2 month ko ina ya ciko kowa se tambayarta ake wani irin gyran jiki takeyi wlh nidakuka ganni bantaba shansa ba bani siyarwa balle ace tallnshi nake amma nayi mamakin yanda take taban labarin har pics seda ta tura min.
Saboda haka koda bayanshi ma akwae wasu supplement dazasu kara miki kyau lokacin aurenki yakamata kinemo asalin original kisha domin yawancin mata dakike ganin jikinsu sumul sumul kamar su sukayi Kansu kigansu kamar alashe yanzu duk su suke sha shikuma gaskiya beda side effects dayawa domin suna kokari gurin inganta shi sosai.
4. SHAFE SHAFE: Sai kuma ananne matsalar take don kowacce damuwarta ta mulka abun dazata ga immediate result ne Wanda nikuma INA sake jaddada miki kiyi kokari kiyi maintaining din asalin skin colour dinki kar kice wae zakiyi dabarun dazaki kara haske kije ki ranar biki aga fuska fara jiki yayi baki ko ko INA yayi different colour se kace wata Aljana.
👉idan ke farace man dazaki Shafa ajikinki da sabulu da komi daman can na farare ne saboda haka amma yakamata kikara ganin changes na nuna cewa kina gyara na musamman ne saboda haka wannan soap din idan kin tashi wanka zaki dinga mixing nashi da shower gel na soap din sannan idan kinzo mai din ma ki mixing nashi da gel da oil dinshi agaskiya nan take zaki ga aikin mayin indae har daman can me kyau ne sedae karki bari kiyi fari gau yanda surutu ze miki yawa duk dacewa ke farace.
👉idan ke tsaka tskaine kalar ruwan kasa kalar da akafi samu kenan cikin mutanen mu to kema hakan take kuma kitabbatar baki banbance mayin fuska Dana jiki dukka mai daya zaki Shafa kar wani gun yayi baki wani yayi fari.
👉idan kekuma kinyi duhu sosai nanma kar kice wae sekinyi haske zaki yi kyau amma kisamu mai me kyau Wanda zesa skin dinki yayi glowing sosai.
5. DILKA: Idan akazo maganar dilka ni banga laifinki ba idan kin fara shi da wuri domin kuwa jikinki ze saba dashi kiga laushin ya zauna irin haka sekiga namiji daga yasa hannunsa ajikinki zeji kamar ya nutse don laushi maza kam gaskiya suna mugun Rena mace Mae kaushin jiki saboda haka kifara dilkarki da wuri koda na 30 mins ne kowacce rana amma fa kar kidinga saka mishi kurkum saboda shiga rana Zeke batashi
Zaki samu dilkarki cokali Biyu kijika da ruwan dumi idan tajiku ta kumburo seki saka mata kwanduwar kwai da peak na ruwa kona gari ki matse lemon tsami akai ki bubbugashi sosai zaki iya kara madarar turare saboda kika she karni sosai idan suka hadu suka kwabu zaki iya shafe dukka jikinshi dashi kizauna ya bushe kamar minti 30 amma ni irin wannan zan baki shawara daki zauna abandaki kina jiran ki bushe why not alokacin kihau yin gyaran tafin kafa da tafin hannu at d same tym kina bushewa kinga kin samu kinyi Abu Biyu kenan.
Idan kuma kina da masu Tayaki kamar yara kannenki to sekiyi kwabin dilkar da kauri kamar lalle se kudinga dirje jikin dashi sosai ana gurjewa hakan yafi fitar da datti kuma yafi shiga fatar jiki.
Idan kika dimanci yin dilka kowacce rana acikin wata ukunnan keda kanki zaki fara sha awar yanda jikinki yake taushi sosai hakanan saboda samun glowing skin ma zaki iya adding man ridi acikin hadin dilka din sedae kirage yawo da zirga zirga.
