Skip to main content

Abin Da Ke Sa Yan Matan MU Na Yanzu Rasa Mazajen Aure

Babban abin da yake dada janyowa wasu ‘yan matan rashin Samun mazajen aure shi ne rowan ido.
Da yawan ‘yan mata yayin da suka kai wani mataki na girma tauraruwar su na haskawa a wannan lokacin wanda hakan ne yake sa wa samari su rinka tururruwar zuwa wajen yarinya don zama masoyinta na aure da wanda ba na aure ba.
A wannan mataki ne ita budurwar take ganin ta zama tauraruwa wanda hakan yakan sa ta ruwan -ido wajen zabar masoyi na kwarai kuma na gaskiya Wanda yake sonta tsakani ga Allah.

‘Yan matan sukan zabi masoyi yayin da suka sami wanda ya fishi sukan canja akalarsu kan wanda idanuwan su ya gano, haka za su yi ta canjawa har su rasa wanda za su zaba. Kyale-kyale da rudin duniya yakan saka idanuwansu rufewa su rasa gane ina suka dosa.
Ba wani abu ba ne yake janyo hakan illah kwadayi da kuma son abin duniya shi yake kawo hakan wani sa in ma da karance-karancen littafin Hausa da yake tasiri cikin zuciyarsu.
Da yawa a yanzu sukan dauki buri me girma su dorawa kansu Wanda hakan ko kusa bazai samu ba idan kuwa ya samu to! Sai an sha wuya ko kuma a same shi da sauki karshe asha wahala.

Wasu sukan sakawa zuciyarsu cewa lallai sai kyakkyawan sairayi zukeke me hanci dogo shi ma dogo fari kamar zubin fulani irin saurayin cikin littafin Hausa.

Sai mace ta sakawa zuciyarta ita a lallai sai irin wannan namijin zata aura wanda yake mara makusa kamar shi ya yi kansa, ko kusa babu wannan bazance babu kwata-kwata ba amma kafin a samu za a dade a ce an samu Wanda ya hada komai ba shida wani makusa kamar yanda na cikin littafin Hausa yake.

Wasu sukan saka wannan a ransu duk saurayin da ya zo sai su ce ba sa so saboda sun ruga sun bar wa zuciyarsu wannan tsarin.

Ko kuma mace ta kudurce cewa lallai sai me kudi sabida mijin kawarta ko saurayin kawarta mai kudi ne, don haka ita ma sai mai kudi ko kuma ajinta ya wuce ta auri talaka ko Wanda sana arsa ba mai girma ba ce irin wadda duniya za ta san da zamansa ba.
Ire-iren wadannan da ma wasu ra’ayoyin nasu wadanda ban fado su ba, toh! Sukan sa wasu matan rowan-ido dan ba dukka ne aka taru aka zama daya ba, sai an amincewa saurayi ringidi-ringidi da zaran wanda ya fi shi ya zo sai zance ya lalace.
Mata sai kun mun hakuri domin yau shafin nawa naku ne, ki sani cewa yayin da kika tsaya rowan-ido za a kai ki a baro ki ne, komai kyanki.
Mata sukan rasa na zaba har lokacin da samarin zasu daina zuwa lokacin mace ta huce wannan matakin da tauraruwar tata take haskawa sai kuma ta dawo tana lissafa adadin samarin da ta yi tana data sani tun a wancen lokacin ta zaba daya fi mata yanzu ga shi tana zaune ana aurar da kannenta tana gani.
A cikin rowan-idon wasu sukan kudurce su ba za su auri mai mata ba wani sa in ma har iyaye sukan ba wa yaran nasu gudummowa wajen haifar da rowan-idon yayin da akaita zaben aka rasa sai a dawo ana addu’ar Allah ya kawo ko da mai mata uku ne saboda burinsu a lokacin a aurar kar masu zaman unguwa su rinka ci gaba da zagi ko kuma saka ido a kowanne motsi na yarinyar.