6. SAMUN HUTU: A gaskiya anason kimaida kanki cikin isasshen Hutu awannan lokacin ba ason yawan fita ko yawan stress ko wasu abubuwan na daban abinda yafi dacewa shine kibawa kanki Hutu na musamman domin a wannan lokacin ne duk wani gyare gyare da kikeyi zae fi zama ajikinki yayi miki aiki sosai saboda haka ko kayan shafe shafe ne yafi aiki alokacin da kike bacci ,bayan baccin da kikeyi nadare anason kowacce rana kidinga kara wani baccin na musamman kamar da rana haka hakanan ba ason kidinga shiga rana yanasa kuraje idan kina dilka hakanan fuskarki zata Dan kone tayi duhu ,hakanan anason kicire damuwa da tunani aranki sosai yanda zaki samu kwawalwarki tazama fresh kar kice tunanin biki ze addabeki wlh duk zaki kwanjale abanza saboda haka kisawa ranki sauki kisamu kije da kumarinki.
7. TAFIN HANNU DA KAFA : A gskiya suma suna bukatar gyara na musamman da kulawa sosai saboda bakaramin rawa suke takawa a rayuwar aure ba musamman gurin sex shiyasa akeson su tabbata cikin taushi da laushi domin kuwa anan namiji ze renaki yaji kaushi ahannunki duk danasan cewa yawancin mu aikin yau da kullum ne yak jawoshi amma mu kula sosai ganin cewa sun biyu acikin wadannan watannin shiyasa ma idan son samune kidinga yinsu kullum idan kuma baki da tym sau 3 asati.
Muhimmancin hannu yafi yawa saboda shikam DA shine zaki sarrafa namiji gurin foreplay to kinga dole suyi taushi domin musamman kan mazakutarsa babu namijin da zae yadda kiyi ta sukarshi da kaushin hannu kice wae kina Sosa mishi kan mazakutarsa.
Hakanan shima tafin kafa yana da wani boyayyen sirrin gurin yiwa namiji susar mazakautarsa da tafin kafa hakanan akwae sex dazakuyi da shi kanshi tafin kafarku kubiyu zamuyi shi agaba shiyasa daman class ne aji gurin cikin laushi don alama CE ta mace me ni’ima.
Idan zakiyi gyaran tafin kafa da hannu to zaki nemo ruwa tafasasshe kibarshi yafara salamcewa se zuba shower gel din da kk wanka dashi aciki kokuma kinemo shampoo kizuba aciki zaki iya zuwa asalin manyan shaguna kinemo asalin gel na wanke tafin kafa kizuba cikin ruwan wasu suna saka spirit ko cikin murfi daya yayi zaki iya matse lemon tsami aruwan kokuma kisaka ruwan khal seki jefa kafarki da tafin hannunki aciki suyi ta tsuma kamar 30 mins ko awa daya seki fitarsu kisamo towel me tsafta ki goge sosai dashi se alokacin zaki zaki iya kankarar datti still da reza atafin kafar idan kinsan kina da datti idan babu kuma se dauko asalin man dayake saka laushi na tafin hannu da kafa kishafesu dashi kigyra faratanki ki kankare su kar kice zaki dinga lalle alokacin kibari tukun se biki yazo.
8. GYARAN FUSKA: A nan kam asalin damuwar take saboda wata ma zakiga fuskarta lafiya lau amma gurin gyaran fuska zata takalowa kanta wani abun yazo yazama damuwa saboda haka shawarata agareki shine kifara duba meye damuwar fuskarki tukun tun afarko idan kinsan baki da wata matsalar rahes ko wani abun to kekam scrubbing duk sati zakiyi ko sau 2 asati karki dameta da gyare gyare.
Hakanan idan kinsan kina da matsalar kuraje kowanni abun to kiyi kokari kinemo maganin shi tukun se kin tabbatar kin gama magance shi sannan kifara scrubbing fuskarki
Dangane da maganin kurajen fuska zaki iya kisamu gel guda Wanda ya karbeki kidinga shafawa shi kadai tukun koda yaushe idan zaki kwanta yawancin naga wasu suna daukar vista plus ,da sabulun black sport asalin original din ko mekako se kidinga Shafa shi 15 mins kafin kiyi wanka idan kinyi wanka zaki kwanta se ki Shafa gel din kar kidinga kara komi bayansu dahaka ze fice ko ya ragu seki fara scrubbing fuskarki.
9. SCRUBBING: Shi kuma wannan shima bawae wani abun dazakiyi tayi kullum bane kawae anayine don kashe dattin fuska da kwayoyin cuta sekuma yana saka wa irin kurajen ko wasu abubuwan dasuke fito miki su kone su mutu sedae shima ya kasu kashi kashi ne.
👉akwae Wanda zaki hada da kanki natural abubuwa kamar kihada zuma da lemontsami ,ko tumatur ,ko ganyen aloe vera.
👉akwae Wanda zaki sayi asalin shi scrub din dakanki se kiyi dashi.
Dafarko zaki zauna tukun kigyara packing din gashinki zuwa baya ba ason ya taba miki gashi ki daura towel akanki ko dankwali se ki Dora zani ajikinki dafarko zaki turara fuskarki cikin ruwan dumin kamar 5 mins se ki goge ta bushe tukun sannan kizo ki kwanta ki bayar da fuskarki amata massaging tukun koda da handkerchief ne sannan kiyi applying scrub din a fuska a barshi ya bushe seki wanke.
👉zaki iya jika fuskarki da ruwan dumi se ki samu scrub din kiyi ta massaging fuskarki dashi na mins kadan se kizo ki wanke shi kizo ki busar da fuskar kidauko mai kifara moisturizing fuskar dashi
Hakanan shima scrubbing na fuska yadanganta da Wanda kk son yi domin akwae Wanda zaki Shafa yoghurt ko kwanduwar kwai ko Zuma se ki lullube fuskarki cikin ruwan zafi kiyi steaming dinta daga nan kicire ki wanke fuskarki.
Zaki iya koda kina zaune ne kisamu lemon tsami kiyi ta goge fuskar dashi kamar na mint 30
Shidae scrubbing na fuska ba ason ki yawaita shi.
10. KAMSHI: Yawancin mun dauka wae shi kamshi se anzo biki daf ake sabawa dashi nan kuwa shima kamata yayi tun ana sauran sati uku kifara yin Wanda ze saba da jikinki irin wannan zakiga koda kinyi kwana daya bakiyi ba kina kamshi hatta kayan jikinki ze fara kamshi duk dattinsa.
Amma dafarko anason kifara kashe duk wani gurin dayake feso da karni ko gumi ajikinki wato irin su hammata da matse matsi da kasan nono duk sune kofofin dasuke kawo warin jiki abun da zakiyi shine kullum kika tashi kisamu lemon tsaminki da madarar turare zaki ganshi Dan kadan ga tsada amma se tabbatacen kamshi inde me kyaun kika samu zakiyi kwana Biyu kina kamshi se kifara goge hammata da lemon tsamin kina Dan dangwalar madarar turaren kina sake goge gurin haka zakiyi asauran sassan jikinki ma amma idan kinsan kina fitar da ruwan gumi daga matse matsinki to kifara daka alimun seki saka agun ya tsotse tukun sannan kishafa lemon tsamin
To idan kina yin hakan kinga jikinki ze Dan rage saurin fitar da wari daga nan kuma zaki nemo asalin turaren wuta na turara jiki kisamu Wanda ta iya hadi me kama jiki tayi miki sosai kullum sau Biyu kidinga yin hayaki dashi dahaka ze saba da jikinki zakiji ko INA kika taka kina kamshi bayan shi ma idan kina da wadata zaki iya hadawa da wankan turare da akeyi da furanni masu kamshi acikin ruwan wanka da turare shima yana kama jiki sosai.
11. GASHI: A gaskiya shikam daman yakamata tuntuni kibashi kulawa sosai kisamu de Wanda zakiyi adon amarci dashi duk dama cewa nataba nuna muku styles dazakiyi koda baki dashi amma de gaskiya kiyi kokari kibashi kulawa kisabarwa kanki da kamshi sosai tun kafin aure karki saba da tsamin gashi don yana kashe sha awar sex agun maza saboda haka shawara ta agareki shine yazamto kina kawata shi da mayuka da kuma shampoo koda yaushe kina wankewa sannan kikoyi ajiye hair spray kisabarwa da kanki yawan fesashi akanki sekuma su dryer su stretcher kina matukar bukatar su agidan aurenki seki tanadesu ki ajiye.