A cewar wasu ‘yan matan zama da sautayi daya tsautsayi ne, gwara su rana kafa har Allah ya sa a dace, sai dai kuma abin takaicin shi ne zakuga wasu mazan na arziki wadaanda suke da niyyar yin aure kuma sun je wajen yarinya da zuciya daya amma ita sai taki amincewa da soyayyarsa ko da kuwa ba shida wani makusa a tare da shi safi biye wa samari matasa wadanda ba su da niyyar yin aure a wannan lokacin wato maza ‘yan tayin hira su rudeta su janye zuciyarta da wasu abubuwan wadanda ita a lolacin ba za ta san hakan ba sai ranar da ta yi hankali ko lolacin da ta saninta ya zo.
Ina kira ga masoya musamman mata tunda batuna gare ku nake a yau da ku daina rowan-ido su tsaya su kula wajen zabar miji na gari, dan gudun da an sani wata rana wasu mazan sukan zo wa ‘yan mata da abubuwa daban-daban dan janye zuciyarta wanda a bayan auren mace za ta ga ba hakan yake ba sai kuma ta yi da ta sani wane ta zaba sai a lokacin za ta runka hango halayyar wancen wanda ta bari ta yi da ta sani ta dauke shi, da na sani dai keya ce.

Wata ma garin rowan-idon ta zabo wa kanta wanda kullum zai rinka jibgarta ko kuma wanda zai rinka hana ta abinci, don akwai masu kudin da ba sa iya fitarwa cikin gidansu ba sa ba wa iyalansu komai sai dai a rinka gyara ginin gida ko shi ya yi dinki yana canjawa ana Alhaji wane mai kudi ne amma fa cikin gidansa iyalai na kuka ‘yan mata sai a kiyaye.
Haka zalika akwai namijin da za ki dabe shi don gayunsa amma bayan an yi aure sai lamari ya canja wannan dan tsukewar da yake yi yana janyo zuciyarki sai ki ga duk ba hakan yake ba sai zai futa yake samun daman yin wanka ma in har zabai futa ba toh ba shi ba wanka kin ga ba labari lamari ya baci sai a kula don gudun da an sani an zabi mai shigar kamala wanda yake sako ta-zarce ana kushe shi ana cewa bai waye ba. Ruwan-ido yakan korarwa da mace samari karshe ta zo tana da ta sani.
Masoya sai a kula a rinka danne zuciya a nutsu a yi aiki da hankali wajen zabar mijin aure don kar a yi zaben tumun dare.
Sanfuran Kalaman Soyayya:
Muna son junan mu kuma yanzu mun gama zama daya amma me ye lefina dan na mamaye zuciyar kyakykyawa kamarki?
Ina ma a ce ki kalli mudubi ki ga tsabar kyan halittarki dole na ririta ki na kula da ke domin ba zan yi wasa ki kubucemin ba.
Ni na san wahalar da na sha har na same ki tabbas ke mai daraja ce kuma ba zan mi ki kishiya ba
A hankali ga shi zuciya ta ta kamu da cutar da ke kadai ce mai maganinta babu maganar na guje to ina ma zan je na samu nutsuwa sama da gun ki masoyiya ta.
Ke ce idona yake son kallo a kodayaushe kallon hotonki ya zamammin aiki wallahi ke kyakykyawa ce. Wannan zumar ta soyayya zan ci gaba da lasa miki muddin za ki sha daga korama ta.
Ke hasken rana ce da ke dusashe dukkan duhu, da daddare kuwa ke ce farin wata sha kallo
Kuma ke ce tauraruwar da take haska sararin samaniyar zuciya ta.
Kyallin kyawun fatarki kadai kan haddasar da hargitsin nishadi a zuciya sanda na tuno da hakan
dukkan hakkin soyayya zan ba ki tunda kin ban ragamarki a hannuna da kuma sanyaya ranki ke ce zara ni wata,
Zan so a ce kina gefena da kin juya ni za ki gani a damarki.
Ni na riga na mallaka kaina gare ki kome ne zan miki ba na kokonto tunda na gane ke ce mai sona.
Kin san walwalarki ita ce sinadarina.
☆Ka goda wa Allah domin kuwa kana da babbar bai wa ta kalamai wadda duk wata ‘ya macen da ta ji su dole su shiga cikin jikinta har ya sa ta walwala ko da kuwa ranta a bace yake lokacin ina alfahari da kai zamowa gwarzo gare ni kuma jajirtacce wajen bayyanar da ingantacciyar soyayya gare ni mai dauke da nishadi.