Dangane da tsawon gashi zaki iya kizabi daya daga cikin ukunnan ki jarraba kigani kozaki dace wato akwae ANDREA, HAIR NOW NOW,CHEBE POWDER.
Ki gwada amfani da daya insha Allah zaki iya dacewa gashinki ya kara tsayi kafin lokacin kicika sakawa ta gaban goshi don gurin yacika da gashi sosai don anason gaban goshin amarya da gashi ba sanko ba zefi kyau gurin make up
Hakanan shima kidinga gyarashi akai akai kar kice wae aboye yake basae kin wahalar da kanki ba
12. SAURA SATI BIYU BIKI: A nan kam daman kowacce tafi bada himma gurin gyara sedae kar kije kiyi kuskuren cewa ganin kinyi kyau bari kifara over dose din abubuwa domin kuwa zakije kibata rawarki da tsalle ne awannan ranakun kawae anfison kisamu Hutu sosai ne bawae ki fiye labtawa kanki abubuwa ba hatta shikanshi angon anason kidan ja mishi class Ku rage yawan hira hakanan kar kibarshi yazo acikin wannan satin karki bari yaga wannan gyaran koda apics ne har se lokacin yazo ki rikita mishi lissafi don wlh akwae yan iyayi wata kam ko dilka akeyi setayi snapping ta tura don zumudi alhali kuma anfison kubawa juna GAF awannan lokacin don shedan ze iya rikita mishi kyaunki kuje Ku afka wani abun da ba afata hakanan gyaran jikin amarya anfison abawa miji surprise ne bawae wata kam ma shine ze dauketa suyi ta yawon gyaran jiki tare.
Sai kuma idan kinaso zaki iya Neman gurin masu gyaran jiki sumiki na musamman awannan sati biyun sedae kar ki bari kishiga rana kidinga saka katuwar hijab da niqaf yanda zaki yi kyau sosai sekuma dangane da gayaran jiki anason kidinga yin dilka sosai zaki dinga saka mata kurkum ,se bacci sosai , se kuma turaren wuta shima anason kiyawaita shi wannan lokacin amma kar kiyarda baya ga abinda kike shafawa kije ki karawa kanki wani abun akai ze iya jawo miki matsala koda zaki chanja mai kar kichanja atake ki bayarda GAF din kwana uku baki Shafa komi tukun sannan ki chanja ,kar ki biyewa tunanin biki kisaka tunani ko zirga zirga ko yawo akanki duk suna zubar da ni imar da kika Tara ajikinki.
13. RANAR BIKI: A nan kam kedae kawae kibar gyaran ya isa haka anfison ki ranar kifito afresh saboda make up da za ayi miki kedae kawae ki tabbatar kin samu bacci me kyau yanda bazaki gaji da wuri ba hakanan lalle kar kibari adama miki hannu kiyi simple one kawae me kyau don idan yayi yawa yanasa hannun suyi baki kuma.
Amma turare kam ki turara sosai ranar har ma jikinki zaki bi dukka ki shafeshi da zallar turare kamar wanka
Sekuma bangaren gyaran HQ da ni ima shikam zamuyi gobe insha Allah.
Sekuma gurin selecting komi na kwalliyar biki tun daga kan make up da dressing kiyi kokari kiyi creating abun dazae fitting dinki banda copy copy kar kizamto komi se anzaba miki kiyi kokari wasu su yi copying akanki kizamto komi naki one in town karkije kina zabar dinkin da bazae karbi jikinki ba ko colour din kayan da bazae zauna da fatarki ba.
Hakanan gurin make up kar ki bari su kara miki haske asaka miki komi dai dai colour din skin dinki yafi class bawae aje ana ganin ki diff colours ba kuma kisamu wacce ta kware sosai.
Hakanan gurin saka kaya banda sabon Allah aje ayita matse wa ana bude tsiraici wlh zubar da kai ne kiyi komi naki cikin class kawae karki bari wae tun agun biki miji yagama ganin surarki gaskiya beyi ba.
Comments
Post a Comment