Comments

Popular posts from this blog

Amfanin Ganyen Magarya A Jikin Dan’adam

Itaciyar ganyen magarya ana kiranta da Assidir a Larabce. Itaciya ce mai albarka da kuma dimbin tarihi.  Ya kasance ana amfani da ita tun kamin zuwan addinin Musulunci a duniya, bayan zuwan musulunci a duniya sai malamai da wasu magabata masana ilmin tsirran itatuwa suka bada fatawar amfaninta da irin cututtukan da take magani. Daga bisani suma masana kimiya ba a bar su a bayaba dan sun kaddamar da irin nasu bincike a kan alfanon ganye da kuma diyan magarya. Binciken ya baiwa masana ilimin harhada magani na yankunan turai da wasu yankunan kasahen duniya na Larabawa da India dama nan Afrika wata muhimmiyar damar saka bishiyar magarya a jerin bishiyoyin da ke da karfi da saurin warkar da wasu cututtukka. Ga kadan daga cikinsu:========= -Ciwon daji: A dafa garin magarya a misalin kofi daya karami sai a tarfa zuma mai kyau cokali biyu sai a sha da safe bayan an ci abinci. Amma a sanda ake shan magani irin wannan akwai bukatar a kauce wa shan wasu rukunnan magunnan bature. -Miki ko kura...

YADDA AKE SADUWA DA AMARYA A RANAR FARKO!

Babban abinda yake sa Mata jin tsoron jama’i shine ta yadda ake fara saduwa dasu a lokacin da suka yi auren farko wato lokacin da aka aurar da yarinya tana budurwa. Abinda ya kamata mu sani anan shine lokacin da ango zai kawar da budurcin amaryar sa yakamata ya bita a hankali domin kada ya manta ita amaryar​ batasan yadda akeyin Jima’i ba. ,             YANDDA ANGO YAKAMATA YAYI YAYIN SADUWAR FARKO , An fi son miji yaje ma matarsa da hira kuma kada yayi gaggawar nuna mata cewar yin jimai ya kawo shi kusa da ita, ldan yana cikin hira da ita sai ya kwantar da kansa akan kafafuwanta kuma yaci gaba da hirar sa. , In an dan dauki lokaci ana hira sai ya dauki daya daga cikin hannayensa ya dora a jikin ta kuma ya fara wasa da jikin nata a hankali, yana wansan yana cire mata kaya a hankali, yana wasa da cibiyarta kuma yana yin sama da hannun sa zuwa kirjinta a hankali, da zaran yakai hannusa a kan nononta, sai yaci gaba da wasa da nonowan n...

LAKANIN DA HADIN KARIN GIRMAN NONO DA KUMA DANKO DA MATSE GABA GA MATA

Yawancin mata rashin kula da kai da rashin sanin irin abubuwan da yakamata su dinga ci domin samun dauwamammiyar ni’ima a jikinsu don samun gamsuwar kawunansu da jin dadin mazajen shi ke haifar mu su da matsalar daukewar ni’ima da kuma daukewar sha’awa. Wasu kuma su kan kamu da ‘toilet infection’ ne saboda rashin tsaftar bandaki, wasu ba sa taba kula da gyaran bandakinsu, wasu kuma su kan dauka a bandakin hadaka..   Abubuwan da ya kamata mu mata mu dinga ci, domin karuwar ni’imar jikinmu da da jin dadin mazajenmu:====== A na son mace ta dinga cin daya ko biyu daga cikin wadannan abubuwan kullum a rana; a cikinsu akwai abubuwa masu saukin kudi wadanda duk rashin kudin ki ko rashin halin maigida, zai iya siya, kuma wadannan abubuwa su na kara lafiya da kuzari a jikkunan aluUmma kuma garkuwa ne ga kamuwa da wasu cutukan. Haka kuma ya na karawa mata ni”ima da jin dadi wajen mazajensu. Wadannan ba wasu abubuwa ba ne illa: Kankana Ayaba Gwanda Goba Lemo Tumatir Rake Aya Kwakwa Dafaf...